Kissoshin Rayuwa: Sirar ImamHassan(a) 143
Published: 4th, October 2025 GMT
143-Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na duniyarmu a yau shiri wanda yake kawo maku kissoshi wadanda suka zo cikin al-kur’ani mai girma ko cikin wasu littafan wadanda suka hada da littafin Dastane Rastan na Aya. Murtadha Mutahhari ko kuma cikin littafin Mathnawa na maulana jalalluddin Rumi ko kuma cikin wasu littafan.
/////… Madalla, masu sauraro idan kuna tare da mu a cikin shirimmu da ya gabata, a kuma cikin sirar Imam Al-Alhassan Almujtaba dan Fatimah (s) diyar manzon All..(s) da muke kawo maku. A cikin shirimmu da ya gabata mun yi Magana dangane da yadda aka gudanar da hukunci tsakanin Abdullahi dan kais da kuma Amru dan Asi.
Da farko Mu’awiya dan Abu Sufyan ne ya Aikawa Imam Ali(a) wasika, ya bukaci a fito zuwa hukuncin da wakilansu biyu zasu yi a daumata jandal. Imam (a) ya amsa kiran kamar yadda yayi alkawali, don haka ya aika mutane 400 zuwa hukuncin, daya daga cikinsu shi ne Abu musa, ku Abdullahi dan kais. Haka ma mu’awiya ya aiki mutane 400 don hakan tare da Amru dan Asi. Kafin su fita ya zauna da Amru suka tattauna yadda zasu fitowa Abu musa, sun tattauna dangane da halayensa da kuma yadda zasu bullo masa.
A lokacinda suka isa wajen hukuncin sai Amru dan Asi ya bar Abu musa har zuwa kwanaki 3 bai yi masa maganar abinda ya kawosu ba. Sai yana nuna masa halaye na girmamawa, yana ce masa, sahabin manzon All..(s), yana nuna masa tawaliliu, amma da alamun Abu musa kuma ya karkata zuwa yabonsa da yake yi.
Banda haka yakan kawo masa abinci mai dadi da kuma abinsha don ya jawo shi a jiki.
Daga nan sai y afara masa maganar cewa, kasancewars babban sahabin manzon All…(a) mai yuwa All..ya yi amfani da shi don kyautata wannan al-ummar al-barkacinsa.
Bayan kwanaki uku, sai y afara fada masa cewa, ni ina ganin abinda ya dace shi ne mu cire Ali da Mu’awiya kan wannan al-amarin sannan mu nemi wani mutum wanda bai da hannu a cikin wannan fitinar, babu jinin wani da ya zubar.
Sai Abu musa ya amince, sannan Amru ya san cewa Abu musa ya karkata zuwa Abdullahi dan Umar a matsayin Khalifa. Sai yace masa ina ganin Abdullahi dan Umar zai dace ko, sai Abu musa yayi farin ciki, sannan ya ce ya amince.
Amma sai ya fara maganar cewa, : Amma ta yaya zan sami tabbacin ba zaka saba mani ba. Ba zaka yaudare ni ba.
Daga nan Amru dan Asi ya ce masa, ai zan rantse maka da All..sai ka yarda. Don haka Amru ya rantse masa da All.. da kuma duk abinda zai iya rantsewa da shi kan cewa ba zai saba masa ba idan sun ke gaban mutane.
Don haka Amru ya rantse, ya rantse, ya ranste a gaban Abu musa har sai da ya ce ya yarda.
Yana yarda sai labari ya fito kan cewa sun sami matsayanda suka gamu a kai. Kuma za’a bayyana lokacin haduwar bayanin abinda suka gamu a kai nan gana kadan.
Don haka a lokacin aka zo wajen bayanin abinda suka tsaya a kai, sai Amru dan Asi ya gabatar da Abu musa y afara yin Magana, ya hau mimbari sai ya zauna. Da farko Abu musa ya ki, amma Amru dan Asi ya matsa, sai shi y afara hawa mimbari.
