HausaTv:
2025-10-13@15:53:19 GMT

Kissoshin Rayuwa: Sirar Imam Hassan (A) 148

Published: 28th, September 2025 GMT

148-Assakamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake
saduwa a cikin shirimmu na kissoshin rayuwa shiri wanda yake kawo maku
kissoshi wadanda suka zo cikin Al-Kur’ani mai girma ko cikin wasu littafan
wadanda suka hada da littafin Dastane Rastan na Aya. Shahid Murtadha Muttahari,
ko kuma cikin littafin mathnawi na maulana jalaluddeen romi, ko kuma cikin wasu
littafan, da fatan masu sauraro zasu kasance tare da mu a cikin wannan Shirin.


////…Madallah, masu sauraro idan kuna tare da mu a cikin shirimmu da ya gabata,
a kuma cikin sirar Imam Hassan Al-mujtaba (a) dan Fatimah (s) diyar manzon
All..(s) da muke kawo maku, a cikin shirimmu da ya gabata mun yadda Mu’awiya
dan Abusfyan ya kwace kasashen musulmi karkashin ikon Amirul muminina (a)
wadanda suka hada da Madina, Makka da Yemen da Hameden da kuma yadda
sojojinsa suka kawo hare-hare a cikin kasar Iraki, musamman a lardin Ambar da
kuma Hit suka kashe Hassan dan Hassan da wasu mutanen Iraki da dama.
Sannan yadda Imam Ali (a) yakan tashi a cikin mutanen Kufa ya kirasu zuwa
yakar hMu’awiya amma babu wani tasirin da khudubobinsa suke yi a cikin
zukatansu.
Zuciyarsu ta mutu har sai da ya kai ga Imam Ali (a) yayi addu’a a kansu, ya kuma
kai ga matsayin yana rokon All..ya fiddashi daga cikinsu, ya kuma maye shi da
shugaba mafi sharri a garesu.
Imam Ali (a) yayi bakin ciki mai yawa saboda kin fita yaki don yakar Mu’awiya
dan Abu Sufyan, har zuwa lokacin da zamu iya cewa sun yi letting don Mu’awiya
ya kwace mafi yawan kasashen musulmi karkashin Imam Ali (a).
Banda wannan mun yi maganar cewa khawarijawa sun sake bullowa, sun kuma
bayyana tawayensu ga gwamnatin Imam (a). Shugabansu shi ne Khurait dan
Rashid al-Naji, Imam (a) ya aika masu runduna wacce ya umurceta da farko ta yi

Mu’awiya dan Abu Sufyan ya kwace mafi yawan kasashen da suke karkashin
ikonsa. Da kuma sake bayyanar Khawarijawa da sauransu.
Amma bayan aikin Hajji a shekara ta 30 bayan hijira, sai Khawarijawa sun yi taro
a Makka bayan aikin hajji, suka tattauna kan yadda al-amuran musulmi suka
lalace, ba tare da ambaton cewa su ma suna daga cikin matsalolin musulmi, don
sun kasa gano waye shugaban na gaskiya a cikin wadanda suke jayayya a cikin
shuwagabannin musulmi ba. Jahilsu ya kai mai kama da manzon All…(s) na
cikinsu amma suka kasa gane shi. Banda haka sune mafi adawa da shi a cikin
musulmi. Wanda ya nuna ko da manzon All..(s) ya dawao zasu yake shi, a
matsayin wanda ya fita daga addinin musulunci.
Daga cikinsu kamar yadda muka bayyana a cikin shirye-shiyemmu na baya, kan
cewa yace manzon All..(s) bai yi adalci a rabonsa ba. (All..ya kiyaye mu).
Don haka bayan taron sun yanke shawarar cewa zasu kashe mutane uku wadanda a
ganinsu suka haddasa halin da musulmi suke ciki. Kuma sune Amirulmumina
Aliyu dan Abutalib (a) wanda Abdurrahman dan Mujam Almuradi ya dauki
alkawalin zai kashe shi, sai kuma Amru dan Asi shugaban kasar Masar wanda
Amru dan Bukair Attamini ya dauki alkarin kashe shi sai kuma mu’awaiya dan
Abu Sufyan wanda a lokacin ya kwace mafi yawan daular musulunci daga ikon
Amirul muminina Aliyu dan Abutalib (a). wanda kuma Hajjaj dan Abdullahi
Assarimi ya yi alkawalin zai kashe shi.
Banda haka sun ittifaki kan kissan ya kasance a lokacin sallar Asubaha ta ranar 19
ga watan Ramadan ta shekara 40 na shekara ta 40 bayan hijira. Da haka suka rabu
kowa yak ama gabansa.
Abdurrahman dan muljam Al-muradi ya shirya takobinsa, wanda ya jikashi cikin
guba da dinari 1000.

