Babban Jami’in Kungiyar Hamas Ya Karyata Batun Mika Fursunonin Isra’ila Cikin Sa’o’i 72
Published: 4th, October 2025 GMT
Babban jami’in kungiyar Hamas ya bayyana cewa: Mika fursunoni da gawarwaki cikin sa’o’i 72 ba gaskiya ba ne a halin da ake ciki yanzu.
Babban jami’in kungiyar Hamas Musa Abu Marzouk ya tabbatar a ranar Juma’a cewa, batun mika fursunoni da gawarwakin yahudawan sahayoniyya cikin sa’o’i 72 lamari ne na nazari, ba tabbas ba, a halin da ake ciki yanzu.
Abu Marzouk ya bayyana cewa: Kungiyar Hamas ta amince da shirin Amurka da aka gabatar “a bisa ka’ida,” yana mai cewa “aiwatar da shi yana bukatar tattaunawa.” Ya kuma lura da cewa dukkan bayanai da suka shafi rundunar wanzar da zaman lafiya “yana bukatar fahimtar juna da fayyace shi dalla-dalla.”
Dangane da batun makamai kuwa, Abu Marzouk ya bayyana a wata hira da ya yi da tashar talabijin ta Aljazeera cewa: Kungiyar Hamas za ta mika makamai ga gwamnatin Falasdinu da za a kafa nan gaba, yana mai jaddada cewa duk wanda ke mulkin Gaza zai mallaki makamai. Ya kara da cewa kungiyar za ta shiga tattaunawa kan dukkan batutuwan da suka shafi batun kungiyar da kuma makamai.
Babban jami’in na Hamas ya bayyana cewa: Kungiyar “ta amince da wani ra’ayi na yanki da kasa da kasa da Masar ta gabatar,” tare da lura da cewa wannan hangen nesa “ya hada da amsoshi game da zaman lafiya da kuma al’amuran nan gaba.”
Kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hamas ta sanar a yammacin jiya Juma’a cewa ta mika martaninta ga shirin shugaban Amurka Donald Trump na dakatar da yakin zirin Gaza ga masu shiga tsakani.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Turkiyya Ta Yi Watsi Da Bukatar Shugaban Amurka Kan Daina Sayen Iskar Gas Daga Rasha October 4, 2025 Hamas ta amince da daftarin zaman lafiya na Trump October 4, 2025 Iran ta bukaci duniya ta bijirewa haramtattun takunkuman Amurka October 4, 2025 Duniya na yabawa Hamas kan amincewa da daftarin Trump October 4, 2025 Gaza : Ana ci gaba da tir da Isra’ila kan kai farmaki akan jiragen ruwan agaji October 4, 2025 Madagaska : Shugaba Rajaolina ya ce ‘’ana zanga-zanga ne da nufin tsige shi “ October 4, 2025 Washington Ta Bada Dalar Amurka Miliyon 230 Don Kwace Damarar Hizbullah October 3, 2025 Mutane 5 Sun Mutu Bayan Hari Kan Wurin Bautar Yahudawa A London October 3, 2025 Iran: Larijani Ya Yi Tir Da Kasashen Yamma A Kokarin Tursasawa Iran October 3, 2025 Kungiyoyin Kare Hakkin Bil’adam Sun Nuna Damuwarsu Da Halin Wadanda HKI Ta Tsare October 3, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: Kungiyar Hamas kungiyar Hamas
এছাড়াও পড়ুন:
Ammar Hakim Ya Gargadi Kasashen Yamma Da su Kiyayi Tsoma Baki A Harkokin Cikin Gidan Kasar.
Rahotannu sun bayyana cewa sayyid Ammar Hakim shugaban kungiyar wisdom movement na kasar Iraqi ya kaddama da yakin neman zabe inda yayi kira da hadin kai tsakanin alummar kasar kuma ya gargadi kasashe waje da su guji tsoma baka a cikin alamuran kasar.
Wadannan bayanai suna zuwa ne adaidai lokacin da kasar Amurka take matsin lamb akan kasar Iraqi na ta rusa kungiyar Hashdu shaabi, musamman bayan abubuwa da suka faru a kasashen siriya da kuma kasar Labanon.
An kafa kungiary ta Hshadushaabi ne karkashin umarnin babban malamin Addini na kasar Ayatullah Sisitani domin tunkarar kungiyar ta’adda ta da’aesh
Daga karshe Hakim ya jaddada cewa alummar iraki ne kawai suke da hakkin yanke hukumci ba tare da ingizasu ba, duk da matsain lambar da take fuskanta daga kasashen waje. Yace muna son iraki madaidaiciya mai mututunta akidar alummar da suka fi rinjaye, saboda iraki ta kowa ce, babu wani mutum ko gunguni jama’a da zai yi abu shi daya.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Sarkin Morocco Ya yi Magana Tun Bayan Barkewar Zanga-zanga A Kasar . October 11, 2025 Wani Dan Majalisar Dokokin Kasar Iran Ya Ja Kunnen Amurka Kan Taba Jiragen Dakon Man Kasa October 11, 2025 Bayan Yakin Kwanaki 12, Kifar Da Gwamnatin JMI Ya Fita Daga Zabin Makiya: Aref October 11, 2025 Iran Ta Bukaci HKI Ta Aiwatar Da Yarjeniya Da Gaza Kamar Yadda Take October 11, 2025 HKI Ta Kashe Mutane 19 A Gaza Duk Tare Da Tsagaita Wuta October 11, 2025 Iran Tana Goyon Bayan Duk Wani Shirin Zaman Lafiya Da Ya Hada Da Kawo Karshen Kisan Kiyashi A Gaza October 11, 2025 Faransa Da Jamus Da Kuma Birtaniya Sun Bayyana Aniyarsu Ta Ganin An Farfado Da Tattauna Da Iran October 11, 2025 Kungiyoyin Falasdinawa Sun Fitar Da Sanarwar Hadin Gwiwa Kan Tsagaita Bude Wuta A Gaza October 11, 2025 Venezuala Ta Bukaci Kwamitin Sulhun M.D.D Da Ya Tabbatar Da Cewa: Amurka Tana Barazana Ga Zaman Lafiya October 11, 2025 Pakistan Ta Kai Hari Kan Kasar Afganistan, Inda Ake Rade-Radin Kashe Shugaban Taliban Na Kasarta October 11, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci