Shugaban Majalisar Shawarar Musulunci ta Iran ya jaddada cewa; Ba dole ba ne Iran ta bi hukunce-hukuncen da ba bisa ka’ida ba

Shugaban Majalisar Dokokin kasar Iran Mohammad Baqir Qalibaf ya tabbatar a cikin jawabinsa yayin zaman majalisar a yau Lahadi cewa: Iran ba ta daukar kanta a matsayin wajibcin aiwatar da kudurorin kwamitin sulhun Majalisar Dinkin Duniya da aka bayyana a matsayin haramtacciyar hanya sakamakon daukar matakin sake dawo da takunkuman da kasashen Turai uku suka yi kan Iran.

Qalibaf ya yi bayanin cewa: Share fagen hanyar da za a bi wajen sake kakaba takunkuman da kasashen Turai uku suka yi da kuma mayar da takunkuman da Majalisar Dinkin Duniya ta kakabawa Iran, ba bisa ka’ida ba ne, yana mai jaddada cewa, a hukumance kasashen Rasha da China sun fayyace cewa wadannan kudurorin ba su tilasta wa wata kasa aiwatar da su ba.

Ya kara da cewa Iran a nata bangaren, “ba ta daukar kanta cewa wajibi ne” ta dakatar da sarrafa sinadarin Uranium ko kuma ta mutunta duk wani daga cikin wadannan kudurori, yana mai jaddada cewa, hakkin Iran na ci gaba da kasancewa a karkashin dokokin kasa da kasa.

Qalibaf ya bayyana cewa takunkumin da aka tanadar a cikin wadannan kudurorin ba su da tasiri sosai fiye da takunkuman Amurka, kuma aiwatar da su a matakin Majalisar Dinkin Duniya na fuskantar cikas mai tsanani na shari’a. Sai dai kuma ya yi gargadin a lokaci guda cewa: Idan har kowace kasa ta aiwatar da wadannan kudurori da suka saba wa doka kan Iran, to za ta fuskanci martani mai tsanani kuma kai tsaye, sannan kasashen Turai uku za su ga matakin da Iran ta dauka a fili.

Share

0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Kissoshin Rayuwa: Sirar Imam Hassan (a) 149 September 28, 2025 Takunkuman MDD kan Iran sun fara aiki September 28, 2025 Kissoshin Rayuwa: Sirar Imam Hassan (A) 148 September 28, 2025 Nijar ta yi Tir da kasashen ketare kan tada zaune tsaye a Sahel September 28, 2025 Italiya : Mutane da dama sun jikkata yayin arangama da masu zanga-zangar goyon bayan Falasdinu  September 28, 2025 Isra’ila ta kashe Falasdinawa kusan 100 a hare-haren da ta kai a Gaza September 28, 2025 Pezeshkian: Iran za ta dauki matakan da suka dace domin shawo kan takunkumi September 28, 2025 Afirka ta Kudu da Sin sun kara habaka huldar tattalin arziki don tukarar harajin Amurka September 28, 2025 Sheikh Qassem: Ba za mu mika makamin gwagwarmaya ba September 28, 2025 Iran: Kisan Nasrallah ya saba wa kundin tsarin mulkin MDD September 28, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci About Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS News Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Explore Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS

উৎস: HausaTv

এছাড়াও পড়ুন:

Tinubu ya aike wa Majalisar Dattawa sunayen jakadu

Shugaba Bola Tinubu ya aike da sunan mutum uku zuwa Majalisar Dattawa, domin tantance su a matsayin sabbin jakadan Najeriya.

Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio ne, ya sanar da haka a zaman majalisar na ranar Laraba.

Sojoji sun yi juyin mulki a Guinea-Bissau Jami’an tsaro sun ƙaddamar da shirin murƙushe ’yan bindiga a Kaduna

Waɗanda aka zaɓa su haɗa da Kayode Are daga Jihar Ogun, Aminu Dalhatu daga Jihar Jigawa da kuma Ayodele Oke.

