2025-10-16@14:53:23 GMT
إجمالي نتائج البحث: 4933

«wa Nijeriya»:

(اخبار جدید در صفحه یک)
    Tukur Muhammad Fakum, daya daga cikin jagororin al’ummar ya shaida wa BBC cewa an riga an kai makura, don haka a yanzu fatan su kawai bai wuce neman wa kai mafita ba.   Ya ce ”Mu yanzu muna nan muna gangami, mai ‘yar karamar gona ya sayar, mai dan karamin gida ya sayar, in muka sayi bindigogi a ba matasa su ma su yi kokari su kare mu.   ”Gwamnati ta ba mu kariya, idan kuma ba ta iyawa to ta bamu makamai a ba matasa, su matasa na iya kare rayukansu da garuruwan su,” in ji Tukur Muhammad Fakum. Dangane da halin da irin barnar da ‘yan bindigar suka yi masu kuwa, Tukur Muhammad Fakum ya ce ”Babu dai...
    Rundunar sojin Najeriya, ta bayyana cewa dakarunta sun kashe ’yan ta’adda biyar a wani samame da suka kai yankin Magumeri da Gajiram, a Jihar Borno. Kakakin rundunar Operation Haɗin Kai, Kanar Sani Uba, ya ce dakarun sun yi arangama da wasu ’yan ta’adda 24 da ke tafe a ƙafa a ranar Juma’a. Mutane 2 sun rasu a rikicin manoma da makiyaya a Kebbi Rashin wutar lantarki ta kassara kasuwanci a Kaduna, Kano da Katsina A cewar sanarwar da ya fitar, sojojin sun yi nasarar kashe biyar daga cikinsu tare da ƙwato kuɗi Naira miliyan biyar. “An hangi ’yan ta’addan suna ƙone gidaje da kuma kai wa mutane hari, sai dakarun suka fara bin su, inda suka tsere zuwa ƙauyen Damjiyakiri,”...
    ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Ƴansanda Sun Ceto Mutane Uku Da Aka Sace A Kano October 10, 2025 Manyan Labarai Matsalar Tsaro: Tinubu Ya Karyata Batun Yi Wa Kiristoci Kisan Ƙare Dangi October 10, 2025 Manyan Labarai Da Ɗumi-ɗumi: Tinubu Ya Zaɓi Farfesa Amupitan A Matsayin Sabon Shugaban INEC  October 9, 2025
    Ya bayyana cewa an riga an hada wadanda aka ceto da iyalansu, kuma ana ci gaba da gudanar da bincike da aikin ceton domin gano wadanda suka aikata laifin da kuma kubutar da sauran wadanda ake tsare da su, idan suna nan.   A halin da ake ciki kuma, kwamandan Runduna ta 6 ta Sojan Nijeriya, Birgediya Janar Kingsley Chidiebere Uwa, ya yaba da saurin daukar mataki da hadin kai tsakanin sojoji da ‘yansanda wanda ya kai ga nasarar aikin ceton.   Ya sake jaddada kudirin rundunar wajen tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin jama’a a Jihar Taraba.   Sai dai, ya bukaci jama’a da su ci gaba da bai wa sojoji da sauran hukumomin tsaro goyon baya ta hanyar...
    Mataimakin shugaban kasar Iran Mohammad Reza Aref ya bayyana cewa, batun kifar da gwamnatin JMI bayan yakin kwanaki 12 ya kuma fita daga abinda makiya zasu iya. Kamfanin dillancin labaran Tasnim na kasar yanakalto mataimakin shugaban kasa na farko yana fadar haka a ranar Alhamis da ta gabata, ya kuma kara da cewa a cikin yakin kwanaki 12 wanda kasashen Amurka da HKI suka dorawa kasar sun so su kifar da gwamnatin JMI a cikin kwanaki 3 zuwa 4 amma suka kasa. Ya ce hatta babban sakataren MDD Antonio Guterres ya tabbatar da haka a wata tattaunawa da shi dangane daha. Ya kuma tabbatar da cewa makiyan JMI ba zasu iya tumbuke tsarin ba. Yasashen yamma musamman Amurka suna kokarin...
    Masu zanga-zanga a nan Iran a jiya jumma’a a manya-manyan garuruwan kasar bayan sallar Jumma’a sun bayyana goyon bayansu ga al-ummar Falasdinu a Gaza, sannan sun bukaci HKI ta aiwatar da yarjeniyar da ta cimma da kungiyoyi masu gwagwarmaya. Har’ila yau sun bukaci a gaggauta shigo da abinci da magungunacikin zirin Gaza. Tashar talabijin talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto masu zanga zangar wadanda suka hada da mata da maza, malaman addini, daliban jami’o’i da sauransu suna tattaki daga dandalin inkilab zuwa dandalin azadi. Har’ila yau sun rera wakoki na goyon bayan masu gwagwarmayar, dauke da hotunan shahidai da kuma  shuwagabannin kawancen masu gwagwarmaya a yankin. An gudanar da jerin gwanon a cikin manya manyan biranen...
    Aƙalla mutane biyu ne suka mutu a rikicin da ya ɓarke tsakanin manoma da makiyaya a unguwar Dambo, wani kauye da ke da tazarar ’yan kilomita daga Birnin Kebbi, babban birnin Jihar Kebbi. Wani mazaunin yankin mai suna Ɗanladi Usman ya ce rikicin ya fara ne bayan an kashe wani mutum mai suna Sule yayin da yake aiki a gonarsa. “Kashe Sule ya tayar da hankulan al’umma, inda manoma suka ɗauki fansa suka kashe wani makiyayi da har yanzu ba a gano sunansa ba,” in ji shi. Ya ƙara da cewa makiyayan sun sha faɗa da manoma a kwanakin baya bayan sun aike musu da sako cewa su hanzarta girbe amfanin gonakinsu domin za su riƙa wucewa da shanunsu ta...
    Wadanda suka amfana da horon, an ba su horon ne a fannoni daban-daban da suka hada da yin noma da takin gargajiya da kuma yin noman kayan lambu da sauransu.   Kajin gidan gona da tare da kuma tallafa masu da kayan aikin noma.   Bisa tsarin wannan haron, kowace mace daya da ta amfana da horon, an ba su tallafin Naira Naira 50,000.   Kazalika, Adeleke ya danganta wannan tallafin kudin a matsayin mayar da hankalin gwamnatinsa na taimaka wa matan jihar.   Gwamnan ya kuma jaddada muhimmcin tallafa wa mata, wanda ya sanar da cewa; hakan na da muhimanci domin inganta gobensu.   Shi kuma shugaban gidauniyar, Dakta Deji Adeleke a nasa jawabin ya bayyana cewa, shirin wanda...
    A cewarta, shirin ya taimaka wajen noman shinkafa da ta kai kimanin tan 99,452, wacce kuma kudinta ya kai kimanin Naira biliyan 13.527 tare kuma da noman rogo da ya kai kimanin tan 87,237, wanda kudinsa ya kai Naira biliyan 3.925, musamman domin a kara samar da wadataccen abinci da kuma kara bunkasa fannin tattalin arzikin jihar.   Sai dai, ta bayyana cewa; har yanzu a jihar ba a samar da wani cikakken tsari a hukumance ba, a kan tsarin na shirin na CAF wanda hakan ke haifar wa da shirin koma baya a jihar.   Ta yi kira ga sauran masu ruwa da tsaki a fannin bunkasa aikin noma, domin samun riba a jihar da su bayar da hadin...
    Duk da Najeriya na cikin yanayin damina, wanda ake ganin a lokacin ta fi samar da wutar lantarki ga ’yan ƙasarta, amma jama’a a jihohin Kaduna da Kano na ci gaba da kokawa kan ƙarancin wutar. A duk shekara jama’a na more wutar lantarki a Nijeriya a lokacin damina saboda tashoshin ruwa na samar da wutar lantarki suna aiki da cikakken ƙarfinsu. Amma, wasu masana a ɓangaren wutar sun shaida wa wakilinmu cewa duk da matsalolin masu nasaba da lalata kayan aiki da kuma ƙin biyan kuɗin wuta da wasu masu amfani da ita ke yi, kamfanonin rarraba wutar (DisCos) suna yin iya bakin ƙoƙarinsu wajen cike giɓin. Masu ruwa da tsaki sun bayyana cewa ana ƙoƙarin daidaita rarraba wuta...
    Kasar Venezuela ta yi kira ga Kwamitin Sulhun Majalisar Dinkin Duniya da ya tabbatar da cewa Amurka tana yin barazana zaman lafiyar duniya Kasar Venezuela ta yi kira ga kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya da ya amince cewa; Lallai Amurka tana yin barazana ga zaman lafiya da tsaro na kasa da kasa, saboda yadda sojojin Amurka suke shisshigi a tekun Caribbean, wannan batu ya zo ne a yayin zaman gaggawa na majalisar a jiya Juma’a. Wakilin dindindin na Venezuela a Majalisar Dinkin Duniya, Samuel Moncada, ya ce: “Suna ba da shawarar ayyuka uku ga kwamitin sulhun Majalisar Dinkin Duniya: Na farko, amincewa da barazanar zaman lafiya da tsaro na kasa da kasa da sojojin Amurka suka haifar a cikin...
    Ministar wadda ta je kamfanin domin daukar sabuwar motarta ta alfarma kirar Nord Demir SUB da kamfanin ya hada nataimakin Shugaban jami’ar na sashen kula da ilimi da gudanar da bincike Farfesa Bola Oboh da kuma Shugaban kamfanin Mista Oluwatobi Ajayi ne, suka karbi bakuncinta.   A jawabin da ta gabatar a lokacin ziyarar ministar ta bayyana cewa,Duba da yarjejeniyar hada-hadar kasuwanci wajen fitar da kaya zuwa ketare kamfanin zai iya yin amfani da wannan samar waken fitar da motocinsa zuwa ketare.   Ta kara da cewa, Nijeriya na da gurare biyu ne da ake hada motoci da suka hada da, na wannan jami’ar da kuma na EPs, inda ta yi nuni da cewa, karfin da kamfanin ya ke da...
    ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin CMG Ya Kaddamar Da Shirin “Dabarun Tallata Kayayyakin Sin” A Tafarkin Gina Kasa Bisa Hadin Gwiwa October 10, 2025 Daga Birnin Sin Sin Za Ta Fara Cajin Kudi Na Musamman Ga Jiragen Ruwan Amurka October 10, 2025 Daga Birnin Sin Kasar Sin Ta Samu Manyan Nasarori A Fannin Inganta Walwalar Yara Da Tsoffi Cikin Shekaru 5 Da Suka Gabata   October 10, 2025
    Hukumar Tsaro ta Sibil Difens a Jihar Kano, ta cafke wasu mutum uku da ake zargi da safarar miyagun ƙwayoyi a Ƙaramar Hukumar Doguwa. Hukumar ta miƙa su ga Hukumar Yaƙi da Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi (NDLEA), domin ci gaba da bincike da gurfanar da su a kotu. ’Yan bindiga sun kashe Civilian JTF 8 a Zamfara Sojoji sun mutu yayin da Boko Haram ta kai hari sansanin soji a Borno Kwamandan hukumar na Jihar Kano, Bala Bawa Bodinga ne, ya bayyana hakan yayin da yake magana da ’yan jarida a hedikwatar hukumar a ranar Juma’a. Ya ce an kama mutanen ne da sanyin safiyar ranar Talata, 7 ga watan Oktoba, 2025, bayan samun sahihin bayaai. Jami’an hukumar daga...
    “Ta yaya Jonathan zai zama barazana? Mun doke shi a baya lokacin da PDP take kan mulki.   “Idan mutum yana ganin cewa PDP ita ce kololuwar jam’iyya a Nijeriya, kuma ya sha kaye a lokacin da yake ganiyarsa, ina ganin sai makiyinsa ne kawai zai tilasta masa ya kara tsayawa takara a zaben 2027,” in ji shi.   Tsohon shugaban jam’iyyar APC na kasa ya ce a yanzu haka Jonathan ya kasance dan siyasa mai daraja, yana mai cewa komawa fagen siyasa na iya rage masa kima da kuma zubar masa da darajar da yake da shi a idon duniya.   Ya jaddada cewa Jonathan ya samu damar nuna cewa mulki bai tsole masa ido ba, domin haka ne...
    Ministan kula da harkokin al’umma na kasar Sin Lu Zhiyuan, ya ce cikin wa’adin shirin raya kasa na shekaru 5-5 na 14 tsakanin 2021 zuwa 2025, walwalar yara da tsoffi a kasar, ta samu gagarumin ci gaba. Lu Zhiyuan, ya bayyana yayin wani taron manema labarai a yau Juma’a cewa, yayin wa’adin shirin, an samar da wani cikakken tsarin bayar da kariya da kulawa ga yara mabukata, wanda ya shafi yaran da ba sa gaban iyayensu saboda wasu dalilai, da yaran da iyayensu suka yi nesa da gida, da yaran da suka kaura, inda a yanzu dukkansu ke cin gajiyar hidimomin kariya da kulawa na kasar. Har ila yau a wa’adin, kasar Sin ta kammala gyarawa da sake fasalin kayayyakin...
    Wani Likitan ƙwaƙwalwa a Asibitin Neuropsychiatric Aro, a Abeokuta, Jihar Ogun, Dokta Emmanuel Abayomi ya ce kimanin mutane miliyan 60 ne ke fama da taɓin hankali a halin yanzu. Ya yi wannan jawabin ne a ranar Juma’a a Abeokuta a wajen wani taron ƙarawa juna sani da Ƙungiyar likitoci ta NAS ƙarƙashin Ƙungiyar masu ruwa da tsaki ta ƙasa ta shirya domin tunawa da ranar kiwon lafiyar ƙwaƙwalwa ta duniya ta bana. Ɗan Majalisa ya nemi ɗaukar mataki kan dorinar ruwa a Gombe ’Yan sanda sun ceto mutum 3 da aka sace a Kano da Kaduna Shirin da Ash Montana Deck tare da haɗin gwiwar Atlantis, Americana 1 da Longhorn Deck suka yi wanda ya ja hankalin ‘yan sanda da...
    A yayin da ake yawan samun ɓarnar dorinar ruwa a garuruwan Daɗin Kowa da Kupto da Malleri da Wade a yankunan Ƙananan hukumomin Kwami da Yamaltu Deba a Jihar Gombe ta kai ga samun asarar amfanin gona da rayuka. Hakan ne ya sa Ɗan majalisar tarayya mai wakiltar mazaɓar Yamaltu/ Deba a Jihar Gombe Inuwa Garba ya gabatar da ƙudiri a gaban zauren Majalisar Wakilai ta tarayya domin neman ɗaukar matakin gaggawa kan ɓarnar dorinar ruwa. ’Yan sanda sun ceto mutum 3 da aka sace a Kano da Kaduna Kwastam ta kama buhunan lalatacciyar fulawa 10,000 ana ƙoƙarin shigo da ita Najeriya Inda ya ce dorinar na yi wa manoma ɓarna sosai da ke janyo asarar rayuka, dukiyoyi da lalacewar...
    Bugu da kari, an rufe shafukan hakar ma’adanai haramtacce 98 a fadin kasar.   “An kiyasta cewa Nijeriya na asarar kusan Dala biliyan 9 a kowace shekara sakamakon haramtacciyar hakar ma’adanai. Wannan sata ta albarkatunmu da ya kamata ta bunkasa kasarmu ta wuce kima, kuma lokaci ya yi da za a kawo karshensa,” in ji Abdulraheem.   A cewar sa, kwamitin na da alhakin hana asarar kudaden shiga, tabbatar da gaskiya da adalci a harkokin hakar ma’adanai, da tabbatar da cewa dukiyoyin ma’adanin kasar suna ba da cikakken gudunmawa ga ci gaban tattalin arziki.   “Yayin da muke ci gaba, daya daga cikin manyan manufofin wannan kwamitin shi ne hana asarar kudaden shiga da haramtacciyar hakar ma’adanai da ayyukanta ke...
    Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano, ta samu nasarar ceto wasu mutum uku da aka sace, bayan wani samame da ta kai a jihohin Kano da Kaduna. Wannan na daga cikin ƙoƙarin da rundunar ke yi domin yaƙi da laifuka da tabbatar da tsaron jama’a. ’Yan sanda sun manta hularsu a motar dalibi bayan karɓar ‘cin hancin’ N99,000 NAJERIYA A YAU: Kalubalen Da Ke Gaban Sabon Shugaban Hukumar Zabe Ta Kasa A cikin wata sanarwa da kakakin rundunar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya fitar, ya bayyana cewa an gudanar da samamen ne tsakanin ranar 7 zuwa 9 ga watan Oktoba, 2025, bisa umarnin Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar, CP Ibrahim Adamu Bakori. A cewar Kiyawa, samamen farko ya gudana ne a ranar...
      “Akwai da yawa malamai marasa cancanta a cikin aikin. Muna da wadanda ke koyarwa a ajujuwa amma ba su da takardun shaidar koyarwa, musamman a makarantu masu zaman kansu,” in ji ta.   Ta bayyana cewa, yayin da wasu mutane ke da sha’awar koyarwa da gaske, rashin horo na hukuma ya hana su shiga aikin koyarwa.   Dr. Soyombo ta bayyana cewa TRCN a halin yanzu na da malamai masu rijista kusan miliyan 1.4, tare da shirin kara wannan adadi zuwa miliyan 20 cikin shekaru biyu masu zuwa ta hanyar dijital da saurin rajista.   “Mun zamanantar da tsarinmu domin mutane da yawa su sami damar yin rijista,” in ji ta. “Kowane malami yana da bai wa ta musamman...
    Hukumar Kwastam shiyyar bodar Najeriya ta Seme da ke jihar Legas ta ce ta cafke motoci biyar da ke maƙare da buhuna 10,000 na lalatacciyar fulawa da darajarsu ta kai Naira biliyan 1.2. Rundunar ta kuma ce ta tara jimillar kuɗin shigar da ya kai Naira biliyan daya da rabi a watan Satumba, wanda hakan ya nuna kari da kaso 182 cikin 100 idan aka kwatanta da Naira miliyan 531 da aka tara a watan Agustan da ya gabata. NAJERIYA A YAU: Kalubalen Da Ke Gaban Sabon Shugaban Hukumar Zabe Ta Kasa Tinubu ya yi wa Mamman Vatsa, Farouk Lawan da wasu mutum 173 afuwa Kwamandan rundunar a shiyyar, Wale Adenuga, ne ya bayyana hakan a taron manema labarai na...
    Kazalika, tarihin Dimokiradiyyar kasar ya sha cin karo da kwam gaba kwam baya kusan za a iya cewa, tun bayan dawowar mulkin Demokaradiyya a 1979 da kuma sake dora kasar a wata turbar ta Demokiradiyyar a 1999.   Alal misali, jamhuriyya ta hudu ta kasance ta jima sosai, amma kusan babu wasu ayyukan na inganta rayuwar ‘yan kasar da za a bigi Kirji a ce gasu an gani a kasar a zahiri.   Idan aka dubi bangaren samar da hasken wutar lantarki kusan za a iya cewa, karni da dama da suka bace, har zuwa yau Nijeriya ta gaza samar da karfin wutar da kuma rabar da ita da ta kai karfin Megawatts 5,000 musamman duba da cewa, wannan adadin...
    Rahotanni daga Gaza na cewa Isra’ila ta fara janye sojojinta daga wasu yankuna na zirin Gaza. Wannan dai na zuwa ne bayan da gwamantin Isra’ila ta amince da yarjejeniyar tsagaita wuta dake kunshe a shirin zaman lafiya na Trump da ta cimma da kungiyar Hamas. Daraktan Hukumar Ba da Agajin Gaggawa da Hadin Kan Kasa da Kasa ta Hukumar Tsaron Fararen Hula ta Gaza Mohammad Al-Moughayyir, ya ce sojojin Isra’ila sun janye daga yankuna da dama a cikin birnin Gaza da arewacin zirin da kuma wasu yankunan kudancin yankin. A Khan Younis da ke kudancin zirin Gaza, Motocin Isra’ila sun janye daga kudancin birnin da tsakiyar birnin zuwa yankunan gabashi. Share 0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of...
    Cibiyar Kula da Harkokin kasuwanci ta kasa ta bayyana kafa Cibiyar Gudanar da taron Kasuwanci na Najeriya a wani bangare na ganin ba a samarda cibiyoyi da ke da aiki iri ɗaya ba.   Babban magatakardar Cibiyar Mista Victor Olannye, ne ya bayyana haka a lokacin da yake gabatar da takardar a yayin taron jin ra’ayin jama’a na kwamitin majalisar wakilai kan harkokin kasuwanci a Abuja.   Mista Victor Olannye ya ce kudurin dokar da ke neman kafa sabuwar cibiyar ya ci karo da ayyukan Cibiyar Gudanarwa ta kasa da tuni Majalisar Tarayya ta 9 ta amince da ita wadda Shugaban kasar na wancan lokacin ya amince da shi.   Ya yi nuni da cewa, babban makasudin kafa Cibiyar Kula...
    Yawan mace-mace ta hanyar cutar kwalarar, na faruwa ne duk da biliyoyin Nairori da aka ce gwamnati da abokan huldar kasa da kasa suna kashewa, domin kokarin ganin an dakile ta.   Wadannan kudade sun hada da kason kasafin kudi na shekara-shekara, wanda ya kunshi miliyoyin Nairori; akwai dala miliyan 700 da bankin duniya ya bayar domin samar da tsaftataccen ruwa sha, tsaftar muhalli a fadin kasa baki-daya, tallafin dala miliyan 2 daga Majalisar Dinkin Duniya, dubban daruruwan allurar rigakafin cutar kwalara da asusun kula da yara na Majalisar Dinkin Duniya (UNICEF) da Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) suka bayar da sauran makamantansu. Alkaluman da aka samu daga cibiyar NCDC, sun nuna cewa a cikin 2020, kasar ta samu rahoton...
    Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kaduna ta kama mutum 26 da ake zargin masu garkuwa da mutane ne tare da kwato makamai da kudade daga hannunsu. Daga cikin abubuwan da aka samu nasarar kwatowar har da bindigogi na gida guda huɗu, makamai masu hatsari da kuma tsabar kuɗi Naira 546,000 da ake zargin wani ɓangare ne na kuɗin fansa. Tinubu ya yi wa Mamman Vatsa, Farouk Lawan da wasu mutum 173 afuwa Tinubu ya naɗa Amupitan a matsayin Shugaban INEC An kama waɗanda ake zargin ne a cikin jerin samame da aka gudanar daga ranar 3 zuwa 5 ga watan Oktoban 2025, a sassa daban-daban na jihar. Samamen ya haɗa jami’ai daga sashen ’yan sanda na Anchau, Hukumar Kula da Tsaro...
      Dare ya jaddada cewa Nijeriya kasa ce mai addinai da dama, wacce aka gina bisa juriya, zaman lafiya, da girmama juna tsakanin mabambantan addinai, al’ummomin da ya ce Tinubu ya shugabanta.   Dare ya ambaci maganar Shugaban Kasa inda ya jaddada cewa Nijeriya “kasa ce mai cikakken ‘yanci da girma, wadda aka gina bisa bangaskiya da juriyar jama’arta,” ya kara da cewa “Babu wani addini da ake zalunta, kuma babu wata al’umma da aka ware.” Yana nuna misali da rayuwar Shugaban Kasa a matsayin shaida ta juriya da fahimtar addinai, Dare ya bayyana cewa Shugaba Tinubu, Musulmi ne da yake auren fasto mai bin addinin Kirista. Ya kuma ruwaito Shugaban yana cewa, “Gaba da kiyayya ba su da gurbi...
    Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya bukaci dukkanin bangarorin da su yi aiki da kuma mutunta yarjejeniyar da shugaban Amurka Donald Trump ya gabatar da kuma yin amfani da wannan  damar. Da yake jawabi a wurin taron Majalisar Dinkin Duniya, Guterres ya bayyana cewa, “Ina kira ga dukkan bangarorin da su mutunta ka’idojin yarjejeniyar, da kuma rungumar damar da tke cikinta.” Duk da cewa dai a  cikin kalaman nasa yafi nuna damuwa a kan fursunonin Isra’ila da ake tsare da su a Gaza, duk da irin mummunan kisan kiyashi da Isra’ila take yi a Gaza, amma mya ce Majalisar Dinkin Duniya ta shirya tsaf domin ba da cikakken goyon bayanta ga aiwatar da yarjejeniyar. A halin da...
    Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya bayar da afuwar Shugaban Kasa ga mutane 175. Daga ciki har da wadanda aka yi wa afuwar bayan mutuwa ga marigayi Manjo Janar Mamman Jiya Vatsa da ɗan gwagwarmayar kwato ’yancin kan Najeriya, Herbert Macaulay. An dauki wannan mataki ne bayan amincewa da shawarwarin da Majalisar Tsofaffin Shugabannin Ƙasa ta bayar a taronta da aka gudanar a ranar Alhamis a Abuja. Gwamnatin Kano ta shirya ɗaurin auren ma’aurata 2,000 Tinubu ya naɗa Amupitan a matsayin Shugaban INEC A cewar sanarwar da mai ba Shugaban Ƙasa shawara kan harkokin bayanai da dabarun sadarwa, Bayo Onanuga, ya fitar, Shugaba Tinubu ya kuma yi afuwa ga tsohon ɗan majalisa Farouk Lawan da wasu mutum uku, Misis Anastasia...
    ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin Duniya Ta Kara Ganin Bunkasuwar Sin a Lokacin Hutun Murnar Ranar Kafuwar Sabuwar Kasar October 9, 2025 Daga Birnin Sin An Samu Karuwar Sayayya Yayin Hutun Bikin Kafuwar Kasar Sin October 9, 2025 Daga Birnin Sin Adadin Biyan Kudade Ta Intanet Yayin Hutun Bikin Kafuwar Jamhuriyar Jama’ar Sin Ya Kai Yuan Tiriliyan 13.26 October 9, 2025
    Gwamnatin tarayya ta yi asarar jimillar gangar danyen mai miliyan 13.5 wanda kudinsa ya kai dala biliyan 3.3 sakamakon sata da fasa bututun mai tsakanin shekarar 2023 zuwa 2024, in ji wata kungiya mai fafutukar kare masana’antu ta Nijeriya (NEITI). Sakataren zartarwa na NEITI, Dokta Ogbonanya Orji, ne ya bayyana hakan a Legas a taron kungiyar masu ba da rahoto kan makamashi ta Nijeriya (NAEC) na 2025 a Legas ranar Alhamis. Ya koka da cewa, rashin gaskiya da rikon amana ne ya dabaibaye masana’antar mai da iskar gas, yana mai cewa akwai bukatar yin gaskiya da aiwatar da sabon tunani na fasaha wajen tafiyar da harkar mai da iskar gas a kasar. Orji ya lura cewa, kudaden da aka yi...
    A bana, bikin Tsakiyar Kaka da Ranar Kafuwar Jamhuriyar Jama’ar Sin sun hadu, inda suka haifar da hutun tsawon kwanaki takwas. An yi hasashen cewa, adadin mutanen da suka yi tafiya a yankuna daban daban na kasar zai kai biliyan 2.432, tare da karuwar kashi 6.2% a kowace rana idan aka kwatanta da shekarar da ta gabata. Adadin ribar da aka samu a manyan kantuna da gidajen abinci a cikin kwanaki hudu na farkon hutun ta karu da kashi 3.3% idan aka kwatanta da na bara, kuma har zuwa karfe 4:00 na yammacin ranar 8 ga watan, kudin shiga da aka samu daga kallon fina-finai yayin wannan biki ya wuce RMB Yuan biliyan 1.8 kwatankwacin fiye da dala miliyan 252....
    Rahotanni sun bayyana cewa, karar mai lamba FHC/OS/194/2024, ta nemi umarnin tilastawa INEC da shugabanta na lokacin da su sanya sunayen wasu jami’an Jam’iyyar AA a shafin hukumar na yanar gizo bayan an cire su.   Sai dai Udeze ya ci gaba da cewa, babu irin wannan hukunci ko umarnin kama shi (Yakubu), yana mai tabbatar da cewa, rahotannin ƙage ne kawai. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Da Ɗumi-ɗumi: Tinubu Ya Zaɓi Farfesa Amupitan A Matsayin Sabon Shugaban INEC  October 9, 2025 Labarai SSANU Da NASU Sun Yi Zanga-Zanga A Abuja Kan Rashin Cika Alƙawarin Gwamnati October 9, 2025 Labarai An Umurci Manyan Makarantu Su Mayar Da Kuɗaɗen TETFund Da Ba Su Kashe Ba October 9, 2025
    Rundunar ’yan sandan Jihar Kaduna ta kama wasu mutane 26 da ake zargi da yin garkuwa da mutane, tare da ƙwato bindigogi guda 4, da muggan makamai da dama. Ta kuma kama wani ɓangare na kuɗin fansa da ake zargin an biya masu garkuwa da mutane a wasu hari daban-daban a jihar. Nasarar kamen dai ya biyo bayan wasu jerin samame da jami’an ’yan sanda da na ’yan banga suka yi a tsakanin ranakun 3 zuwa 5 ga watan Oktoban 2025, inda suka yi ta kai farmaki kan gungun masu garkuwa da mutane da ke kai hari a ƙananan hukumomin Anchau, Ikara da kuma Makarfi. Tinubu ya naɗa Amupitan a matsayin Shugaban INEC Ma’aikatan jami’a sun yi zanga-zanga a Jami’ar...
    Shugaban ƙaramar hukumar Oredo, Hon. Gabriel Iduseri, ya ziyarci kasuwar da safiyar ranar Alhamis.Yayin ziyararsa, Iduseri, ya bayyana lamarin a matsayin babban iftila’i ga ‘yan kasuwa, tare da alƙawarin cewa za su ba su tallafi.“Wannan lokaci ne na matuƙar baƙin ciki ga mutanenmu, musamman ma ‘yan kasuwar da suka dogara da wannan waje don samun abincin yau da kullum. Ba za mu bar su su fuskanci wannan asara su kaɗai ba,” in ji shi.ShareTweetSendShareMASU ALAKA SiyasaNi Ne Ɗan Siyasa Mafi Shahara A Kudu Maso Gabas, Ba Peter Obi Ba – Orji Kalu October 9, 2025Manyan LabaraiTattalin Arziƙin Nijeriya Ya Ƙaru Da Kashi 3.9 – Bankin Duniya October 9, 2025Manyan LabaraiTinubu Na Son A Saka Hannun Jari Da Kuɗaɗen Fansho A...
    Babban kwamandan dakarun kare juyin juya halin Musulunci ya jaddada cewa: Duk wani kuskuren da makiya za su yi, za su fuskanci martani mai tsanani Babban kwamandan dakarun kare juyin juya halin Musulunci (IRGC) Manjo Janar Mohammad Pakpour ya jaddada cewa: Duk wani kuskuren da makiya za su yi a mashigar tekun Farisa, da mashigar Hormuz da tsibirin Iran, za su fuskanci hukunci mai tsauri, nan take, murkushewa, da kuma nadama. A cikin sakon taya murnar zagayowar ranar sojojin ruwa na dakarun kare juyin juya halin Musulunci, Manjo Janar Pakpour ya bayyana cewa: “A jajibirin ranar sojojin ruwa na dakarun kare juyin juya halin Musulunci, yana mika sakon taya murna ga babban matsayi na kwamandoji da mayakan da suka yi...
    Tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya kaddamar da sabuwar cibiyar taro ta Ahmadu Bello da aka gina a Bauchi, inda ya bayyana ta a matsayin alamar ci gaba a gwamnatin Gwamna Bala Mohammed.   Da yake jawabi a wajen taron, Obasanjo ya jaddada muhimmancin dunkulewar duniya, inda ya ce babu wata al’umma da za ta iya rayuwa a ware ba tare da yin hulda mai ma’ana da sauran kasashen duniya ba.   Ya yaba wa Gwamna Bala Mohammed bisa ayyukan raya kasa, musamman a fannin samar da ababen more rayuwa, wanda a cewarsa hakan zai karawa Bauchi damar karbar bakuncin taron kasa da kasa da kuma jawo hankalin masu zuba jari.   Tsohon shugaban kasar ya bayyana cewa irin wadannan...
