Majalisa za ta yi dokar kula da harkar Crypto da POS
Published: 7th, October 2025 GMT
Majalisar Wakilai ta fara yunkurin kafa dokar da za ta daidaita harkokin kudin zamani na Crypto da kuma harkokin POS a Najeriya.
Shugaban majalisar, Abbas Tajudeen, ya ce yin hakan ya zama dole saboda yadda damuwa ke karuwa kan zamba, laifukan intanet, daukar nauyin ta’addanci da cin zarafin masu amfani da irin wadannan hanyoyin kudi.
Ya ce, “Akwai damuwa ta gaskiya kan yadda ake iya amfani da kudin zamani wajen daukar nauyin ta’addanci da safarar kudaden haram, la’akari da yadda tsarin yake da duhu, dole a yi tsayayyiyar doka doka ba, da kuma cikakken binciken yadda ake sarrafa kudaden.”
Abba ya bayyana haka ne a yayin kaddamar da wani kwamitin wucin gadi a ranar Litinin domin nazarin tasirin tattalin arziki, dokoki da tsaro da ke tattare da mu’amalar kudi ta zamani.
A ba mu damar ɗaukar makamai don kare kanmu daga ’yan bindiga —Sakkwatawa Ya kamata a karɓe ikon naɗa Shugaban INEC daga hannun Shugaban ƙasa — IPACYa bayyana cewa tattalin arzikin Najeriya ya nuna jajircewa sosai a cikin shekaru, inda ya farfado daga durkushewa kuma ya samu ci-gaba a sassan da ba na mai ba.
A cewarsa, hakan ya nuna cewa akwai yanayi da ya dace da cinikayyar kudin zamani. Sai dai ya gargadi cewa akwai manyan gibi da bai kamata a yi sakaci da su ba.
উৎস: Aminiya
এছাড়াও পড়ুন:
Pakistan Ta Kai Hari Kan Kasar Afganistan, Inda Ake Rade-Radin Kashe Shugaban Taliban Na Kasarta
Jiragen saman yaki sun yi luguden wuta kan birnin Kabul fadar mulkin kasar Afganistan, kuma rahotanni masu karo da juna suna cewa an kashe shugaban Taliban na Pakistan
Kafofin yada labaran Afghanistan sun yi ikirarin cewa: Sojojin Pakistan ne ke da alhakin harin da aka kai a Kabul babban birnin kasar Afganistan a yammacin ranar Alhamis.
Tashar Talabijin ta Tolo News da Khabar Online Afganistan sun ruwaito cewa: Sojojin Pakistan sun dauki alhakin hare-haren da aka kai cikin daren jiya a Kabul.
Kakakin Taliban Zabihullah Mujahid ya rubuta a dandalin X a yammacin ranar Alhamis cewa: An ji karar fashewar wani abu a birnin Kabul.
Ya kara da cewa: “Babu wata damuwa, lamarin dai kamar yadda aka saba, ana ci gaba da gudanar da bincike kan lamarin, kawo yanzu ba a samu hasarar rayuka ba.”
Majiyar leken asirin Afganistan ta shaidawa Al-Araby Al-Jadeed cewa: Shugaban Taliban na Pakistan kuma wani babban kwamandan kungiyar ya tsallake rijiya da baya a harin da Pakistan ta kai kan Kabul.
A halin da ake ciki, wasu kafafen yada labaran Afghanistan sun sanar a cikin wani rahoto da ba a tabbatar da shi ba, y ace: An kashe Mufti Noor Wali Mehsud shugaban Taliban na Pakistan a wani hari da aka kai ta sama a Kabul a daren yau.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Putin: Natanyahu Yana Son Warware Matsaloli Da Iran Cikin Lumana Ba Tare Da Yaki Ba October 10, 2025 Majalisar Turai Ta Bukaci Kasashen Nahiyar Su Kakkabo Jiragen Yakin Rasha October 10, 2025 Sa’o’ii Da Fara Janyewar Sojojin HKI A Gaza An Fara Gano Gawakin Falasdinwa October 10, 2025 Falasdinawa Daga Kudancin Gaza Sun Fara Komawa Gidajensu Da Aka Rusa A Arewacin Yankin October 10, 2025 Rahotanni : Isra’ila ta fara janye dawa wasu yankuna na Gaza October 10, 2025 Amurka ta kakaba wa wasu kamfanoni 50 takunkumi saboda sayen man Iran October 10, 2025 Isra’ila ta ce yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza ta fara aiki October 10, 2025 Mohajirani: Iran na goyon bayan shawarar Falastinawa kan batun dakatar da bude wuta October 10, 2025 Khalil al-Hayya: Mun cimma yarjejeniyar tsagaita wuta ta dindindin October 10, 2025 Ministan mai na Nijar ya gana da Jakadan Iran a Yamai October 10, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci