Kissoshin Rayuwa: Sirar Imam Hassan (a)
Published: 28th, September 2025 GMT
149-Assakamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na kissoshin rayuwa shiri wanda yake kawo maku kissoshi wadanda suka zo cikin Al-Kur’ani mai girma ko cikin wasu littafan wadanda suka hada da littafin Dastane Rastan na Aya. Shahid Murtadha Muttahari, ko kuma cikin littafin mathnawi na maulana jalaluddeen romi, ko kuma cikin wasu littafan, da fatan masu sauraro zasu kasance tare da mu a cikin wannan Shirin.
////…Madallah, masu sauraro idan kuna tare da mu a cikin shirimmu da ya gabata, a kuma cikin sirar Imam Hassan Al-mujtaba (a) dan Fatimah (s) diyar manzon All..(s) da muke kawo maku, a cikin shirimmu da ya gabata mun ji yadda al-amura suke kara dagulewa a cikin daular musulunci karkashin shugabancin Amirulmuminina (a), tun bayan yakin siffin bayan da sojojinsa suka saba masa, suna kuma daina yaki saboda bangaren Mu’awiya ya daga nushafi yana son wai ya shiga tsakaninsu.
Daga nan sai Khawarijawa sun fito daga cikinsu. Suka bullo da sabon Akida wacce a cikinta suke kafarta musulmi daga ciki har da shi Amirul muminina (a). Ammam wani abun mamaki shi wadan nan khawarajiwa suna kafirta musulmin da suke karshen daular musulunci ne kawai, su kuma yakesu, amma ba zata taba jin sun yaki mutanen Mu’awiya ba. Wanda yake Sanya shakku kan cewa sun sani ko basu sani ba suna atimakawa Mu’awiya dan Abu Sufyan a kan Imam Ali(a) ne.
Don haka da farko ya yayiku a Nehravan, ya kashe mutum kimani 4000 daga cikinsu. Sannan suka sake bullowa tare da jagoranshin Khurait dan Rashid nan ma ya tura makama suka kara da su, a lokacinda Khurait ya cewa an fi karfinsa sai ya sulale da sojojinsa cikin dare suka koma bangaren Basra.
Daga nan sai Imam (a) ya sake turawa wata runduna wacce ta fi ta farkon karfi, ta bi sawunsu, har suka riskesu a yankin na Basra, sannan suka fatata. A karo na biyu Khurait ya sake solalewa ya tsere ya shiga lardin Ahwaz, Rundunar ta bisu sai da ta riskesu suka fafata har, a wannan karon suka kashe shi Khuraita, suka kama wasu mabiyansa da ransu. Wanda ya dawo cikin musulunci su sallame shi wanda kima ya ki ya dawo sai akidar Khawarijanci sai su ci gaba da rike shi.
Khawarijawa, sun sa kiristoci da dama da suka musulunta suka yi ridda sannan sun hana sauran kiristocin biyan jiziya, sannan musulmi kuma sun hanasu biyan zakka ga gwamnatin Imam Ali (a).
A dayan bangaren kuma Mu’awiya dan Abu Sufyan ya ci gaba da mamayar kasashen da suke karkashin Ikon Amirul muminin (a). Ya zuwa shekara ta 38 na hijira sun kwace iko da Masar, da Makka da Madina da yamen da Hamedan suka kama matan wasu wurare a yankin a matsayin fursinonin yaki. Bayan hake sun kai hare-hare a kan wasu yankuna a kasar Iraki wadanda suka hada da Ambar da kuma Hit.
A duk wadan nan lokaci ba abinda Imam (a) bai yi da mutanen kufa na su fito yaki da shi don hana mu’awiya mamayar yankunan da suke karkashin ikons aba sun ki yin haka. Suna zaune a Kufa.
Don haka a lokacinda al-amarin ya kai matsayin da ba komawa baya , sai Imam (a) ya fara la’antarsu, saboda saba masa da suka yi ta yi har aka kai inda aka kai a lokacin. Sannan yana gurin All…ya dauke shi daga cikinsu, yana gurin mutuwa.
Ana cikin wannan halin a shekara ta 38 bayan aikin hajji, sai khawari jawa sun yi taro a Makka suka tattauna kan al-amuran da ke faruwa a kasashen musulmi da kuma irin halin da ake ciki. Sai suka yanke shawarar kashe shugabanni 3 wadanda suke jayayya a kan Mulki. Suka fara da Amirulmuminina (a), sai Abdurrahman dan Muljam al-Muradi ya dauki alhakin kashe shi, sannan Mu’awiya walin sham, wanda ya mamaye mafi yawan yankunan da suke karkashin ikin Imam Ali (a) , Hajjaju dan Abdullahi ya dauki nauyin kashe shi, sannan Amru dan Asi kuma Amru dan Bukair ya dauki alkawarin zai kiashe shi,
Banda haka sun Sanya rana guda da kuma lokaci guda na aiwatar da kissan. Wanda kuma shi ne safiyar ranar 19 ga watan Ramadan shekara ta 40 bayan hijira a lokacin sallar Asubaha.
Khawari jawan sun yanke wannan shawarar ba tare da wani tunani ba, kan cewa duk wanda aka kashe wani ne daga cikin mutanen wanda aka kashen zai hau, kuma kissan ba zai kawo wani al-khairi ga musulmi ba.
A cikin wannan Halin Abdurrahman Dan Mujam al-muradi ya shi birnin Kufa ya sauka a gidan diyar amminsa Qum wacce yake son aure. Sai ya samu ita ma tana makokin mahainta da dan’uwanta wadanda aka kashe a Nahrawan. Don haka yayi mata maganar aure, ta ce masa ba zai iya biyan sadakinta ba. Sai yace ta fada sai tace, dinari 3000, da bawa da mawakiya, da kuma kisan Imam Ali(a).
Sai ya amsa da cewa zai iya bayin kudade ya kuma saya mata bawa da mawakiya, amma kashe Aliyu dan Abi Talib (a) zai masa wuya saboda yana da masu kareshi da dama.
Anan tana boye masa kan cewa zuwansa Kufa tun asali a wannan karon don kashe Imam Ali (a) ne.
Amma sai ta zuga shi tana cewa idan ka kashe mani shi ka yaye mani bakin ciki a zuciya ta. Sannan idan an kashe ka kana da Lahira wanda ya fiye makama wannan duniyar. Idan kuma ka rayu kana da rayuwa mai dadi da (Qutam).
Sannan bayanda sahabban Imam Ali (s) suka fahinci cewa khawarijawa suna barazana ga rayuwar sa. Sai suka bukaci ya basu damar su kara yawan masu tsaronsa amma ya ki.
Don haka a cikin watan ramadan yakan ya buda baki a gida daya daga cikin yayansa, wata rana a wajen Imam Alhassam, wata rana a gidan Imam Al-Hussain (a), wataran kuma a gidan Abdullahi dan jaafaru, wanda yake auren diyarsa Zainab(a). Idan kuma an kawo masa abin buda baki baya fin loma uku. Da aka tambayeshi sai yace, bayan son Al-amarin All…ya zo masa face jana jin yuwa.
Sai kuma a daren 18 wayewar garin 19 na watan, Imam (a) ya kasa barci, ya na ta yawo a tsakiyar gida, yana Kallon sama, yana cewa
{Wallahi ban yi kariya ba, ba ai mani kariya ba, shi ne, shine, daren da aka yi mani alkawari}.
Imam Ali (a) ya kasashen a cikin tsawon dare yana cikin damuwa, yana ta ambaton All.., daga karshe ya zo ya kyautata al-walarsa ta karshe, ya kuma hanya zai fita zuwa masallaci sai ya gamu da agwagi suna ta kuka a gabansa, kamar suna fada masa cewa kana zuwa ga mutuwarka. Sai Imam Hassan dansa (a) ya ji karar mahaifinsa zai fita daga gida sai yayi sauri ya fito a rikice, ya babana me ya fito da kai a wannan lokaci na dare?
-Mafarkin da na ga ni a cikin wannan daren da ya dame ni,
Sai Imam Hassan (a) yace: alkhairi ka gani, kuma alkhairi zai kasance, bani labarin mafarkin.
Sai Imam (a) yace: Na ga jabra’il hakika ya sauko daga sama, a kan dutsen Abu Qubais , sai ya dauko duwatsu biyu daga kan dutsen, ya je da su wajen Kaaba, sai ya daki duwatsun da juna, sai suka dawo nikekke, sannan ya watsasu a cikin iska, ba wani gida da ya rage a Makka da Madina face wannan garin ya shiga cikinsa.
Imam Hassan (a) yace menen fassarar wannan mafarkin? Sai Imam (a) yace:
{Idan mafarkin nan ya zama gaskiya to, an kashe mahaifinka, babu wani gida da zai rage a makka da Madina face bakin ciki ya shige shi saboda ni.
Sai Imam Hassan (a) ya ji tsoro ya ce: {Yaushe hakan zai kasance? Sai yace: Ai All..ta’ala yana cewa {Kuma rai bata san abinda zata yi gobe ba, kuma rai bata san a inda zata mutu ba} Lukman 34. Amma masoyina manzon All..(s) ya fada mani, kan cewa hakan zai kasance a 10 na karshen watan Ramadan. Abdurrahman dan Muljam zai kashe ni.
Sai Imam Hassan yace:{Idan ka san haka ka kashe shi! Sai Imam yace: Baya halattan a yi kisasa kafin laifin kisa, laifin kisa bai faru ba.