    An shawarci mata a karamar hukumar Kirikasamma da ke jihar jigawa da su kawo ‘ya’yansu domin yi musu rigakafin cutar shan inna, kyanda, da Gaida da sauran cututtuka masu ban tsoro.   Uwargidan Shugaban Karamar Hukumar, Hajiya Fatima Maji Marma ta ba da wannan shawarar a lokacin kaddamar da shirin rigakafin cutar kyanda da na rigakafi na yau da kullum a fadar Hakimin Marma.   Ta kuma jaddada aniyar karamar hukumar na bayar da tallafin da ake bukata domin samun nasarar gudanar da aikin rigakafin.   Hajiya Fatima ta kuma yabawa gwamnatin jihar Jigawa bisa bullo da inshorar lafiya ga marasa galihu a matakin unguwanni a kananan hukumomin jihar 27.   A nasa jawabin manajan hukumar kula da lafiya matakin...
    Gwamnatin jihar Neja ta bayyana shirinta na yin hadin gwiwa da kungiyar injiniyoyin ma’adanai ta Najeriya a matakin jiha da tarayya domin tabbatar da aiwatar da kudurorin da aka cimma a karshen taron kasa da kasa karo na ashirin da hudu.   Gwamnan jihar Mohammed Umar Bago ya bayyana haka a lokacin da yake bayyana bude taron shekara-shekara da taron kasa da kasa na shekara ashirin da hudu da aka gudanar a Minna babban birnin jihar Neja.   Gwamnan wanda ya samu wakilcin shugaban ma’aikata Injiniya Idris Abubakar ya bayyana cewa hakan ya zama dole domin dorewa da aikin hakar ma’adanai na da matukar muhimmanci wajen kare shirin makamashi maras illa a matsayin Jigon gwamnatin sa.     A nasa...
    Gwamna AbdulRazaq ya yabawa Shugaba Tinubu yayin da Sojoji suka tura cikakken birgediya domin fatattakar masu garkuwa da mutane daga dazukan Kwara.     Hedkwatar sojojin Najeriya ta aika da  cikakken birgediya da manyan kayan aiki a sassa daban-daban na Kwara ta Kudu, domin rage matsalolin tsaro a yankin.   Wata sanarwa da sakataren yada labarai gwamnan, Rafiu Ajakaye ya fitar ta ce Tuni dai sojojin suka yi ta luguden wuta ta cikin kauyukan Oke Ode da Babanla, dukkansu a karamar hukumar Ifelodun.   Har ila yau, rundunar ta kara da cewa, aikin ya zarce zuwa Edu da Patigi domin ratsa dazuzzukan da masu garkuwa da mutane suka fara kai hare-hare na matsorata a kan al’ummomi daban-daban tare da yin...
    Majalisar Wakilai, ta yi watsi da zargin da Ƙasar Amurka, ta yi na cewa ana yi wa Kiristoci kisan gilla a Najeriya. Wannan martani na zuwa ne bayan wani Sanatan na Amurka, Ted Cruz, ya gabatar da ƙudirin doka a Majalisar Dattawan ƙasar, inda ya ce ana yi wa Kiristoci kisan gilla a Najeriya. Sauye-sauyen Tinubu ba su rage talauci a Najeriya ba — Bankin Duniya Fadar Shugaban Ƙasa ta ƙaryata rahoton Bankin Duniya kan yawan talakawa a Najeriya A yayin gabatar da ƙudirin ya buƙaci a ƙaƙaba wa wasu jami’an Najeriya takunkumi. Cruz ya ce: “ Ana kashe Kiristocin Najeriya saboda addininsu… lokaci ya yi da za a ɗauki mataki na gaske kan jami’an Najeriya da ke taimaka wa...
    Cristiano Ronaldo ya zama biloniya na farko tsakanin ƴan wasan kwallon kafa a duniya Bloomberg mai sharhi da kididdiga tarin dukiya tsakanin attajiran duniya, ta fayyace tarin kudin da mai shekara 40 dan kwallon tawagar Portugal mai taka leda a Al-Nassr ta Saudiya ke da shi. Ta ce yana da dalar Amurka biliyan daya da miliyan 400 daga kudin da yake samu na albashi da ladan wasa da tallace-tallace da zuba hannun jari. Ya samu albashin sama da dalar Amurka miliyan 550 tsakanin 2002 zuwa 2023 da kwantiragin da ya kai  dalar Amurka miliya 18. Lokacin da Ronaldo ya koma Al-Nassr ta Saudiyya a 2022, ya zama wanda ke kan gaba da ake biya albashi mafi tsoka a tarihi. da...
    Bankin Duniya ya ce har yanzu talauci na ci gaba da yaɗuwa a Najeriya duk da sauye-sauyen tattalin arziƙi da Gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta aiwatar domin daidaita tattalin arziƙin ƙasar. A wajen ƙaddamar da rahoton ci gaban da aka samu a Abuja, Daraktan Bankin Duniya a Najeriya, Mathew Verghis, ya bayyana cewa aƙalla mutum miliyan 139 ne ke rayuwa cikin ƙangin talauci a shekarar 2025. Fadar Shugaban Ƙasa ta ƙaryata rahoton Bankin Duniya kan yawan talakawa a Najeriya NAJERIYA A YAU: Abin Da Dokar Kasa Ta Ce Kan Nada Shugaban Hukumar Zabe Ya ce duk da cewa tattalin arziƙin Najeriya ya ɗan bunƙasa, kuma gwamnati tana samun ƙarin kuɗaɗen shiga, yawancin jama’a har yanzu na fama da tsadar...
    Fadar Shugaban Ƙasa ta yi fatali da sabon rahoton tattalin arziki da Bankin Duniya ya fitar, wanda ya kiyasta cewa mutane miliyan 139 na rayuwa cikin talauci. Fadar ta bayyana adadin a matsayin wanda ya saba da zahiri kuma ya kauce wa hakikanin halin tattalin arzikin ƙasar. SSANU da NASU za su yi wa gwamnati zanga-zanga kan rashin cika musu alƙawari 2027: Atiku, Jonathan da Obi ba za su iya kayar da Tinubu ba — Kalu Mai ba Shugaban Najeriya Bola Tinubu shawara kan harkokin yaɗa labarai da sadarwa, Sunday Dare, ya bayyana a shafinsa na X a ranar Laraba cewa dole ne a rahoton bai duba yanayin tsarin auna talauci na duniya ba. “Duk da cewa Najeriya na daraja...
    Ƙungiyar Ma’aikatan Manyan Makarantun Najeriya (SSANU) da Ƙungiyar Ma’aikatan Ilimi (NASU), sun shirya gudanar da zanga-zangar gargaɗi ta rana ɗaya a yau Alhamis saboda Gwamnatin Tarayya ta gaza cika musu alƙawuran da ta ɗauka. Ƙungiyoyin, ƙarƙashin jagoranci Joint Action Committee (JAC), sun gudanar da taron gaggawa a ranar Laraba don shirya zanga-zangar. 2027: Atiku, Jonathan da Obi ba za su iya kayar da Tinubu ba — Kalu ’Yan sanda sun kama ɗan bindiga a kan iyakar Najeriya da Kamaru Sun ce za su gudanar da tattaki a cikin jami’o’i, tare da ɗaukar kwalaye masu rubuce-rubuce, sannan za su yi wa manema labarai jawabi domin bayyana ƙorafe-ƙorafensu. Sun zargi gwamnati da rashin adalci wajen rabon Naira biliyan 50 na alawus-alawus, ƙin...
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba A tsarin mulkin Najeriya, an bai wa Shugaban Ƙasa ikon naɗa shugaban Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) tare da sauran mambobinta. Wannan iko yana daga cikin muhimman nauyukan da ke hannun shugaban ƙasa domin tabbatar da cewa ana gudanar da zaɓe cikin tsari, gaskiya da adalci.   Sai dai, kafin wanda shugaban ƙasa ya naɗa ya fara aiki, dole ne a nemi amincewar Majalisar Dattawa, domin tabbatar da cewa wanda aka zaɓa ya cancanci rike wannan muhimmiyar kujera. Wannan tsari yana taimakawa wajen tabbatar da cewa hukumar zaɓe ta kasance mai zaman kanta, ba ta karkata ga wani ɓangare na siyasa ba, kuma tana iya gudanar da aikinta cikin gaskiya...
    Kakakin majalisar wakilai, Hon. Abbas Tajudeen, ya jaddada buƙatar ɗaukar ƙwararan matakai na kafa tsarin ‘yansandan jihohi a kasar nan domin magance kalubalen tsaro da ake fuskanta.Abbas ya bayyana haka ne a wajen taron jin ra’ayin jama’a kan kudirin dokar hukumar leken asiri da binciken sirri ta shekarar 2024, wanda kwamitin majalisar kan harkokin tsaro da leken asiri ya shirya a harabar majalisar dokokin kasar da ke Abuja ranar Laraba.Kakakin majalisar wanda ya samu wakilcin mamba mai wakiltar mazabar Ilorin ta Yamma/Asa, Honarabul Muktar Shagaya, ya ce, kawo sauye-sauye a fannin tsaro ya zama abinda aka fi mayar da hankali, kuma yanzu dole a tashi daga rubutu kawai zuwa aiwatar da cikakken tsari.Shugaban majalisar ya ce kafa ‘yansandan jihohi ta...
    An kashe wani yaro ɗan shekara 13 mai suna Abubakar Wada da shanu 36, yayin da wasu ’yan bindiga sun kai wa makiyaya hari a kusa da ƙauyen Inzon da ke yankin Fan, a Ƙaramar Hukumar Barkin Ladi a Jihar Filato. Aƙalla shanu 49 kuma sun ɓace ba tare da sanin inda suka shiga ba. ’Yan sanda sun kama ɗan bindiga a kan iyakar Najeriya da Kamaru Kamfanonin rarraba lantarki sun tafka asarar biliyan 358 a cikin wata uku – NERC Shugaban ƙungiyar makiyaya ta Miyetti Allah (MACBAN), a Jihar Filato, Ibrahim Yusuf Babayo, ya bayyana cewa harin ya faru ne da yammacin ranar Talata lokacin da wasu makiyaya uku ke dawowa daga kiwo. Ya ce ’yan bindigar sun buɗe...
    Rundunar ’Yan Sandan Jihar Gombe, ta kama wani mutum da ake zargin ɗan bindiga ne da ke aiki tsakanin iyakar Najeriya da Kamaru. Rundunar ta kuma ƙwato bindigogi ƙirar AK-47 guda biyu, harsasai 80 da wasu tarin makamai. Gwamnatin Gombe ta kafa hukumar bunkasa fasahar zamani da tattalin arziƙi Yadda Obasanjo ya ƙaddamar da cibiyar taron ƙasa da ƙasa a Bauchi Kakakin rundunar, DSP Buhari Abdullahi, ya bayyana cewa wanda aka kama, Adamu Adamu, mai shekaru 30, ɗan asalin Ƙaramar Hukumar Song a Jihar Adamawa. Amma wanda aka kama mazaunin unguwar Jauro Jatau da ke Akko, Jihar Gombe. An kama shi ne ranar 4 ga watan Oktoba, 2025, bayan samun sahihan bayanai da suka nuna cewa yana tare da wata...