Sannan a bangaren Amirulmuminina kuwa hatsarin khawarijawa gare shi yana
dada bayyana, don haka wasu daga cikin sahabbansa sun bukaci ya basu dama su
kara kyautata tsaronsa, amma yaki haka. Yana cewa
{Lalle Aliyu yana da kariya daga All..mai karfi, idan ranar mutuwa ta ta zo,
zai dauke wannan garkuwan ta sannan garkuwa ta sallamani, a lokacin
kibiya ba zata kuranye bararsa ba, kuma raunin da zata yi ba zai warke ba}.
A lokacinda watan Ramadan ta shekara ta 40 bayan hijira ya shigo Amirul
muminia (a) yana buda baki a gidan dansa Imam Al-Hassan, wata rana a gidan dan
Imam Al-hussain (a) wannan wata rana a gidan Abdullahi dan Jaafaru mijin
diyarsa Zainab.
Kuma idan ya zo buda baki baya fin loma uku ba. Da aka tambayeshi (a) sai yace
{Ina son al-amarin All..ya zo mani ina jin yunwa}.
Sannan a lokacinda Abdurrahman dan muljam Almuradi ya shiga kufa, ya zo ya
dushe hasken All.. a doron kasa, ya zo ya kashe Amirul muminina (a). Da farko ya
sauka a gidan diyar amminsa Qutam, wacce yake tsananin sonta, yana son aurenta.
Banda haka Qotam tana da kyau wanda yake jawo hankalin mazaje.
Ya shiga wajenta ya tuna mata batun aures ai tace masa, bayan iya biyan sadakinta
ba, sai ya zai iya biya ko menen tsadarsa.
Sai lissafa mata sadakinta, daga ciki ta ce dinari 3000, na kudi, sannan da bawa da
kuma mawakiya sannan na karshen, kamar yadda ya zo a cikin wasu ruwayoyi da
kan Aliyu dan Abitalib(a). Saboda tana makokin mahaifinta da danuwanta
wadanda aka kashe a yakin Nahrawan, wanda ya nuna tana dauke da ikidar
khawarijawa.

Dan mulkin ya ce zai biya dukkan abinda dukiya zai same shi, na dinari 3000, da
bawa da mawakiya, amma kan Aliyu dan Abitalib, yadda yake da masu tsaronsa da
wuya ya samu.
A nan yana boye mata kan cewa kashe Aliyu dan Abitalib (a) ne ya zo da shi Kufa.
Amma duk da cewa bata san shi ne ya kawo shi Kufa ba, amma ta yi ta zuga shi
tana cewa idan ka kashe shi ka yaye bakin cikin da ke cikin zuciya ta. Idan kuma
na kashe ka kana da abinda yafi duniya a Lahiri, idan ka sami nasara kuma kana da
rayuwa da maid ani da Qutam.
Wannan ya tabbatar da cewa tana da akidar Khawarijawa, wadanda suke ganin
sune kawai musulmi, kuma idan sun mutu wajen kashe sauran musulmi shahidai ne
zasu shiga aljanna.
Dangane da sadakin Qutam, Farazdak mawakin iyalan gidan manzon All…(s) yana
cewa a wata kasidar da ya rera:
Ban taba ganin Sadakin da wani mai daraja- Mawadaci da ko talaka, kamar
Sadakin Qutam ba.
Dinari dubu 3, da bawa da mawakiya..Da sare Aliyu(a) da takobin da aka Sanya a
Guba.
Ba sadakin da ya fi Aliyu(a) ko menene yawansa-Babu kisa kamar kisan dan
Muljam.
Na rantse da Baitul Harami da wanda ya zo-Masa a bayyane cikin harami da ba
harami ba.
Hakika wanda yayi kokarin kashe limaminsa ya Tabe-Bone ya tabbata a gareshi
daga zafin wutan Jahannama.

Don haka a daren 18 ga watan Ramadan ya karaso, Imam (a) ya kasa barci a cikin
dare, yana ta yawo a tsakiyar gida, sannan ya duba sama daga lokaci zuwa lokaci,
yana cewa
{Ban yi kariya ba, kuma ba’a yi mani karya ba, Lallai daren ne, wanda aka yi
mani alkawali a cikinta}.
Masu sauraro a nan zamu dasa aya a cikin shirimmu na yau sai kuma wata fitowa
idan All..ya kaimu wassalamu alaikum wa rahamatullahi wa barakatuhu.

Share

0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Takunkuman MDD kan Iran sun fara aiki September 28, 2025 Nijar ta yi Tir da yadda kasashen ketare ke da hannu wajen tada zaune tsaye a yankin Sahel September 28, 2025 Italiya : Mutane da dama sun jikkata yayin arangama da masu zanga-zangar goyon bayan Falasdinu  September 28, 2025 Isra’ila ta kashe Falasdinawa kusan 100 a hare-haren da ta kai a Gaza September 28, 2025 Pezeshkian: Iran za ta dauki matakan da suka dace domin shawo kan takunkumi September 28, 2025 Afirka ta Kudu da Sin sun kara habaka huldar tattalin arziki don tukarar harajin Amurka September 28, 2025 Sheikh Qassem: Ba za mu mika makamin gwagwarmaya ba September 28, 2025 Iran: Kisan Nasrallah ya saba wa kundin tsarin mulkin MDD September 28, 2025 Argentina ta nemi jinkirta ziyarar Netanyahu a kasar saboda fargabar boren jama’a September 28, 2025 Sojojin Isra’ila Sun Kashe Sama Da Falasdinawa 77 A Gaza A Yau Kawai. September 27, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci About Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS News Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Explore Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS

উৎস: HausaTv

কীওয়ার্ড: masu sauraro

এছাড়াও পড়ুন:

Sojoji sun hallaka ’yan ta’adda 5 a Borno

Rundunar sojin Najeriya, ta bayyana cewa dakarunta sun kashe ’yan ta’adda biyar a wani samame da suka kai yankin Magumeri da Gajiram, a Jihar Borno.

Kakakin rundunar Operation Haɗin Kai, Kanar Sani Uba, ya ce dakarun sun yi arangama da wasu ’yan ta’adda 24 da ke tafe a ƙafa a ranar Juma’a.

Mutane 2 sun rasu a rikicin manoma da makiyaya a Kebbi Rashin wutar lantarki ta kassara kasuwanci a Kaduna, Kano da Katsina

A cewar sanarwar da ya fitar, sojojin sun yi nasarar kashe biyar daga cikinsu tare da ƙwato kuɗi Naira miliyan biyar.

“An hangi ’yan ta’addan suna ƙone gidaje da kuma kai wa mutane hari, sai dakarun suka fara bin su, inda suka tsere zuwa ƙauyen Damjiyakiri,” in ji Kanar Sani.

Ya ƙara da cewa bayan awanni huɗu ana bin su, sojoji suka sake kai musu farmaki, inda suka kashe biyar daga cikinsu, sauran 19 kuma suka tsere da raunuka.

Abubuwan da aka ƙwato daga hannunsu, sun haɗa da bindiga ƙirar AK-47, jakar harsashi gyda biyar, waya guda ɗaya da wuƙa.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Falasdinawa Sun Gano Gawakin Wadanda HKI Ta Kashe A gaza  Fiye Da 320 Cikin Kwanaki Biyu Kacal
  • Soja ya kashe matarsa, ya hallaka kansa a Jihar Neja
  • An Wallafa Ra’ayoyin Shugaba Xi Kan Batutuwan Da Suka Shafi Mata Da Yara Cikin Karin Harsunan Waje
  • Maryam Sanda na cikin waɗanda Tinubu ya yi wa afuwa
  • ’Yan sanda sun ceto mutum 10 daga hannun ’yan bindiga a Kaduna
  • Tarihin Hassan Usman Katsina (1)
  • Wasu Daga Cikin Muhimman Alamomin Ciwon Kansa
  • Sojoji sun hallaka ’yan ta’adda 5 a Borno
  • ’Yan bindiga sun kashe sojoji 3 a Kebbi 
  • ’Yan bindiga sun kashe Civilian JTF 8 a Zamfara