Sai Imam ya cewa dansa Hassan(a) ya koma kan shimfidarsa. Don haka Imam Hassan (a) bai da wata mafita sai ya koma gida.
Don haka Imam(a) ya fita zuwa dakin All..a lokacin Sahur, ya zo cikin hadisai kan cewa a lokacin suhur ne, All..yana saukar da Rahamarsa, yake kuma saukar da Alkhairi da Albarka. An so mutum ya yawaita addu’a a lokacin.
A lokacinda Imam (a) ya shiga masallaci, sai y afara tada mutane daga barci kamar yadda ya saba, don su bautawa All..su kuma yi munajati da shi.
Bayan ya kammala hakan, sai y afara sallolinsa. Yana cikin wannan halin da sallah ga Ubangijinsa, zuciyarsa ta shagaltu da tunanin ubangijinsa, sai la’anenen Abdurrahman Dan Muljam ya zo ta bayansa ya zare takobinsa ya sare shi a tsakiyar kansa kusa da gushinsa, sai da takobin ya ratsa kansa har ya kai ga kwakwalwar Imam(a).
Kwakwalawam bai taba tunani bas ai alkhairi ga mutane. Ya tsaga gushinsa wanda bai taba sujud aba sai ga All..madaukakin sarki. A lokacinda Imam (a) ya ji zafin takobi a cikin kansa sai ya daga murya yana cewa: {Na rantse da Ubangijin Ka’aba na rabauta !.}
Hakika Imam (a) ya rabauta, ba wani rabautan da ta fi wannan, karshen rayuwarsa ta zo masana yana munajati da All..yana sallah zuwa gareshi, lebbansa na ambaton All..a cikin masallaci mafi tsarki a kuma cikin watan ramadan mai alfarma.
Inna lillahi wa ina ilaihi raji’un.
Masu sauraro a nan zamum dasa aya a cikin shirimmu nay au sai kuma wata fitowa idan All..ya kaimu. Wassalamu alaikum wa rahamatullahi wa barakatuhu.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Takunkuman MDD kan Iran sun fara aiki September 28, 2025 Kissoshin Rayuwa: Sirar Imam Hassan (A) 148 September 28, 2025 Nijar ta yi Tir da kasashen ketare kan tada zaune tsaye a Sahel September 28, 2025 Italiya : Mutane da dama sun jikkata yayin arangama da masu zanga-zangar goyon bayan Falasdinu September 28, 2025 Isra’ila ta kashe Falasdinawa kusan 100 a hare-haren da ta kai a Gaza September 28, 2025 Pezeshkian: Iran za ta dauki matakan da suka dace domin shawo kan takunkumi September 28, 2025 Afirka ta Kudu da Sin sun kara habaka huldar tattalin arziki don tukarar harajin Amurka September 28, 2025 Sheikh Qassem: Ba za mu mika makamin gwagwarmaya ba September 28, 2025 Iran: Kisan Nasrallah ya saba wa kundin tsarin mulkin MDD September 28, 2025 Argentina ta nemi jinkirta ziyarar Netanyahu a kasar saboda fargabar boren jama’a September 28, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: Abdurrahman dan a cikin wannan A cikin wannan masu sauraro
এছাড়াও পড়ুন:
Sojoji sun hallaka ’yan ta’adda 5 a Borno
Rundunar sojin Najeriya, ta bayyana cewa dakarunta sun kashe ’yan ta’adda biyar a wani samame da suka kai yankin Magumeri da Gajiram, a Jihar Borno.
Kakakin rundunar Operation Haɗin Kai, Kanar Sani Uba, ya ce dakarun sun yi arangama da wasu ’yan ta’adda 24 da ke tafe a ƙafa a ranar Juma’a.
Mutane 2 sun rasu a rikicin manoma da makiyaya a Kebbi Rashin wutar lantarki ta kassara kasuwanci a Kaduna, Kano da KatsinaA cewar sanarwar da ya fitar, sojojin sun yi nasarar kashe biyar daga cikinsu tare da ƙwato kuɗi Naira miliyan biyar.
“An hangi ’yan ta’addan suna ƙone gidaje da kuma kai wa mutane hari, sai dakarun suka fara bin su, inda suka tsere zuwa ƙauyen Damjiyakiri,” in ji Kanar Sani.
Ya ƙara da cewa bayan awanni huɗu ana bin su, sojoji suka sake kai musu farmaki, inda suka kashe biyar daga cikinsu, sauran 19 kuma suka tsere da raunuka.
Abubuwan da aka ƙwato daga hannunsu, sun haɗa da bindiga ƙirar AK-47, jakar harsashi gyda biyar, waya guda ɗaya da wuƙa.