Jami’an Tsaro Sun Ceto Fasinjoji 8 Da Aka Sace A Kogi
Published: 28th, September 2025 GMT
Jami’an tsaro a Jihar Kogi sun ceto mutane takwas daga cikin fasinjojin da aka yi garkuwa da su har 12 a hanyar Okene–Auchi.
Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ƴansanda ta jihar, William Aya, ya tabbatar da faruwar lamarin a Lokoja ranar Asabar. Ya bayyana cewa fasinjojin suna tafiya ne a cikin motar haya ta Big Joe mai lambar Edo FUG 13 XY daga Abuja zuwa Benin, da Jihar Edo, kafin ƴan bindiga su tare su a hanya.
Aya ya ce rahoton sace Fasinjoji yana shigowa, DPO na Okene, Nasir Muhammad, tare da haɗin gwuiwar Sojoji da ƙungiyar sa-kai, suka ƙaddamar da sintiri wanda ya kai ga kuɓutar da mutane takwas ciki har da direban motar.
Ya ƙara da cewa ana cigaba da ƙoƙarin ceto sauran mutane huɗun da ke hannun masu garkuwa da su, tare da tabbatar da cewa za a kamo waɗanda suka aikata wannan ta’asa domin fuskantar hukunci.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppকীওয়ার্ড: Gwamnatin Kogi
এছাড়াও পড়ুন:
Tinubu ya ayyana dokar ta-ɓaci kan matsalar tsaro
Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ayyana dokar ta-ɓaci kan matsalar tsaro da ta addabi dukkan sassa a Nijeriya.
Cikin wata sanarwa da ya fitar a yammacin wannan Larabar mai ɗauke da sa hannunsa, Tinubu ya bayyana cewa dole ne a ɗauki matakan gaggawa da suka dace domin fuskantar barazanar tsaro da ke ƙaruwa ƙasar nan.
Shugaban ya bayar da umarnin ɗaukar ƙarin jami’an tsaro da suka haɗa da jami’an ’yan sanda 20,000, lamarin da zai ƙara adadin jami’an da za a ɗauka zuwa 50,000, bayan umarnin da ya bayar a ranar Lahadi na ɗaukar jami’an tsaro 30,000.
Real Madrid za ta yi karon-batta da Olympiacos a Gasar Zakarun Turai Tinubu ya aike wa Majalisar Dattawa sunayen jakaduHaka kuma, Tinubu ya bai wa rundunar sojin ƙasa da sauran hukumomin tsaro umarnin ɗaukar ƙarin jami’ai.
Sanarwar ta ce za a yi amfani da sansanonin masu yi wa ƙasa hidima NYSC a matsayin wuraren horas da sabbin ’yan sandan.
Kazalika, shugaban ya bai wa hukumar ’yan sandan farin kaya ta DSS umarnin ɗaukar ƙarin jami’ai a rundunar kare dazuka wato Dakarun Gandun Daji ta Forest Guard.
Shugaba Tinubu ya kuma umarci DSS ta aika dakarun Forest Guard “domin zaƙulo ’yan ta’adda da ’yan fashi daga dazuka.”
“Babu wani sauran gidan ɓuya ga miyagu,” in ji shi kamar yadda wata sanarwa daga fadar shugaban ta bayyana.
Sanarwar ta ƙara da cewar, za a sake horar da jami’an ’yan sanda da aka janye daga gadin fitattun mutane kafin mayar da su aikin ɗan sandan gada-gadan.
Shugaban ya yi amfani da damar wajen jinjinawa hukumomin tsaro wajen kuɓutar da mutane 34 da aka sace a Mujami’ar Kwara da ɗalibai 24 da aka sace a makarantar jihar Kebbi, yayin da ya ce suna ɗaukar matakan da suka dace wajen kuɓutar da ɗaliban makarantar mabiya ɗarikar Katolika da ke Jihar Neja.
Tinubu ya jinjinawa rundunar sojin ƙasar a kan gudumawar da jami’anta ke bayarwa da kuma gabatar da ta’aziyar rasuwar Janar Musa Uba da ƴanta’adda suka yiwa kisan gilla, yayin da ya buƙace su da su ƙara ƙaimi wajen tabbatar da tsaro a yankunan da ake fama da tashin hankali.
Shugaban ya buƙaci majalisar ƙasa da ta sake fasalin dokokin tsaro domin bai wa jihohi damar samar da ’yan sanda na kashin kan su, yayin da ya ce gwamnatin tarayya za ta taimaka musu.
Tinubu ya kuma buƙaci Masallatai da Majami’u da su dinga neman taimakon jami’an tsaro a duk lokacin da za su gudanar da taron ibadun su, musamman a yankunan da ake fama da matsalar tsaro.
Shugaban ya kuma jajanta wa gwamnatoci da kuma mutanen jihohin Kebbi da Borno da Zamfara da Neja da Yobe da kuma Kwara saboda kisan gillar da ƴan ta’adda suka yiwa mutanen su.