A lokacinda Abdullahi dan Abbas ya ga haka sai ya masu wajen Abu musa ya ce masa kada ya fara don Amru dan Asi Makiri, yana iya saba masa.
Amma daga karshe sai da ya sa shi ya hau ya kuma fara da yabon All..da salati ga manzon All..(a) sannan ya bayyana cewa, sun tsaida cewa, don maslahar alumma da kuma zaman lafiya a tsakaninsu, sun tsaida cewa, zasu tube Ali(a) da Mu’awiya daga wannan al-amarin, sannan sun nada Abdullahi dan Umar a matsayin Khalifa…shi kaza-kaza ne, ya yabe shi ya sauka.
Amru ya hau kan mimbari, sai y afara da yabon All..da salati ga manzon All..(s). sannan yace ya ku mutane kunji abinda Abu musa ya fara, kan cewa ya Tube Ali daga cikin wannan al-amarin ni ma kamar yadda ya tube Aliyu ni ma na tube shi, kamar yadda na cire rawani na, sannan na nada Mu’awiya dan Abu Sufyan a matsayin shugabana shugabanku. Sannan ya ci gaba da yabon mu’awiya. Yana cewa shima sahabi ne.
Sai Abu Musa ya tashi ya la’ani Amru dan Asi ya ce masa, kare. Sai Amma ya sauka daga mimbari ya zagi Abu musa yana ce masa, jaki dauke da littafai. Da haka kuma aka watse.
Abu musa yak ama hanya ya tafi makka bayan ya tube Aliyu dan Abitalib (a) daga khalifanci, ya dora Abdullahi dan Umar.
Al-amarin ya sa mutanen kasar iraki wadanda suka sabawa Imam Ali (a) a lokacinda ya fada masu cewa, sun daga mushafi don yaudara ne, suka yi ta zargin juna, amma mafi yawansu ma sun zama khawarijawa.
A lokacinda rikicin yadda hukunci ya kara a daumata jandal ya yi zafi a cikin irakawa. Sai imam Ali(a) ya tara mutane ya fadawa dan Imam Al-Hassan yayi masu Magana a kan wadannan mutane biyu Amru da Abu musa.
Daga nan sai Imam Hassan (a) ya hau mimbari ya
{Ya ku mutane! Lallai kun yawaita Magana kan Abdullahi dan Kais da Amr dan Asi, gaskiyan al-amarin an aikasu ne don su yi hukunci da littafin All..sai suka yi hukunci da son zuciya maimakon littafin All.. wanda ya kasance haka, ba za’a kira shi alkali ba, sai wanda yakamata a yi hukunci a kansa.
Abdullahi dan Kais yayi kuskure wajen maida wannan al-amari ga Abdullahi dan Amur. Yayi kura-kurai har guda uku a cikinsa. Da farko babansa (Umar) bai yarda ya zama khalif aba, sannan bai taba Sanya shi shugaba ba, sannan sahabban manzon All..(s) muhajirun da Amsara basu gamu a kan nada shi khalifa ba, wadanda sune suka nada wanda ya zo bayansa. Kuma ku san cewa shugabanci wajibi ne daga All…
Kuma manzon All..(s) ya hukuntar da Sa’ad dan Mu’azu kan yahudawan Banu Quraizah, sai yayi hukunci a kansu da hukuncin All.. babu shakka a cikinsa. Manzon All..(s) ya zartar da hukuncinsa, da ya saba da bai zartar ba. }
Sanna ya sauka.
Hakika Imam Hassan (a) ya ambaci al-amura masu muhimmanci a cikin wannan al-amarin ko fitinar, ya kuma bayyana shi kamar yadda ya dace. Ya kuma bayyana sukkan abinda yakamata a bayyana a takaice, sannan ya tushe duk wata kafa ta masu taraddudi a cikinsa. Ya bayyana cewa alkali shi ne wanda idan yayi hukunci hukuncinsa mai rarrabewa ne ya kuma kauda dukkan son zuciya daga hukuncin.
