Aminiya:
2025-11-27@21:51:59 GMT

’Yan sanda sun kama wanda ake zargi da sace hakimi a 2023 a Kano

Published: 4th, October 2025 GMT

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano, ta kama wani mutum da ake zargi da hannu wajen sace Hakimin Garin Garun Babba, Alhaji Abdulmumini Mudi Zakari, a shekarar 2023.

Kakakin rundunar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa ne, ya bayyana hakan cikin wata sanarwa a ranar Asabar.

Gwamna Namadi ya raba wa mata 1,400 tallafin kayan ɗinkin hula a Jigawa Dalilin da ya sa na tsere Kamaru bayan Boko Haram ta ƙone fadata a Borno — Basarake

Ya ce an kama wanda ake zargin mai suna Usman Lawan Baba, wanda aka fi sani da “Yellow,” mai shekara 27, a ranar 2 ga watan Oktoba, 2025, a garin Dakatsalle da ke Ƙaramar Hukumar Bebeji.

Wanda ake zargin tare da wasu sun sace hakimin sannan suka ƙwace masa kuɗi har Naira miliyan 2.75, waya ƙirar Tecno Kevo 4 da kuma agogo.

Daga baya ’yan sanda sun ceto hakimin bayan sun fatattaki ’yan bindigar.

Yayin gudanar da bincike, Baba, ya amsa cewa yana daga cikin waɗanda suka aikata laifin, inda ya bayyana cewa Naira 6,000 aka ba shi a matsayin rabonsa.

Ya kuma bayyana sunayen wasu daga cikin abokan aikinsa.

Wasu daga cikinsu sun muty a hannun jami’an tsaro a yayin wasu samame da aka kai, kamar su Bello Kici-Kici daga Doguwa da Mallam Sale daga Gezawa.

Wani kuma mai suna Ruwa Shehu daga Bebeji, yana gidan yari bayan samun sa da laifin satar mutane.

Sauran da suka haɗa da Ibrahim Gwanja da Sule Naye har yanzu ana ƙoƙarin gano inda suka shiga.

’Yan sanda sun ce za a gurfanar da Baba a kotu bayan an kammala bincike.

Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Kano, CP Ibrahim Adamu Bakori, ya yaba wa rundunar da ke yaƙi da garkuwa da mutane, bisa jajircewarsu, tare da gode wa jama’a kan goyon bayan suke bai wa jami’an tsaro.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Yan Sanda

এছাড়াও পড়ুন:

’Yan sanda sun gano harsasai 210 a kan titin Zariya-Funtuwa

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kaduna, ta gano harsasai 210 da aka jefar a kan babbar hanyar Zariya zuwa Funtuwa, a unguwar Dogo Itace da ke Samaru, Zariya.

Lamarin ya faru ne lokacin da DPO na Samaru tare da tawagarsa suke sintiri a kan hanyar.

Allah Ya yi wa Sheikh Dahiru Bauchi rasuwa Juyin mulki ya rutsa da Jonathan a Guinea-Bissau

Jama’ar yankin ne suka kira rundunar cewar fasinjojin wata mota ƙirar Volkswagen Golf mai launin baƙi sun jefar da wata jaka, sannan suka tsere.

Da jami’an rundunar suka isa, sun tarar da jakar da aka jefar.

Bayan gudanar da bincike, sun gano harsasai 210 na ɗangon 7.56mm.

DPO ɗin yankin ya sanar da sauran jami’an rundunar da ke kan hanyar Funtuwa domin dakatar da motar amma ba a ga motar ba.

Ana zargin direban da fasinjojin motar sun lura da jami’an tsaron da ke kan hanyar, wanda hakan ya sa suka zubar da jakar.

Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Kaduna, CP Rabiu Muhammad, ya yi kira ga jama’a da ci gaba da bai wa rundunar sahihan bayanai.

Ya jaddada ƙudirin rundunar na ci gaba da sintiri da kare rayuka da dukiyoyin al’umma a faɗin jihar.

Ya kuma gargaɗi masu aikata laifi da su guji duk wani yunƙurin tayar da zaune-tsaye, inda ya ce duk wanda aka kama zai fuskanci hukunci mai tsanani.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • An janye ’yan sanda 11,566 daga gadin manyan mutane a faɗin Nijeriya
  • ’Yan sanda sun gano harsasai 210 a kan titin Zariya-Funtuwa
  • ’Yan sanda sun kama masu laifi 34 a Kaduna
  • ’Yan sanda sun kama masu laifi da 34 a Kaduna
  • Ko sisi ba a biya ’yan bindiga ba kafin su saki ɗaliban da suka sace – Gwamnan Kebbi
  • ’Yan bindiga sun sake kai hari a Kwara, sun sace mutum 11
  • An sako ɗalibai 25 da ’yan bindiga suka sace a Kebbi
  • An buɗe wasu makarantu domin ci gaba da jarawaba a Katsina
  • ’Yan bindiga sun sace mutum 8 a Kano
  • Amarya ta yi wa angonta yankan rago bayan kwana 3 da aurensu a Katsina