    ShareTweetSendShareMASU ALAKA Manyan LabaraiBoko Haram Ta Taɓa Ayyana Buhari A Matsayin Wanda Zai Yi Mata Sulhu Da Gwamnati – Dalung October 8, 2025Manyan Labarai‘Yan Nijeriya Sama Da Miliyan 33 Ne Ke Fama Da Matsananciyar Yunwa – Akpabio October 8, 2025Manyan LabaraiDa Ɗumi-ɗumi: Yakubu Ya Miƙa Ragamar INEC Ga Agbamuche-Mbu A Matsayin Shugabar Riƙo October 7, 2025
    Wasu da ake zargin ’yan bindiga ne, sun tare hanyar Gusau zuwa Gummi a Jihar Zamfara, inda suka sace mutane da dama. Wata majiya ta bayyana cewa, maharan sun tare motoci sannan suka yi awon gava da fasinjojin da ke ciki. Yadda Obasanjo ya ƙaddamar da cibiyar taron ƙasa da ƙasa a Bauchi Ban yi murabus don ina da laifi ba — Nnaji Wani shaida ya ce ’yan bindigar sun ɗauki lokaci suna sharafinsu kafin daga bisani suka tafi da mutanen da suka kama. Daga cikin waɗanda suka sace akwai Malam Sadis Isa, shugaban Majalisar Malamai ta Ƙaramar Hukumar Gummi, abin da ya jefa al’umma cikin tsoro da damuwa. “Da yammacin ranar Talata, ’yan bindiga sun tare hanyar Gusau zuwa...
    Tsohon Shugaban Ƙasa, Olusegun Obasanjo, ya ƙaddamar da sabon ginin Cibiyar Taron Ƙasa da Ƙasa, wadda aka sanya wa sunan Sir Ahmadu Bello a Jihar Bauchi. An ƙaddamar da cibiyar ne kafin babban taron zuba jari da nufin bunkasa kasuwanci da masana’antu a jihar. Ban yi murabus don ina da laifi ba — Nnaji Kamfanonin rarraba lantarki sun tafka asarar biliyan 358 a cikin wata uku – NERC A jawabinsa, Obasanjo ya yaba wa Gwamna Bala Mohammed, bisa irin ayyukan raya ƙasa da yake aiwatarwa, waɗanda ke inganta rayuwar jama’a. “Na yi farin ciki da abin da na gani da kuma abin da na ji. Ban zata cewa zan dawo Bauchi cikin ƙanƙanin lokaci don buɗe irin wannan katafaren waje...
    Hukumar da ke Kula da Wutar Lantarki ta Najeriya (NERC) ta ce kamfanonin rarraba wutar lantarki guda 11 sun tara Naira biliyan 546.71 daga hannun abokan cinikinsu a cikin zango na biyu na shekarar 2025. Sai dai hukumar ta ce wannan adadi bai kai kaso 60 cikin 100 na wutar da aka tura musu daga babbar hanyar rarraba wuta ba, sakamakon matsalolin lissafin wutar da suka karɓa da kuma yadda aka raba wutar ga rukunan abokan ciniki daban-daban. Zulum ya ba ma’aikaciyar lafiya ’yar kabilar Igbo kyautar gida, ya ba danta aiki Matar aure mai ’ya’ya huɗu ta rataye kanta a Jigawa Hakan, a cewar hukumar, ya haifar da gibin biyan kuɗi na naira biliyan 167.25. kazalika, NERC ta ce...
    Gwamnan Jihar Borno, Babagana Umara Zulum, ya bai wa wata ma’aikaciyar lafiya ’yar ƙabilar Igbo kuma ‘yar asalin jihar Anambra, Marbel Ijeoma Duaka, kyautar gida mai dakuna biyu. Gwamnan ya kuma ba ɗan ma’aikaciyar aikin yi na dinidindin saboda jajircewarta da sadaukarwa wajen hidimtawa jihar na sama da shekara 20. Matar aure mai ’ya’ya huɗu ta rataye kanta a Jigawa Joash Amupitan na iya zama sabon shugaban INEC Gwamnan ya bayyana hakan ne a ranar Talata yayin rabon gidaje 72 ga malamai da ma’aikatan lafiya a ƙaramar hukumar Mafa. Zulum ya ce Marbel ta shafe fiye da shekaru 24 tana aiki a cibiyar kula da lafiya ta matakin farko da ke Mafa, kuma ba ta taɓa barin wurin ba ko...
    “Yanzu muna kammala sabbin sharuɗan aikin da ASUU ta gabatar, kuma za mu bayyana amsar gwamnati nan ba da jimawa ba,” in ji shi.“Shugaba Tinubu yana da niyyar kawo ƙarshen wannan matsala gaba ɗaya.”Ya roƙi ASUU da ta ci gaba da tattaunawa maimakon fara yajin aiki, yana mai tabbatar da cewa gwamnati na da niyyar gaskiya da jajircewa wajen warware matsalar.LEADERSHIP ta ruwaito cewa ASUU ta fara shirin tursasa wa mambobinta fara yajin aikin gargadi, yayin da wa’adin kwanaki 14 da ta bai wa gwamnati zai ƙare a ranar Lahadi mai zuwa.ShareTweetSendShareMASU ALAKA Manyan LabaraiBoko Haram Ta Taɓa Ayyana Buhari A Matsayin Wanda Zai Yi Mata Sulhu Da Gwamnati – Dalung October 8, 2025Labarai‘Yansanda Sun Kama Masu Laifi 153, Sun Ƙwato...
    Al’umma a kauyen Sumore da ke Ƙaramar Hukumar Dutse a Jihar Jigawa sun shiga cikin alhini bayan mutuwar wata mata mai shekaru 30, Adama Hannafi, wacce ake zargin ta rataye kanta. Lamarin, wanda ya faru a ranar Talata, ya tayar da hankulan mazauna kan ƙalubalen da ke tattare da rashin lafiyar kwakwalwa a cikin al’umma, musamman a yankunan karkara. ‘Akwai ɗaliban da ke yin digiri yanzu ba tare da sun taɓa shiga ɗakin karatu ba saboda AI’ Joash Amupitan na iya zama sabon shugaban INEC Mai magana da yawun rundunar ’yan sandan jihar, SP Lawan Shi’isu Adam, ya tabbatar da faruwar lamarin, yana mai cewa an samu gawar matar a rataye a jikin wata bishiya a kauyen. “Mun samu kiran...
    Shugabar Cibiyar Nazarin Karatu da Ci Gaban Ilimi ta Najeriya (NCRRD) da ke Jami’ar Bayero Kano (BUK), Farfesa Amina Adamu, ta bayyana damuwa kan yadda dalibai ke ƙara gujewa amfani da dakunan karatu, tana danganta hakan da dogaro da kirkirarriyar fasaha ta AI. Da take jawabi a taron ƙasa da ƙasa karo na biyar kan nazarin karatu da nazari da aka gudanar a Jami’ar Bayero Kano, Farfesa Amina ta ce da dama daga cikin ɗalibai yanzu suna kammala karatun jami’a ba tare da sun taɓa shiga ɗakin karatu ko sau ɗaya ba. Yadda zargin mallakar takardun bogi ya yi awon gaba da kujerar Ministan Tinubu Joash Amupitan na iya zama sabon shugaban INEC “Muna da daliban da ke yin rajista...
    Ya buƙaci jama’a suke bambanta “gaskiya da siyasa.”ShareTweetSendShareMASU ALAKA Manyan Labarai‘Yan Nijeriya Sama Da Miliyan 33 Ne Ke Fama Da Matsananciyar Yunwa – Akpabio October 8, 2025Manyan LabaraiDa Ɗumi-ɗumi: Yakubu Ya Miƙa Ragamar INEC Ga Agbamuche-Mbu A Matsayin Shugabar Riƙo October 7, 2025Manyan LabaraiYa Kamata Nijeriya Ta Ayyana Yaƙi Da ‘Yan Ta’adda — Tsohon Hafsan Sojin Ƙasa October 7, 2025
    Shugaban hukumar makamashin nukiliya ta Iran ya jaddada cewa: Iran ba zata daina samar da magungunan da take yi ta hanyar fasahar makamashin nukiliya ba Kakakin Kwamitin Tsaro da Harkokin Waje na Majalisar Shawarar Musulunci (wato Majalisar Dokoki) Ibrahim Reza’ei, ya tabbatar da cewa ana ci gaba da samar da magungunan ta hanyar fasahar makamashin nukiliya a Iran, kuma ba a taba dainawa ba, kuma za a ci gaba da gudanarwa. Reza’i ya bayyana cewa: Kwamitin tsaron kasar ya gudanar da zaman hadin gwiwa tare da shugaban hukumar makamashin nukiliya ta Iran (AEOI), Mohammad Eslami, da wasu jami’an kungiyar. Islami ya gabatar da wani rahoto kan ci gaban da aka samu a fannin makamashin nukiliya, da hasarar da aka samu...
    Haka kuma ya buƙaci a aiwatar da gyare-gyare don farfaɗo da tattalin arziƙi, inganta ilimi da kiwon lafiya, tare da samar da damammaki ga matasa.Ya ƙara da cewa majalisar za ta sake duba Kundin Tsarin Mulki na 1999 domin bunƙasa dimokuraɗiyya da inganta mulki a Nijeriya.ShareTweetSendShareMASU ALAKA Manyan LabaraiDa Ɗumi-ɗumi: Yakubu Ya Miƙa Ragamar INEC Ga Agbamuche-Mbu A Matsayin Shugabar Riƙo October 7, 2025Manyan LabaraiYa Kamata Nijeriya Ta Ayyana Yaƙi Da ‘Yan Ta’adda — Tsohon Hafsan Sojin Ƙasa October 7, 2025Manyan LabaraiTinubu Ya Bayar Da Umarnin Rage Kuɗin Aikin Hajjin 2026 October 7, 2025
    Uche Nnaji, Ministan Ƙirƙira, Kimiyya da Fasaha, ya yi murabus daga mukaminsa. Mai magana da yawun shugaban ƙasa, Bayo Onanuga, ne ya tabbatar da hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar da yammacin ranar Talata. Joash Amupitan na iya zama sabon shugaban INEC Jerin ministocin da zargin takardun bogi ya tabaibaye su Nnaji na fuskantar zarge-zarge kan sahihancin takardun karatunsa, inda binciken da jaridar Premium Times ta gudanar ya gano cewa Jami’ar Najeriya da ke Nsukka (UNN) ta ce ba ta ba shi takardar kammala digiri ba. A cewar jami’ar, tsohon Ministan bai kammala karatunsa a cikinta ba, kuma ba ta taɓa ba shi takardar shaidar kammala ta ba. A cewar jaridar, Simon U. Ortuanya, Shugaban Jami’ar UNN, ya...