Sannan ya bayyana cewa khalifantar da dan Umar bai dace ba don mahaifinsa ma baya ganin ya cancanta. Da ya ga ya cancanta, da ya Sanya shi cikin shura. Sannan hakan ya rasa sharadi na asasin, wato amincewar muhajirun da Ansara.
Sannan ya yi shiru bai yi maganar alkalancin kansa ba, saboda Khawarijawa basu amince da it aba.
Bayan Imam Hassan (a) sai Abdullahi dan Abbas ya tashi yayi Magana yana cewa: Ya ku mutane, lalle gaskiya tana da mutane wanda suka yi muwafakar samunta suka yarda da ita.
Sannan mutane kuma, akwai mai amincewa da ita da kuma wadanda ba zasu amince ba. Abin sani Abu musa ya tafiya da ita gaskiya (wato Aliyu (a) a matsayin shugabansa) zuwa bata ( zuwa wanda ya nada da son zuciyarsa Abdullahi dan Umar). …har zuwa karshen maganarsa.)
Bayansa ma Abdullahi dan Jaafaru ya tashi yayi Magana. Hankali ya kwanta, sannan aka fara maganar sake tada wata runduna don kwace sham daga hannun Mu’awiya.
Amma ana cikin wannan halin sai Khawarijawa sun taru a wani wuri da ake kira Nehravan suna ayyukan ta’addanci sun watsa tsoro a cikin kasar. Don haka sai Imam (a) ya ga ba makawa sai ya yake su kafin ya wuce sham.
Watana rana wani sahabin manzo All..(s) wanda ake kira Abdullahi dan Habbab Al-art ya zo yana wucewa ta inda suka kafa sansaninsu. Sai suka tsaida shi tare da matarsa wacce take da ciki wanda ya girma.
Suka ce waye kai , sai yace mutum mumini, sai suka ce: me kake fada dangane da Aliyu dan Abitalib.
Sai yace: Shi ne amirul muminina, kuma na farkon wanda ya musulunta da kuma Imani da All..da manzonsa (s) . sai suka ce : Menene Sunanka, sai yace Abdullahi dan Habbab dan Al-Art sahabin manzon All..(s). . sai suka ce, mun tsoratar da kai? Sai yace : ee, sai suka ce kada ka ji tsoro.
Sai suka ce masa, ka bamu labarin wani hadisi daga babanka wanda ya ji daga manzon All…(a) mai yuwa All..ya amfanar da mu da shi.
Sai ya ce to: babana ya fada mani daga manzon All..(s) yana cewa: Fitina zata kasance bayana, zuciyar mutum zata mutu kamar yadda jikinsa yake mutuwa, ya yi maraice mumini sannan ya wayi gari kafiri.
Sai suka ce : wannan hadisin ne muka tambayeka, Wallahi sai mun kasheka kissan da bamu taba kishe wani da irinsa ba.
Masu sauraro saboda kurewar Lokaci a nan zamu dasa aya sai kuma wata fitowa idan All..ya kaimu.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Kissoshin Rayuwa : Sirar Imam Hassan (a) 142 October 4, 2025 Kissoshin Rayuwa Sirar Imam Hassan (a) 141 October 4, 2025 Araqchi Ya Ce: Bai Kamata Dokar Kasa Da Kasa Ta Zama Abin Wasa A Hannun Amurka Ba October 4, 2025 Guterres Ya Yi Tsokaci Dangane Da Martanin Kungiyar Hamas Kan Yarjejeniyar Zaman Lafiya A Gaza October 4, 2025 Trump Ya Bukaci Gwamnatin Isra’ila Da Ta Daina Kai Hare-Hare Kan Zirin Gaza October 4, 2025 Babban Jami’in Kungiyar Hamas Ya Karyata Batun Mika Fursunonin Isra’ila Cikin Sa’o’i 72 October 4, 2025 Turkiyya Ta Yi Watsi Da Bukatar Shugaban Amurka Kan Daina Sayen Iskar Gas Daga Rasha October 4, 2025 Hamas ta amince da daftarin zaman lafiya na Trump October 4, 2025 Iran ta bukaci duniya ta bijirewa haramtattun takunkuman Amurka October 4, 2025 Duniya na yabawa Hamas kan amincewa da daftarin Trump October 4, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: Abdullahi dan Umar wannan al amarin Amru dan Asi ya a cikin wannan masu sauraro Abu musa ya kamar yadda
এছাড়াও পড়ুন:
’Yan bindiga sun sake kai hari a Kwara, sun sace mutum 11
’Yan bindiga sun yi garkuwa da aƙalla mutum 11 mazauna garin Isapa da ke kusa da Eruku a Ƙaramar Hukumar Ekiti ta Jihar Kwara.
