Isra’ila ta kai hare-hare a Gaza duk da kiran Trump na tsagaita wuta
Published: 4th, October 2025 GMT
Hukumar kashe gobara ta yankin Gaza ta ce a ranar Asabar, sojojin Isra’ila sun kai hare-hare da dama a birnin Gaza duk da kiran da Shugaban Amurka Donald Trump ya yi na a dakatar da luguden wuta bayan ƙungiyar Hamas ta amince da yarjejeniyar tsagaita wuta.
A ranar Asabar din nan da karfe 6 na yamma wa’adin da Trump ya bayar na cimma yarjejeniyar zaman lafiyar take cika.
“Dare ne mai tsanani ƙwarai, inda sojojin Isra’ila suka kai hare-haren sama da harbin manyan bindigogi da dama a birnin Gaza da wasu yankuna na zirin, duk da kiran Shugaba Trump na a dakatar da luguden bama-bamai,” in ji kakakin hukumar kashe gobara ta Gaza, Mahmud Bassal, yayin tattaunawa da kamfanin Dillancin Labarai na AFP.
Bassal, wanda ke jagorantar ƙungiyar agaji da ke ƙarƙashin ikon Hamas, ya ce gidaje 20 ne suka rushe sakamakon hare-haren da aka kai cikin dare.
’Yan bindiga sun ƙaƙaba wa ƙauyuka harajin N10m a Neja Wata mata ta banka wa kanta wuta a Bauchi“Yanayin ya yi tsanani ƙwarai a birnin Gaza,” in ji shi, yana mai ƙarawa da cewa ƙungiyarsu ba ta iya isa ga dukkan mutanen da abin ya shafa ba saboda “tankoki da kuma ci gaba da luguden wuta.”
Da AFP ta tuntuɓi rundunar sojin Isra’ila, ta ce tana “bincike” rahotannin hare-haren da aka kai cikin dare a Gaza.
Shirin zaman lafiya da Shugaba Trump ya gabatar a wannan makon, tare da goyon bayan Fira Ministan Isra’ila Benjamin Netanyahu, ya ƙunshi tsagaita wuta, sakin fursunonin da ake rike da su cikin sa’o’i 72, ajiye makaman Hamas da kuma janye sojojin Isra’ila a hankali daga Gaza.
Hamas ta bayyana a ranar Juma’a cewa tana shirye ta saki fursunonin da ke hannunta bisa shirin Trump, amma ta nemi a tattauna cikakkun bayanai tare da samun damar ba da gudummawa a tattaunawar kan makomar yankin Falasɗinu.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Isra ila Zaman lafiya
এছাড়াও পড়ুন:
Reuters: Kungiyar Likitoci Ba Da Iyaka Ba Ta Fice Daga Asibitin Darfur Bayan Bude Wa Ma’aikatanta Wuta
Kungiyar ta kasa da kasa mai gudanar da a ayyukan agaji, ta sanar da janye ma’aikatanta daga asibitin Darfur, bayan da aka bude musu wuta, ya kuma kai ga kashe daya daga cikin masu aikin agaji.
Kungiyar ta yi kira ga rundunar kai daukin gaggawa RSF da ta tabbatar da tsaro da kuma kiyaye lafiyar ma’aikatan agaji.
Bugu da kari kungiyar ta ce mutumin da aka kashe a ranar 18 ga watan nan na Nuwamba ma’aikaci ne a ma’aikatar kiwon lafiya ta Sudan.
Asibitin Zalnagi yana a jihar Darfur ta tsakiya ne da a halin yanzu ke karkashin ikon rundunar “RSF.
A nata gefen, jami’a mai kula da tafiyar da ayyukan kungiyar ta “ Likitoci Ba Tare Da Iyaka Ba.” Maryam Li Arusi ta ce, babu yadda za a yi ma’aikatansu su ci gaba da gudanar da ayyukansu na jin kai a halin da ake ciki, har sai idan RSF ta bayar da tabbaci da lamunin bayar da kariya ga ma’aikatan da kuma marasa lafiya.
A daya gefen,rundunar RSF ta kore cewa tana cutar da fararen hula, tana mai jaddada cewa duk wanda aka same shi da aikata laifi to za a hukunta shi.
Tun bayan da yankin Darfur ya shiga karkashin ikon rundunar RSF ne ake fito da bayanai akan yadda mayakanta su ka aikata laifukan yaki da cin zarafin mutanen yankin.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Shugaban Iran: Kasuwar jarin cikin gida sirrin nasarorin gwamnati na tattalin arziki November 26, 2025 Larijani: Hadin gwiwar Iran da Pakistan na taimaka wa zaman lafiya a yankin November 26, 2025 Al-Houthi ya yi ta’aziyyar shahadar babban kwamanda na Hizbullah November 26, 2025 UNIFIL: Isra’ila tana sabawa wa kudurorin MDD a cikin Lebanon November 26, 2025 Matsalolin Tsaro A Yankunan Bakin Ruwa A Kasar Siriya Ya Kai Ga Zanga-Zangar Lumana November 26, 2025 Aljeriya Ta Bukaci Kasashen Duniya Su Dauki Mataki Don Kawo Karshen Ta’asan HKI A Yankin Asiya Ta Kudu November 26, 2025 Shugaban Majalisar Koli Ta Taron Kasa Iran Ya Yabawa Pakistan Saboda Goyon Bayanta November 26, 2025 EU da AU na taro kan diyya ga laifukan mulkin mallaka da cinikin bayi November 25, 2025 Hizbullah: Isra’ila na kure idan ta na tunanin kashe-kashe zai kawo karshen kungiyarmu November 25, 2025 Tashar Press TV ta kaddamar da sashen harshen Hebrew November 25, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci