‘Yan fashi sun sace mutum 17 a mahadar tekun Akwa Ibom da Kuro Riba
Published: 28th, September 2025 GMT
Wasu mutane da ake kyautata zaton ‘yan fashin teku ne sun yi awon gaba mutum 17 a wani kwale-kwale da ke kan iyakar teku a jihohin Akwa Ibom da Kuros Riba.
Lamarin ya faru ne a lokacin da fasinjojin suka taso daga wani ƙauye a kan iyakar jihohin biyu, inda ‘yan fashin suka afka wa kwale-kwalen a cikin nasu jirgin ruwa, sannan suka yi awon gaba da fasinjoji 17.
Kwale-kwalen na wani kamfani ne da ke aikin jigilar fasinjoji tsakanin jihohin biyu a kan teku.
A ‘yan shekarun baya matsalar satar mutane da garkuwa da su ta yi ƙamari a yankin, amma daga baya ta lafa.
Sai dai alamu na nuna cewa lamarin yana neman sake dawowa a kudancin ƙasar, haɗi da matsalar safarar yara zuwa ƙasashen waje domin kai su aikatau.
Rundunar ’yan sandan Kuros Riba ta tabbatar wa Aminiya faruwar lamarin ta hannun mataimakin mai magana da yawunta, DSP Igri Ewa.
A cewar DSP Ewa, “Gaskiya ne lamarin ya faru ranar Alhamis, amma jami’anmu na iya bakin ƙoƙari wajen bincike domin gano wadanda aikata wannan laifi da kuma inda aka ɓoye mutanen.”
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: yan fashi Akwa Ibom
এছাড়াও পড়ুন:
Sojoji Sun Kashe Ƴan Ta’adda 9, Sun Ƙwato Naira Miliyan 5 A Borno
Uba ya ce dakarun sun ci gaba da bincike da fatattakar ƴan ta’addan don hana su sake samun damar motsi a yankin Arewa maso Gabas.
ShareTweetSendShare MASU ALAKA