Harin ya faru ne sa’o’i kadan bayan sakin wasu masu ibada da aka yi garkuwa da su suna tsaka da ibada a coci.
An haramta cin naman Kare da Kyanwa a Indonesia An sako ɗalibai 25 da ’yan bindiga suka sace a KebbiA cocin CAC da ke Ekuru, ana gudanar da bikin godiya domin murnar ’yantar da mambobi 18 da aka yi garkuwa da su kusan wata guda da ya gabata, sai ’yan bindiga suka kutsa suka yi garkuwa da mutum 38 bayan sun harbe uku har lahira.
Sabon harin, wanda ya faru da misalin ƙarfe 6:00 na yammacin Litinin, an ce ’yan bindiga kimanin 20 zuwa 30 ne suka kai shi.
Bayanai sun una cewa maharan su rika yin harbi ta ko’ina yayin da suke kutsa cikin garin, lamarin da ya sa mutane suka ranta a na kare.
Wata tsohuwa ta ji rauni sakamakon harbin kan mai uwa da wabi.
Wani jagoran al’umma da bai amince a bayyana sunansa ba, ya tabbatar da lamarin, inda ya ce: “Mutane 11 aka yi garkuwa da su, bakwai daga cikin su ’yan gida ɗaya. Waɗanda aka sace sun haɗa da mace mai juna biyu, masu shayarwa biyu da kuma kananan yara.”
Shaidar y ace sunaye mutanen sun hada da Talatu Kabiru, 20, Magaji, 6, Kande, 5, Hadiza, 10, Mariam, 6, Saima, 5, Habibat (mahaifiya), Fatima Yusufu (mahaifiya), Sarah Sunday, 22 (mai juna biyu), Lami Fidelis, 23 (uwa mai shayarwa) da kuma Haja Na Allah, ita ma uwa mai shayarwa.
Shaidun gani da ido sun ce ’yan bindigar sun bi wasu sassa na garin, inda suka bar alamun ramukan harsashin harbe-harbe a bangon gidaje da ƙofofi.
An gano harsashin bindiga AK-47 da aka harba daga wurare da dama bayan ’yan bindigar sun ja da baya tare da mutanen da suka yi garkuwa da su.
Lamarin ya haifar da tsananin tashin hankali a yankin da makotan garuruwa, yayin da jami’an tsaro da ’yan sa-kai ke ƙara ƙoƙari wajen gano maharan da ceto waɗanda aka sace.
Kwamishinan ’Yan Sanda na Jihar Kwara, Adekimi Ojo, ya tabbatar da lamarin ga yana mai cewa: “Eh, lamarin ya faru, amma ba zan iya cewa komai da yawa ba yanzu ba. Ina gab da shiga Isapa daga Ilorin. Zan ba da rahoto idan na isa.”
A yanzu haka dai Najeriya na fuskantar ɗaya daga cikin mafi munin matsalolin tsaro a tarihin ta. Hakan dai ya haifar da rufe makarantu da dama, musamman a Arewacin ƙasar.