Aminiya:
2025-11-27@21:14:35 GMT

Wata mata ta banka wa kanta wuta a Bauchi

Published: 4th, October 2025 GMT

Wata mata ta zuba wa kanta man fetur sannan ta banka wa kanta wuta a Jihar Bauchi.

Matar wadda mai matsakaicin shekaru ce, ta yi wannan aika-aika ne a ƙofar gidan tsohon Fira Ministan Najeriya, Marigayi Sa Abubakar Tafawa Ɓalewa.

Shaidu sun ce bayan saukar matar daga wani babur mai kafa uku, riƙe da galan ɗin man fetur a hannunta, ta nemi ganin Yelwa Abubakar, ’yar Marigayi Tafawa Ɓalewa, wadda ita ce Shugabar Hukumar Kula da Yara Masu Rauni da Marayu ta Jihar Bauchi (BASOVCA).

Amma da aka shaida mata cewa Hajiya Yelwa ba ta nan, sai matar ta zuba wa kanta fetur ɗin ta kuma kiyasta wa kanta ashana a babbar ƙofar shiga gidan.

Duk ƙoƙarin mutanen da ke wurin na kashe wutar ya gagara, sai daga baya aka garzaya da ita zuwa Asibitin Koyarwa na Jami’ar Abubakar Tafawa Ɓalewa (ATBUTH), inda daga bisani ta mutu a sakamakon munanan raunukan da ta samu daga ƙunar.

Shaidu sun bayyana cewa akwai alamar taɓin hankali a tare da matar.

Kakakin ’yan sandan jihar, Mohammed Ahmed Wakil, ya tabbatar da faruwar lamarin, ya mai bayyana takaici bisa haka.

Ya ce kwamishinan rundunar, Sani-Omolori Aliyu, ya ba da umarnin gudanar da bincike don gano ainihin abin da ya faru a ranar Juma’a 26 ga watan Satumba, 2026 ta gabata.

Ya bayyana cewa an yi nasarar yi wa matar tambayoyi a gadon asibiti, amma ta yi iƙirarin cewa ba ta san cewa fetur ne a cikin jarkar da ke hannunta ba, da kuma dage cewa ta ɗauka ruwa ne.

Wakil ya ce bayan zurfafa bincike an gano cewa matar tana da tarihin taɓin hankali, wanda maƙwabta suka ce matsalar ta ƙaru bayan ta  haifu autanta.

Ya ce tuna aka mika gawar ga iyalan mamaciyar domin yi mata jana’iza.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Tafawa Ɓalewa

এছাড়াও পড়ুন:

Amarya ta yi wa angonta yankan rago bayan kwana 3 da aurensu a Katsina

Ana zargin wata amarya da yi wa angonta yankan rago kwana uku bayan ɗaurin aurensu a Jihar Katsina.

Angon mai suna Abubakar Abdulkarim da aka fi sani da Dan Gaske, ana zargin ya rasa ransa bayan da amaryar ta yi amfani da wuƙa wajen halaka shi.

Shaidu sun ce ta yi masa mummunan rauni a wuya wanda ya yi sanadiyyar mutuwarsa.

Angon da amaryarsa suka daura aure ne a ranar Alhamis, 18 ga Nuwamba, 2025, amma farin cikin aure ya rikide zuwa makoki a ranar Lahadi da rana lokacin da lamarin ya faru.

Gobarar tankar mai ta ƙone gidaje a Jihar Neja NAJERIYA A YAU: Irin Radadin Da Masu Cutar Amosanin Jini Ke Fuskanta

Wani ɗan uwansa mai suna Aminu Danladi ya ce cewa sun yi taro da marigayin da safiyar ranar, suna shirya ziyarar ’yan uwansu da za a kai da yamma.

Ya ce daga baya ango ya koma gida domin shiri, sai kuma aka ji labarin an same shi kwance a cikin jini babu rai.

Aminu ya kuma ƙaryata jita-jitar da ake yaɗawa cewa auren dole ne aka yi wa ma’auratan, inda ya tabbatar da cewa dangantakarsu ta kasance lafiya kafin aure.

Majiyoyi sun ce matar, ’yar asalin Katsina, ta taɓa yin aure a baya, abin da ake zargin dangin mijin ba su sani ba.

An ce bayan faruwar lamarin amaryar ta ruɗe inda ta je gidan maƙwabta tana neman abinci. Wannan hali ya sa tsofaffin mata zargin akwai matsala, suka bi ta gida inda suka tarar da gawar mijin, suka kuma sanar da jami’an tsaro.

Rundunar ’Yan Sanda ta tabbatar da faruwar lamarin, inda ta ce ta fara gudanar da bincike a kai.

Kakakin ’yan sanda na jihar, DSP Abubakar Sadiq Aliyu, ya ce an kama mutum ɗaya da ake zargi da hannu a lamarin, kuma bincike na ci gaba.

Kwamishinan ’Yan Sanda na Katsina, CP Bello Shehu, ya tabbatar da cewa za a gudanar da bincike mai zurfi, tare da kira ga jama’a da su bayar da bayanai masu amfani.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Wata mata ta kashe ’yar shekara 7 a Ribas
  • An janye ’yan sanda 11,566 daga gadin manyan mutane a faɗin Nijeriya
  • An rantsar da sabon shugaban kasa a Guinea-Bissau bayan juyin mulkin sojoji
  • Majalisar Wakilai ta nemi gwamnati ta gaggauta dauko Jonathan daga Guinea Bissau
  • Sheikh Dahiru Bauchi: Malamin da zuri’arsa ta fi kowacce yawan mahaddata Alkur’ani
  • Ma’aikatar Harkokin Wajen Falasdinu Ta Sanar Cewa Akalla Yan Mata 33000 Ne Isra’ila Ta Kashe A Gaza
  • Reuters: Kungiyar Likitoci Ba Da Iyaka Ba Ta Fice Daga Asibitin Darfur Bayan Bude Wa Ma’aikatanta Wuta
  • Kotu ta yanke wa mutum 5 hukuncin rataya a Oyo saboda aikata kisan kai
  • An haramta cin naman Kare da Kyanwa a Indonesia
  • Amarya ta yi wa angonta yankan rago bayan kwana 3 da aurensu a Katsina