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba A zamanin nan, ana alakanta almajirai da bara – hasali ma a lokuta da dama akan yi amfani da kalmar “almajiri” idan ana nufin mabaraci. Amma a da ba haka lamarin yake ba – almajiri baya bukatar yin bara ko roko kafin ya sami na sakawa a bakin salati. NAJERIYA A YAU: Tasirin Takardun Shaida Na Bogi Ga Rayuwar Al’umma DAGA LARABA: Tasirin Bambance-bambance Tsakanin ‘Yan Najeriya Shekara 65 Da Samun ‘Yancin Kai Shirin Daga Laraba na wannan mako zai yi nazari ne a kan yadda almajirci ya sauya salo a wannan zamani da ma irin halin da almajirai suka tsinci kan su a ciki. Domin sauke shirin, latsa nan
    Ya gargadi masu kafa kungiyoyi daban-daban a Arewa, yana kiran irin waɗannan ƙungiyoyi “barazana ga haɗin kan Arewa.” Haka kuma ya yaba wa sojojin Nijeriya bisa kokarinsu da sadaukarwa wajen yaki da matsalar tsaro. Alhaji Dalhatu ya kuma yi Allah wadai da “ƙungiyoyin marasa kishin ƙasa” da suka jawo rikicin baya-bayan nan a matatar mai ta Dangote, tare da kira ga Gwamnatin Tarayya da ta shiga tsakani. A cewarsa, kwanan nan an samu rikice-rikicen maganganu masu karo da juna daga wasu jami’an ACF a matakin kasa da jihohi, wanda hakan ya sa dole a kafa tsarin sadarwa mai tsauri. “Majalisar Amintattu tana da ikon da nauyin Ya bayyana cewa taron, wanda shugabannin jihohi, sakatarori, da mambobin Arewa 100% Focus Group suka halarta, zai...
    Shugaban ofishin jagoran juyin musulunci na Iran, Hujjatul Islam Wal Muslimina Muhammad Gulpayagani ya bayyana yunkurin nan na: Goyon Bayan Iran.” Da cewa, aikin da suke yi yana a karkashin amsa kiran jagoran juyi ne wanda ya yi kira da a taimakawa waddanda su ka cutu daga hare-haren HKI. Kamfanin dillancin labarun “Mehr” ya nakalto Hujjatul-Islam Muhammad Gulpayagani yana bayyana muhimmin matakin da Ayatullah Khamnei yake dauka a fagen gwgawarmaya, yana mai kara da cewa; Shi ne wanda yake dauke da tutar gwgawarmaya akan wannan tafarkin cikin dogara da Allah madaukakin sarki da tafiya akan tafarkin Ahlul Bayti ( a.s). Hujjatul-Islam golpayagani ya ambaci wasu ayyukan da yukurin na Iran take yi wajen taimakawa wadanda su ka cutu daga hare-haren...
    Hukumar kula da yan gudun hijirar a majalisar dinkin duniya ta jinjinawa kasar Iran game da kokarin da tayi wajen kulawa da miliyoyin yan gudun hijira kasar Afghanistan , da suka zauna a kasar na tsawon shekaru, Babban darakta na hukumar ta IOM shi ne yayi wannan bayani ga Mohammad Batgae mtaimakin ministan harkokin cikin gidan kasar iran a birnin janeva a jiya litinin, a wani taro da suka gudanar a bayan babban taron Majalisar dinkin duniya karo na 76 da hukumar kula da yan gudun hijira ta majalisar dinkin duniya take gudanarwa. Ana sa bangaren bathaei babban jami’I na kasar Iran ya bayyan yadda jamhuriyar musulunci suka bada kula ta musamman  ga dubban yan gudun hijiran kasar ta Afghanistan...
    Majalisar Wakilai ta fara yunkurin kafa dokar da za ta daidaita harkokin kudin zamani na Crypto da kuma harkokin POS a Najeriya. Shugaban  majalisar, Abbas Tajudeen, ya ce yin hakan ya zama dole saboda yadda damuwa ke karuwa kan zamba, laifukan intanet, daukar nauyin ta’addanci da cin zarafin masu amfani da irin wadannan hanyoyin kudi. Ya ce, “Akwai damuwa ta gaskiya kan yadda ake iya amfani da kudin zamani wajen daukar nauyin ta’addanci da safarar kudaden haram, la’akari da yadda tsarin yake da duhu, dole a yi tsayayyiyar doka  doka ba, da kuma  cikakken binciken yadda ake sarrafa kudaden.” Abba ya bayyana haka ne a yayin kaddamar da wani kwamitin wucin gadi a ranar Litinin domin nazarin tasirin tattalin arziki,...
    A cewarsa, gyaran yana taimakawa wajen samun bayanai daidai domin tsara ci gaba da kuma rarraba albarkatun ƙasa bisa adalci daga gwamnatin tarayya.“Wannan tsarin yana daidai da yadda ake yi a wasu jihohi, inda ake amfani da bayanan masarautu, yankuna da ƙauyuka wajen tsara ci gaba da rarraba kuɗaɗe,” in ji shi.Gwamnan ya jaddada muhimmancin sarakunan gargajiya wajen haɗa kan jama’a da tallafa wa ayyukan ci gaba, tare da tabbatar da cewa za a aiwatar da sabon tsarin cikin gaskiya.Ya yaba wa kwamitin bisa jajircewarsu da yadda suka gudanar da aikin cikin gaskiya da tsari.Tun da farko, shugaban kwamitin, Hamza Koshe Akuyam, ya bayyana cewa sun karɓi buƙatu 196, wanda 17 don kafa sabbin masarautu, 166 don sabbin yankuna, da...
    An yi wa yara miliyan biyu da dubu takwas allura, yayin aikin rigakafin cutar Polio, kyanda, da kuma Gaida a jihar Sakkwato.   Gwamna Ahmed Aliyu Sokoto ya bayyana haka a wajen kaddamar da shirin da aka gudanar a garin Bodinga da ke karamar hukumar Bodinga.   Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Daraktan hulda da manema labarai na ofishin mataimakin gwamnan jihar, Garba Muhammed, Alhaji Ahmed Aliyu ya raba wa manema labarai, ya bayyana cewa aikin polio din zai gudana ne a daukacin unguwanni 244 dake fadin jihar.   Don haka ya yi kira ga shugabannin al’umma da na addini da kuma abokan ci gaba da masu ruwa da tsaki da su ba da himma wajen...
    Ya gode wa Shugaba Bola Tinubu da shugabannin tsaro bisa goyon bayansu wajen yaƙi da rashin tsaro a Kogi.Tags: KogiOdodoTsaroShareTweetSendShare Sadiq Related LabaraiMajalisar Wakilai Ta Kafa Kwamiti Da Zai Binciki Harkokin Kirifto Da POS A Nijeriya 1 hour agoManyan LabaraiYa Kamata Nijeriya Ta Ayyana Yaƙi Da ‘Yan Ta’adda — Tsohon Hafsan Sojin Ƙasa 2 hours agoManyan LabaraiTinubu Ya Bayar Da Umarnin Rage Kuɗin Aikin Hajjin 2026 3 hours ago
    Al’ummar Ƙaramar Hukumar Kebbe da ke Jihar Sakkwato sun roƙi gwamnati ta ba su dama su riƙa ɗaukar makamai domin kare kansu daga hare-haren ’yan bindiga da suka addabi yankinsu. Mutanen sun ce sun gaji da kashe-kashe, sace-sace, da kona gidaje da gonakinsu da ’yan bindiga ke yi, wanda ke jefa su cikin tsananin wahala da asara. Mazauna yankin sun ce daga cikin garuruwa 17 da ke cikin Ƙaramar Hukumar Kebbe, an riga an raba mazauna akalla 11 da gidajensu saboda yawan hare-hare. Wani shugaban al’umma a yankin, Tukur Muhammad Fakum, ya shaida wa BBC cewa halin da suke ciki ya sa suka fara tunanin yadda za su kare kansu da kansu. Ya kamata a karɓe ikon naɗa Shugaban INEC...
    A wani bangare na kudirinta na bunkasa tattalin arzikin mata, gwamnatin jihar Kano ta bayyana shirinta na shirya tarurrukan horaswa kan kula da tsaftar madara, da shirya kayayyaki, da dabarun kiyayewa ga mata masu sayar da madara ko nono a fadin jihar.   Kwamishiniyar harkokin mata da yara da masu bukatu ta musamman Ambasada Amina Abdullahi Sani ta bayyana hakan a wata ziyarar aiki da ta kai kasuwar masu sayar da madarar mata (Nono Sellers) dake kan titin Zaria a Kano.   A cewar kwamishinan, ziyarar na da nufin tantance yanayin da kasuwar ke ciki da kuma lalubo hanyoyin da za a bi don inganta yanayin aiki da kuma sa’o’in na mata masu sana’ar sayar da kayayyaki a can.  ...
    Al’ummar Ƙaramar Hukumar Kebbe da ke Jihar Sakkwato sun roƙi gwamnati ta ba su dama su riƙa ɗaukar makamai domin kare kansu daga hare-haren ’yan bindiga da suka addabi yankinsu. Mutanen sun ce sun gaji da kashe-kashe, sace-sace, da kona gidaje da gonakinsu da ’yan bindiga ke yi, wanda ke jefa su cikin tsananin wahala da asara. Mazauna yankin sun ce daga cikin garuruwa 17 da ke cikin Ƙaramar Hukumar Kebbe, an riga an raba mazauna akalla 11 da gidajensu saboda yawan hare-hare. Wani shugaban al’umma a yankin, Tukur Muhammad Fakum, ya shaida wa BBC cewa halin da suke ciki ya sa suka fara tunanin yadda za su kare kansu da kansu. Ya kamata a karɓe ikon naɗa Shugaban INEC...
    Ya ƙara da cewa kwamitin zai gudanar da zaman jin ra’ayoyi daga masana da sauran masu ruwa da tsaki kafin ya kammala rahotonsa.Tags: BincikeKiriftoKwamitiMajalisar WakilaiPOSShareTweetSendShare Sadiq Related Manyan LabaraiYa Kamata Nijeriya Ta Ayyana Yaƙi Da ‘Yan Ta’adda — Tsohon Hafsan Sojin Ƙasa 1 hour agoManyan LabaraiTinubu Ya Bayar Da Umarnin Rage Kuɗin Aikin Hajjin 2026 2 hours agoManyan LabaraiKada Ku Yi Sanadiyar Rugujewar Matatar Mai Ta Dangote – Shettima Ga PENGASSAN  14 hours ago
    Takardun shaida na bogi na daya daga cikin matsaloli dake kara addabar Najeriya a fannoni da dama.   A wasu lokuta ana samun mutane da ke amfani da takardun makaranta ko na ƙwarewa da ba su cancanta da su ba domin samun aiki, mukami, ko wasu fa’idodi da suka wajaba ne kawai ga waɗanda suka cancanta. Wannan dabi’a ta zama barazana ga ci gaban ƙasa da amincin al’umma gaba ɗaya, domin tana lalata tsarin ilimi, rage darajar masu gaskiya, da haifar da rashin inganci a wuraren aiki. Haka kuma, tana haifar da rashin amincewa tsakanin gwamnati da jama’a, da kuma tsakanin mutane da kansu. NAJERIYA A YAU: ‘Halin Kunci Ya Sa Muke Zama A Baca A Abuja’ DAGA LARABA: Tasirin...
