Jerin ministocin da zargin takardu ya tabaibaye su
Published: 7th, October 2025 GMT
A yayin Ministan Kimiyya, Fasaha da Ƙirƙire-ƙirƙire, Uche Nnaji, ke fuskantar matsin lamba bayan ya amsa a gaban kotu cewa Jami’ar Najeriya da ke Nsukka (UNN) ba ta taɓa ba shi takardar digiri ba, zargin sa da amfani da takardun bogi da kafar PREMIUM TIMES ta bankaɗo ya ƙara ƙarfi.
Fadar Shugaban Ƙasa ta ce za ta jira hukuncin kotu kafin ta ɗauki mataki kan batun Nnaji.
Wannan ya sanya Mista Nnaji cikin jerin wasu ministoci da suka fuskanci irin wannan tuhuma:
– Uche NnajiUche Nnaji, wanda Shugaba Bola Tinubu ya nada a watan Yuli 2023, ya gabatar da takardar digiri da kuma takardar kammala aikin NYSC a lokacin tantancewa. Amma jami’ar UNN da hukumar NYSC sun ce ba su da masaniya da takardun da aka gabatar.
Tinubu ya umarci NAHCON ta rage kuɗin aikin Hajjin 2026 Makiyaya sun kashe manomi a gonarsa a BornoShugaban jami’ar UNN, Farfesa Simon Ortuanya, ya tabbatar cewa an ɗauki Nnaji karatu a 1981 amma bai kammala ba.
NYSC ma ta ce takardar da Nnaji ke amfani da ita ba ta da tushe.
– Olubunmi Tunji-OjoMinistan Cikin Gida, an zarge shi da gabatar da takardar NYSC ta bogi.
Amma daga bisani NYSC ta ce takardarsa ta gaskiya ce, bayan an sake tura shi aikin a 2019.
– Stella Oduah:Taohuwar Ministar Sufurin Jiragen Sama, an zarge ta da ƙin kammala aikin NYSC a 1982.
A 2023, EFCC ta gurfanar da ita bisa zargin jabun takardu da bayanan ƙarya. Ta musanta zargin, kuma shari’ar na gaban kotu.
– Hannatu MusawaSaɓanin Nnaji da Olubumi da ake zargi da amfani da takardun bogi, da Stella Oduah da ke zargi da ƙin kammala aiki NYSC, qn yi zargin cewa Ministar Al’adu da Tattalin Arzikin Ƙirƙre-ƙirƙiye, tana cikin aikin NYSC lokacin da aka naɗa ta a 2023.
Ministar ta ci gaba da kare kanta cewa ba ta aikata laifi ba, kuma ta kammala aikin NYSC.
Kotun tarayya ta yi watsi da ƙarar da aka shigar, duk da tambayoyi da ke ci gaba da tasowa.
– Adebayo Shittu:Tsohon Ministan Sadarwa, Adebayo Shittu kuma, an zarge shi ne kan ƙin halartar aikin NYSC kasancewar ya kammala jami’a ne a lokacin da yake ɗan shekara 25.
Amma ya bayyana cewa zaɓen sa da aka yi a matsayin ɗan Majalisar Dokokin Jihar Oyo ya maye gurbin aikin, amma NYSC ta ce ba haka doka ta tanada ba.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Adebayo Shittu Takardun bogi
এছাড়াও পড়ুন:
ASUU ta tsunduma yajin aikin mako 2
Ƙungiyar Malaman Jami’o’i ta Ƙasa (ASUU), ta sanar da fara yajin aikin gargaɗi na tsawon mako biyu a dukkanin jami’o’in gwamnati da ke Najeriya.
Shugaban ASUU, Farfesa Chris Piwuna ne, ya bayyana hakan a ranar Lahadi yayin wani taron manema labarai da aka gudanar a Jami’ar Abuja.
Egbetokun ya sauke kwamishinan ’yan sandan Abuja Gwamnan Kebbi ya bai wa sojoji kyautar motoci 6 da babura 30 don inganta tsaroYa ce yajin aikin zai fara ne da tsakar daren ranar Litinin, 13 ga watan Oktoba, 2025.
ASUU, ta riga ta bai wa Gwamnatin Tarayya wa’adin kwanaki 14 wanda ya ƙare a ranar 28 ga watan Satumba, 2025.
A cewar Farfesa Piwuna, babu wani abu da aka yi don dakatar da yajin aikin, don haka dukkanin malamai za su daina aiki a lokacin yajin aiki.
Wannan yajin aikin na zuwa ne duk da cewa har yanzu gwamnati da ASUU na ci gaba da tattaunawa don warware matsalolin da suka daɗe suna fama da su.
Wasu daga cikin matsalolinsu sun shafi batun albashi, kuɗaɗen alawus-alawus, da kuma yarjejeniyar da aka cimma tun shekarar 2009 tsakanin ɓangarorin biyu.
Ministan Ilimi, Dokta Tunji Alausa, ya bayyana a ranar Laraba cewa gwamnati na matakin ƙarshe na tattaunawa da ASUU da sauran ƙungiyoyi don warware matsalolinsu.
Ya kuma ce gwamnati ta riga ta fitar da Naira biliyan 50 don biyan haƙƙoƙin malaman da suka cancanta, yayin da aka sake sakin wasu Naira biliyan 150 a kasafin kudin 2025 domin biyan buƙatun jami’o’i.