Bayan karanta takardar Tinubu, Akpabio ya ce, “Sunaye uku ne zuwa yanzu, tabbas sauran za su biyo baya.”

Tun bayan ɗarewarsa kan mulki a 2023, Tinubu bai naɗa jakadu ba har yanzu.

Mutane da dama sun daɗe suna ƙorafin kan jinkirin naɗa jakadun.

Amma wasu na ganin aike sunayen jakadun na da alaƙa da barazanar da shugaban Amurka, Donald Trump, ya yi na ɗaukar matakin soji a kan Najeriya, kan zargin yi wa Kiristoci kisan ƙare dangi.

A wata hira da aka yi da shi a watan Satumba, Ministan Harkokin Waje, Ambasada Yusuf Tuggar, ya ce babu wata matsala game da jinkirin.

Ya ce, “Dukkanin ofisoshin jakadancinmu suna aiki yadda ya kamata. Kowace ofishi yana gudanar da ayyukansa yadda ya dace. Rashin jakadu ba zai haifar da giɓi ba.”

Ya ƙara da cewa duk da cewa jakada shi ne shugaban ofishin jakadanci, akwai kwamishinoni, wakilai da ma’aikatan diflomasiyya da ke tafiyar da harkokin yau da kullum.

A cewarsa, “Diflomasiyya ba aikin mutum ɗaya ba ne. Tsarin ya tanadi irin wannan yanayi.”

Tuggar, ya kuma ce shugaban ƙasa ne kaɗai ke da ikon naɗa jakadu, kuma zai yi hakan a lokacin da ya dace.

Ya bayyana cewa, “Shugaban ƙasa yana duba batun, kuma za a sanar da sunayen a lokacin da ya dace.”

Ya ƙara da cewa, “’Yan Najeriya a ƙasashen waje har yanzu suna samun ayyuka, kuma mu’amala da ƙasashen da muke hulɗa da su ba ta ragu ba.”

Ya ce kuma akwai ƙasashe da dama da suka shafe dogon lokaci ba tare da jakadu ba, amma hakan bai lalata dangantakarsu da wasu ƙasashe ba.

Ya ce, “Wannan ba sabon abu ba ne. Diflomasiyya tana da tanadin irin wannan yanayi. Abin da ya fi muhimmanci shi ne aiki, ba kwaikwayo ba.”

A ƙarshe ya ce Najeriya tana aiki kafaɗa da kafaɗa da sauran ƙasashen duniya.

“Manufofin ƙasashen waje na Najeriya sun bayyana, kuma ana jinmu a duniya. Abin da muke yi shi ne tabbatar da cewa ofisoshinmu suna samar da sakamako mai amfani ga ’yan Najeriya.”

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Gwamnan Bauchi ya yi ta’aziyyar rasuwar Sheikh Dahiru Bauchi
  • An Zabi JMI A Cikin Majalisar Zartarwan Ta Hukumar Yaki Da Makaman Guba Ta Duniya CWC
  • Ma’aikatar Harkokin Wajen Falasdinu Ta Sanar Cewa Akalla Yan Mata 33000 Ne Isra’ila Ta Kashe A Gaza
  • Larijani Iran Tana Maraba Da Tattaunawa Ta Gaskiya Amma Ba Tsararren Sakamako Ba
  • Tinubu ya aike wa Majalisar Dattawa sunayen jakadu
  • Shugaban Iran: Kasuwar jarin cikin gida sirrin nasarorin gwamnati na tattalin arziki
  • Shugaban Majalisar Koli Ta Taron Kasa Iran Ya Yabawa Pakistan Saboda Goyon Bayanta
  • Shugaban Majalisar Koli Ta Taron Kasa Iran Ya Yawaba Pakistan Saboda Goyon Bayanta
  • Tashar Talabijin ta Press TV ta kaddamar da sashen harshen Hebrew
  • Velayati: Alakar Iran da Iraki tana da karfi