    Irabor ya ƙara da cewa dole ne gwamnati ta bi hanyoyi daban-daban wajen magance matsalar tsaro, ba ta hanyar amfani da sojoji kaɗai ba.Ya ce ya kamata a samar da manufofi masu inganci da za su rage talauci, rashin aiki da yawan yara marasa zuwa makaranta.“Idan muka rage yara marasa zuwa makaranta da kuma marasa aikin yi, za mu rage yawan mutanen da ‘yan ta’adda ke iya ɗauka aiki,” in ji shi.Ya kuma gargaɗi ‘yan siyasa da su daina sa siyasa a batun harkar tsaro.A ranar bikin cikar Nijeriya shekara 65 da samun ‘yancin kai, Shugaba Bola Tinubu ya bayyana cewa dakarun Nijeriya suna samun nasara a yaƙi da ta’addanci da garkuwa da mutane, amma jam’iyyun adawa sun ce matsalar...
    A yayin Ministan Kimiyya, Fasaha da Ƙirƙire-ƙirƙire, Uche Nnaji, ke fuskantar matsin lamba bayan ya amsa a gaban kotu cewa Jami’ar Najeriya da ke Nsukka (UNN) ba ta taɓa ba shi takardar digiri ba, zargin sa da amfani da takardun bogi da kafar PREMIUM TIMES ta bankaɗo ya ƙara ƙarfi. Fadar Shugaban Ƙasa ta ce za ta jira hukuncin kotu kafin ta ɗauki mataki kan batun Nnaji. Wannan ya sanya Mista Nnaji cikin jerin wasu ministoci da suka fuskanci irin wannan tuhuma: – Uche Nnaji Uche Nnaji, wanda Shugaba Bola Tinubu ya nada a watan Yuli 2023, ya gabatar da takardar digiri da kuma takardar kammala aikin NYSC a lokacin tantancewa. Amma jami’ar UNN da hukumar NYSC sun ce ba...
    Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya umarci Hukumar Aikin Hajji ta Ƙasa (NAHCON) ta sake rage kuɗin aikin Hajjin shekarar 2026 nan take, kuma ta fitar da sabon farashin cikin kwana biyu. Wannan na zuwa ne kwanaki kaɗan bayan hukumar ta sanar da rafin kimanin N200,000 a kan farashin da maniyyata suka biya a bara. Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ne ya isar da umarnin shugaban kasa yayin wani taro da ya yi da shugabanni da mambobin hukumar NAHCON a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja, a ranar Litinin. Shettima ya buƙaci a samu hadin kai tsakanin jami’an jihohi da na tarayya, ciki har da gwamnoni, wajen fitar sabon farashin da ya dace da yanayin tattalin arzikin ƙasar. An fara...
    Wasu da ake zargin makiyaya ne sun kai farmaki a wata gonar wake, inda suka kashe wani mai gonar yana tsaka da aiki a Ƙaramar Hukumar Monguno da ke Jihar Borno. Shaidu sun ce makiyaya kimanin 10 ne  suka kai harin bayan sun kutsa da shanunsu suka yi kiwo a wasu gonaki da misalin ƙarfe 12:20 na  ranar Asarar a Dajin Ngolom. Ɗaya daga cikin manoman da makiyayan suka kutsa gonarsu, Abatcha Abatcha da ke yankin Gana Ali Ward, manoman sun buƙaci makiyayan su bar gonakin, amma sai lamarin ya rikice zuwa tashin hankali. “Makiyaya sun kai mana hari da sanduna. Ɗaya daga cikin manoman da Allah Ya yi wa rasuwa, Bakulu Bafindi mai shekaru 30 daga unguwar Sabon Lamba...
    A gobe Talata ce 7 ga watan Otoba, yakin tufanul-Aksa ya ke cika shekaru 2 tsakanin HKI da kungiyar Hamas wacce take iko da zirin gaza na kasar Falasdinu da aka mamaye. Jaridar ‘The National’ na kasar Amurka ta nakalto firay ministan HKI Benyamin Natanyahu yana cewa gwamnatinsa tana samun nasara a yakin, duk da cewa abinda yake kasa yana nuna akasin haka. Musamman idan an dubi manufofin HKI na fara shiga yakin. Wasu masana a HKI basu amince da da cewa Natanyahu yana samun nasara a wannan yakin ba. Wanda shi ne yaki mafi tsawo wanda HKI ta shiga tun bayan kafata shekaru kimani 80 da suka gabaya. Jaridar ‘The Nation’ ta yi hira da Nimrod Novik daya daga...
    Ya kuma tabbatar da cewa Gwamnatin Tarayya tana aiki don ƙirƙirar yanayi mai sauƙin zuba jari, da zaman lafiya don masana’antu, da haɓaka tattalin arziki mai dorewa. A ƙarshe, ya kira masu ruwa da tsaki da su fifita tattaunawa a wajen neman mafita maimakon rikici, yana cewa, “Nijeriya ƙasa ce mai girma da ke neman mafita a abubuwa da yawa, ya zama dole ne mu haɗa kai wajen kare abin da ke amfanar ƙasa baki ɗaya.” Tags: Aliko DangoteShettima ShareTweetSendShare Abubakar Sulaiman Related Manyan Labarai Talaucin Da Ya Ninku Fiye Da Sau Biyu A Gwamnatin Tinubu, An Ƙuduri Aniyar Kawar Da Shi Nan Da Shekaru 5 4 hours ago Manyan Labarai Uba Sani Ya Amince...
      Manufofin da aka tsara sun karfafa kashe kudi. Kafin wannan hutu, gwamnatin tsakiya ta ware yuan biliyan 69 kwatankwacin dalar Amurka biliyan 9.7 a matsayin lamuni na musamman don tallafa wa hada-hadar kayayyakin masarufi, wanda hakan ya kai ga jimillar abin da ake warewa a shekara ta kai yuan biliyan 300. Daga watan Janairu zuwa na Agusta, shirye-shiryen ba da tallafi na hada-hadar kasuwanci sun jawo hankulan masu nema miliyan 330, wanda hakan ya haifar da cinikin sama da yuan tiriliyan 2. (Abdulrazaq Yahuza Jere)     ShareTweetSendShare Sulaiman Related Daga Birnin Sin Karamin Ofishin Jakadancin Sin Da Ke Legas Ya Yi Bikin Bunkasa Al’adu Na Bikin Tsakiyar Kaka 1 hour ago Daga Birnin...
    A zaman da aka yi a yau, lauyan Ministan ya shaidawa kotu cewa an isar da takardun shari’ar ga dukkan waɗanda ake ƙara, yana mai zargin Shugaban Jami’ar UNN da saɓa umarnin kotu ta hanyar rubuta wasika ga jaridar yanar gizo Premium Times, inda ya ƙalubalanci ikirarin Nnaji na cewa tsohon ɗalibin jami’ar ne. A cewar lauyan, wannan wallafa ta karya umarnin kotu na barin komai a yadda yake har sai an saurari shari’ar. Sai dai lauyan jami’ar ya musanta yin wani kuskure, amma ya ce za su ja hankalin jami’an su don bin umarnin kotu yadda doka ta tanada. Tags: MinistaNnajiUNN ShareTweetSendShare Naziru Adam Ibrahim Related Ilimi Uwargidan Shugaban Ƙasa, Remi Tinubu, Ta Nuna Damuwa...
    A cewar Bankin Duniya, talauci a tsakanin mazauna karkarar Nijeriya ya kai kashi 75.5 cikin dari, wanda ke nuna ƙaruwar rashin daidaito da kuma tsananin matsin tattalin arziki a fadin kasar.   Ministan ya ce, gwamnati ta kuma kuduri aniyar inganta hasashen tattalin arziki da inganta sauye-sauyen da zai sanya Nijeriya ta samu ci gaba mai ɗorewa.   Bagudu ya jaddada cewa, gwamnatin da shugaban kasa Bola Tinubu ke jagoranta tana ba da fifiko wajen samar da ayyukan yi ta fuskar fasahar zamani, noma, tattalin arziki da ƙirƙire-ƙirƙire. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake...
    Daga Abdullahi Usman, Kaduna Sardaunan Ikulu, Alhaji Dr. Isma’īl Yusuf Ashafa, ya kira mata da matasa a garin Ikulu da su shiga harkokin siyasa domin kawo ci gaba a yankinsu. Ya fadi hakan ne a lokacin Taron Ikulu da aka shirya a Kaduna karkashin jagorancin Ikulu Political Forum (IPF). Ya jaddada cewa babu wata al’umma da za ta bunkasa sai an samu hadin kai tsakanin jama’a da kuma cikakkiyar rawar da matasa da mata ke takawa a siyasa. Ya kara da cewa wajibi ne a wayar da kan matasa da mata, a ilimantar da su, sannan a motsa su su gane muhimmancin jagoranci ta hanyar jam’iyyun siyasa. Hakazalika, ya gargadi ‘yan siyasa a yankin da su guji “siyasar do ko...
      Ya kara da cewa yan shekarun da suka gabata, an yi shakku kan dorewar wasan Hockey a Nijeriya, amma yanzu tawagarmu ta mata ita ce ta zo matsayi na 3 a Afirka, yayin da tawagar maza ke matsayi na 4, wadannan nasarorin sun nuna irin yadda muka himmatu wajen ganin mun kara inganta wannan wasa a Nijeriya. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Firaministan ƙasar Faransa, Sebastien Lecornu, ya yi murabus daga muƙaminsa kwana guda bayan ya kafa gwamnatinsa. Fira Minista Sebastien Lecournu ya sanar da ajiye mukaminsa ne a safiyar Litinin ɗin nan bayan ya yi wata da Shugaba Emmanuel Macron. Ya yi murabus ne washegarin da ya kafa majalisar ministocinsa domin tafiyar da gwamnati, kuma ƙasa da wata guda bayan Shugaba Macron ya naɗa shi a kujerar. A jiya  Lahadi ne ya sanar da sunayen mambobin sabuwar majalisar ministocinsa inda ya naɗa sabbin muƙamai, amma ya bar wasu da dama a kan kujerunsu, lamarin da bai yi wa ’yan adawa daɗi ba. Zargin takardun bogi: Jami’ar Nsukka ba ta taɓa ba ni takardar digiri ba — Minista ’Yan bindiga sun kashe...
    Ana tsaka da Sallah ’yan bindiga suka karbe wani mutum har lahira sa’annan suka yi garkuwa da basarake a ƙauyen Rani Ramat da ke Ƙaramar Hukumar Patigi a Jihar Kwara. Al’ummar yankin sun ce maharan sun kai farmaki ne a kan babura a yayin da ake Sallar Magariba ranar Lahadi inda suka rika harbi babu ƙaƙƙautawa. A yayin da jama’a ke guje-gujen neman tsira ne ’yan bindigar suka harbe wani mutum. Daga nan suka yi awon gaba da basaraken ƙauyen mai suna Alhaji Ndako, zuwa inda ba a sani ba. Mazauna yankin sun bayyana cewa ’yan bindigar sun shafe sa’o’i suna cin karensu babu babbaka kafin su koma cikin daji. Kwamitin gwamnati ya ba da shawarar ƙirƙirar sababbin masarautu 13...
    Kwamitin da Gwamnatin Jihar Bauchi ta kafa domin nazarin buƙatun ƙirƙirar sababbin masarautu da yankunan hakimai da dagattai, ya ba da shawarar ƙirƙirar masarautu 13, da hakimai 2 da dagattai 113 a fadin jihar. Wannan shawara na kunshe ne a cikin rahoton da shugaban kwamitin, Hamza Koshe Akuyam, ya miƙa wa Gwamna Bala Mohammed a ofishinsa da ke Bauchi. Da yake miƙa rahoton, Akuyam ya bayyana cewa masarautu 13 da yankunan hakimai biyu da aka bayar da shawarar kafa su su ne suka cancanta daga cikin sama da buƙatu 100 da aka karɓa daga sassan jihar daban-daban. Kwamitin, an kaddamar da shi ne a ranar 4 ga Yuli 2025, da umarnin ya duba buƙatun al’ummomi, ya tantance dalilan tarihi, al’ada da...
    Iran ta sanar cewa tana goyon bayan “duk wani shiri” da zai ba da damar samar da ‘yancin kai ga al’ummar Falasdinu, gabanin tattaunawa da ake shirin farawa a Masar tsakanin Isra’ila da Hamas da nufin kawo karshen yakin zirin Gaza. A cikin wata sanarwa da ma’aikatar harkokin wajen kasar ta fitar, iran ta ce “a ko da yaushe tana goyon bayan duk wani yunkuri na kawo karshen laifukan yaki, da cin zarafin bil’adama a Gaza da duk wani yunkuri na share fagen tabbatar da ‘yancin kai na al’ummar Palasdinu.” Sanarwar ta ce, tilas ne yanke duk wata shawara kan tsagaita bude wuta ko sasantawa ta siyasa ta rataya a wuyan Falasdinawa da kansu. Tehran ta ce tana maraba da...
    Jam’iyyar ADC ta zargi Shugaba Bola Ahmed Tinubu da rashin mayar da hankali kan yadda matsalar tsaro ke ƙara taɓarɓarewa a ƙasar nan.  Jam’iyyar ta ce shugaban yaf i damuwa 2ajen halartar tarukan siyasa da biki, maimakon kare rayukan ’yan Najeriya. Ɓarayin daji sun kashe kwamandan maharba a Kaduna Mata da yara 95,000 ke mutuwa a sanadin shaƙar hayaƙin girki — Uwargidan Fubara A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun jam’iyyar, Mallam Bolaji Abdullahi, ya fitar, ADC ta ce maganar da Shugaba Tinubu ya yi a Cocin COCIN a Jos, na batun haɗa kan ‘yan Najeriya, ba komai ba ne illa siyasa kawai. Jam’iyyar ta ce tun da ya hau mulki, ba a ga wani mataki da ke...
    A jerin ƙarshe, birnin Quito na ƙasar Ecuador ya kasance na 40 cikin biranen da ke da mafi ƙarancin ingancin rayuwa, yayin da Delhi (Indiya) da Saint Petersburg (Rasha) suka kasance a matakai na 39 da 3 8 bi da bi.   Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Jam’iyyar ADC ta zargi Shugaba Bola Ahmed Tinubu da rashin mayar da hankali kan yadda matsalar tsaro ke ƙara taɓarɓarewa a ƙasar nan. Jam’iyyar ta ce shugaban yaf i damuwa 2ajen halartar tarukan siyasa da biki, maimakon kare rayukan ’yan Najeriya. Ɓarayin daji sun kashe kwamandan maharba a Kaduna Mata da yara 95,000 ke mutuwa a sanadin shaƙar hayaƙin girki — Uwargidan Fubara A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun jam’iyyar, Mallam Bolaji Abdullahi, ya fitar, ADC ta ce maganar da Shugaba Tinubu ya yi a Cocin COCIN a Jos, na batun haɗa kan ‘yan Najeriya, ba komai ba ne illa siyasa kawai. Jam’iyyar ta ce tun da ya hau mulki, ba a ga wani mataki da ke...
    Bisa labarin da ma’aikatar kula da harkokin sufuri ta kasar Sin ta bayar, a ranar 4 ga wannan wata, yawan mutanen da suka yi zirga-zirga a kasar Sin ya kai miliyan 301 da dubu 291 da dari 1, wanda ya karu da kashi 6.1 cikin dari bisa na makamancin lokacin bara. Yawan mutanen da suka yi zirga-zirga a rabin farko na hutun bikin kafuwar jamhuriyar jama’ar kasar Sin PRC da bikin Zhongqiu ya kai matsayin koli a tarihi, wato ya kai biliyan 1 da miliyan 243, wannan ya shaida cewa, an fi yin zirga-zirga a lokacin hutun.   Game da hanyoyin zirga-zirga a lokacin wannan hutu, an fi zabar hanyoyin mota. Game da yankunan da aka fi sha’awar ziyarta, an...
    Uwargidan Shugaban ƙasa, Sanata Remi Tinubu, ta bayyana damuwa kan yadda ake samun ƙaruwar ƙarancin malamai a duniya, tana kira da a gaggauta ɗaukar matakai na ɗaukar sabbin malamai, da horar da su, da kuma tallafa musu domin ci gaban sana’ar koyarwa. A cikin sakonta na taya murna yayin bikin Ranar Malamai ta Duniya ta 2025 mai taken “Mayar da Hankali Kan Ƙarancin Malamai a Duniya,” Uwargidan ta ce wannan matsala tana buƙatar a magance ta cikin gaggawa ta hanyar ƙarfafa wa malamai gwuiwa ƙarfi da kuma dabarun samun ƙwarewa. Remi Tinubu Ta Bai Wa Waɗanda Ambaliya Ta Shafa A Neja Tallafin N1bn Ƴan Bindiga Sun Sace Malamin Krista Na Ɗarikar Katolika A Kogi Ta bayyana malamai a matsayin “gwarazan al’umma”,...
    A karon farko a tarihin kwallon raga ta mata ta Iran ta zami lashe kofin zakarun Asiya, bayan samun galaba akan kawarta ta kasar Uzbakestan. An fara wasan fidda gwani a tsakanin kungiyoyin kwallon raga na mata na Asiya a ranar 2 ga watan nan na Oktoba, a birnin Tashqand wanda ya zo karshe a yau Lahadi da samun galabar Iran. Tun da fari kungiyar kwallon ragar ta Iran ta sami nasarori har sau uku a jere, da a karshe ta kai ga samun nasara akan mai masaukin baki kasar Uzbakestan. Mai bayar da horo ga ‘yan wasan Li Du Hi, ta bayyana jin dadinsa da nasarar da su ka samu, musamman saboda wannan ne karon farko aka sami wannan...
    Jaridar Ma’ariv ta HKI ta buga labarin da yake cewa gwamantin HKI ta kwace kudaden gwamnatin kwarya-kwarya ta Faladinu da sun kai dala miliyan 7.54 ta rabawa wasu iyalan yahudawa 41 da su ka riya cewa hare-haren Faladinawa sun yi sadaniyyar kashe musu ‘ya’ya da dangi. Jaridar ta kuma kara da cewa; An rabawa iyalan yahudawan kudin da sun kai Shakel miliyan 25 wanda shi ne kwatankwacin Dala miliyan 7.54, ta hannun lauyoyinsu. Haka nan kuma jaridar ta ce hukumar dake kula da haraji da ke karkahsin ma’aikatar shari’a ce ta aiwatar da raba kudin a matsayin abinda su ka kira diyyar ayyukan t’addanci.! Jaridar ta kuma ce tun a 2019 ne wadannan ‘yan sahayonioyar su ka bukaci a biya...
    Wasu da ake zargin ’yan fashin daji ne sun kashe ɗaya daga cikin kwamandojin maharba a yankin Gangara da ke Ƙaramar Hukumar Giwa a Jihar Kaduna. Lamarin ya faru ne a yau Asabar, 4 ga watan Oktoba, 2025, inda aka tabbatar da mutuwar Malam Kabiru, wanda yake ɗaya daga cikin kwamandojin ƙungiyar maharba ta ƙasa, reshen Giwa. Hukuma ta fara binciken Ganduje kan zargin karkatar da N4bn a Kano An yi wata gagarumar zanga-zangar goyon bayan Falasɗinawa a Turai Rahoto ya bayyana cewa Malam Kabiru ya rasu ne yayin aikin ceto wasu mutane da ’yan fashi suka sace daga yankin Danja na Jihar Katsina. Shugaban ƙungiyar maharba ta ƙasa, Kwamanda Usman Taju, ya tabbatar wa Aminiya faruwar lamarin, jim kaɗan...
    Uwargidan Gwamnan Jihar Ribas, Eyoanwan Bassey Otu, ta ce aƙalla mata da ƙananan yara 95,000 ne ke mutuwa a kowace shekara a Najeriya sakamakon shaƙar hayaƙin girki. Ta bayyana haka ne yayin wani taron wayar da kai da aka gudanar a ofishinta da ke Kalaba, inda ta jaddada buƙatar amfani da hanyoyin girki masu tsafta da aminci a Najeriya. Wike ya gana da Fubara da dattawan Ribas kafin kafa sabuwar majalisar zartarwa Rundunar Sojin Nijeriya ta cafke jami’anta 16 kan saɓa ƙa’idar aiki Uwargidan gwamnan, wacce Asi Akiba, matar ɗan Majalisar Tarayya mai wakiltar Kalaba, Kalaba ta Kudu da Odukpani ta wakilta, ta ce hayaƙin itacen girki da sauran hanyoyin da ba su da inganci sun zama hanyar mutuwa ta...
    Uwargidan Gwamnan Jihar Ribas, Eyoanwan Bassey Otu, ta ce aƙalla mata da ƙananan yara 95,000 ne ke mutuwa a kowace shekara a Najeriya sakamakon shaƙar hayaƙin girki. Ta bayyana haka ne yayin wani taron wayar da kai da aka gudanar a ofishinta da ke Kalaba, inda ta jaddada buƙatar amfani da hanyoyin girki masu tsafta da aminci a Najeriya. Wike ya gana da Fubara da dattawan Ribas kafin kafa sabuwar majalisar zartarwa Rundunar Sojin Nijeriya ta cafke jami’anta 16 kan saɓa ƙa’idar aiki Uwargidan gwamnan, wacce Asi Akiba, matar ɗan Majalisar Tarayya mai wakiltar Kalaba, Kalaba ta Kudu da Odukpani ta wakilta, ta ce hayaƙin itacen girki da sauran hanyoyin da ba su da inganci sun zama hanyar mutuwa ta...