Me Ake Nufi Da Ado?
Published: 26th, September 2025 GMT
Saboda haka ne ma a yanzu, duk idan za a yi nazarin al’adar mutane, sai an karanci yadda suke kallon ado da kuma yanayin adonsu. Ta yadda za a iya fahimtar wadanne samfurin ado ne daidai, wadanne ne kuma ba daidai ba. don haka shi lamarin ado wani babban abu ne mai kusanci da al’ada, duk kuwa yadda mutane suka kai ga gurbata al’adunsu da wasu al’adun wasu wuraren, sai ka tarad da birbishin tufafi ko suturar ado na gargajiya wanda ke bambanta tsakaninsu da wasu al’adun.
Da yawan mutane sukan kuskure abin da ake nufi da ado, wasu sun dauka cewa dole ne yadda suke kallon ado a al’adarsu ta kasance haka a wasu al’adun. Misali, sai a samu Bahaushen da ke ganin ado shi ne kawai a sa shadda mai kyau da babbar riga, a yi mata aikin hannu na alfarma, sannan a samo hula kube. Wannan shi ne kurewar ado a wurin bahaushe. Amma idan ka yi wannan ado a wasu yankunan na duniya dariya za a yi maka. Saboda kayan mata ne kawai a ke yi musu aiki a jikin riga.
Akwai wani abokina da ya taba bani labari, ya na karatu a yankin Asia. Farkon zuwanshi, sai watarana ya yi ado irin na hausawa, sa hularsa ta kube. Tun fitowarsa daga gida ake kallonsa cike da mamaki, wasu sukan tsayar da shi suyi hoto, wasu kuma su yi ta mishi dariya, akwai ma wuraren da ake binsa ana ja mishi kaya.
Wani babban abu da ado shi ne yadda ya zama hanyar samar da aiki da samun kudi ga al’umma. Sannan ya na samar da hanyoyin kudin shiga, walau daga ciki ko daga wajen kasa. Idan kasa ko gari suka shahara a fagen dinki, za a rika tururuwa zuwa kawo dinki daga sassa daban-daban, wasu kuma sukan shahara ne a fagen yin ado akan tufafi, shi ma z aka taras ana yi musu tururuwa. Kamar misali, garin Zariya ya shahara da masu yin aikin hannu da ado akan tufafi, wannan ya sa matasa da dama sun samu sana’ar da suke iya rike iyalinsu da ita.
Idan ka tafi yankin Barebari a wuraren Borno, can zaka tarad da yadda ake sarrafawa hulunan kube, sakan hannu sai wanda kake so. Duk wata hula ta kece raini daga can take fitowa. Ba kawai a samun kudin siyar da hulunan mutanen wannan yankin suka takaita ba. sun bi garuruwan Nijeriya sun bubbude shagunan siyarwa da wankin hula. Kuma duk idan ka kai musu wanki sau daya, shi kenan ka yi ta kawowa kenan, saboda kwarewa da sanin makamar aikin.
Duk wadannan abubuwan na nemo sutura; shadda ko yadi masu kyau, zuwa nemo mai dinki wanda ya kware, zuwa ga nemo hula wacce aka zana ta da kyau suna da alaka mai karfi da ado. Kuma wannan adon ta fuskacin al’adun mutanen Arewa ne. hatta a Nijeriya, ba zai zama kurewar ado a wurin Inyamuri ko Bayarabe ba, don ka sa babbar riga da aiki mai kyau, da hular kube.
Abin da nake son nunawa a nan shi ne, shi ado mutane da al’adarsu ne ke samar da shi. misali, akwai wata al’umma wadanda ke yin ado da jinin dabba. Idan aka yanka dabba, shanu ko rago ko tinkiya, sai su tattara jinin dabbar su busar a rana. Idan ya bushe sai su rika shafawa a matsayin hoda. Su a wurin ‘yan matansu wannan wani samfurin ado ne mai jan hankali. Amma idan ka ce ma wasu mutanen a wani yanki su aikata haka, za su ga kamar ka yi hauka ne.
Idan mutum na mu’amala da kasuwannin siye da siyarwa na duniya, zai ga yadda kayan ado suke. Tufafi da takalma za ka ga kowanne da kudinsa, kayyadadden farashi. Akwai wani takalmi da na taba gani a irin wadannan kasuwanni, farashinsa naira dubu 200,000 a kudin Nijeriya. a maganar gaskiya, ni ko kyauta aka bani takalmin zai yi wahala na amsa, saboda mu a wurin ba wai kawai ba ado bane, a’a za ma a rika yi maka wani irin kallo ne.
Haka kuma akwai wani lokaci da aka kawo min wani takalmi daga wata kasa, irin takalmin nan da ake shiga dusar kankara da shi ne ‘Snow’. Tun da aka kawo na ajiye takalmin, na kasa yin amfani da shi, saboda mutane zasu rika yi min wani irin kallo. Takalmin jibgege ne, amma kuma yana da kyau sosai. Sai da yayi shekaru a ajiye, sai wani abokina ya zo ya ganshi a ajiye, sai ya tambaye ni me ya sa bana amfani da takalmin nan? Sai na ce, yayi min girma, shi kenan sai ya dauka, shi a wurinshi zai yiwu yayi ado da shi a Nijeriya, kuma komi daidai. Idan ka fahimci ado da kyau, tuni za ka daina tsaurararawa.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Mutane 2 sun rasu a rikicin manoma da makiyaya a Kebbi
Aƙalla mutane biyu ne suka mutu a rikicin da ya ɓarke tsakanin manoma da makiyaya a unguwar Dambo, wani kauye da ke da tazarar ’yan kilomita daga Birnin Kebbi, babban birnin Jihar Kebbi.
Wani mazaunin yankin mai suna Ɗanladi Usman ya ce rikicin ya fara ne bayan an kashe wani mutum mai suna Sule yayin da yake aiki a gonarsa.
“Kashe Sule ya tayar da hankulan al’umma, inda manoma suka ɗauki fansa suka kashe wani makiyayi da har yanzu ba a gano sunansa ba,” in ji shi.
Ya ƙara da cewa makiyayan sun sha faɗa da manoma a kwanakin baya bayan sun aike musu da sako cewa su hanzarta girbe amfanin gonakinsu domin za su riƙa wucewa da shanunsu ta gonakin nan ba da daɗewa ba.
An yi jana’izar sojojin da ’yan bindiga suka kashe a Kebbi Rashin wutar lantarki ya rusa harkoki a Kaduna, Kano da Katsina“A lokacin da wasu manoma suka je gonakinsu domin yin aiki, sai makiyaya suka kai musu hari, daga nan ne aka shiga tashin hankali,” in ji shi.
Wani mazaunin yankin, Abubakar Aliyu, ya roƙi gwamnati da ta kawo ƙarshen wannan rikici na dogon lokaci tsakanin manoma da makiyaya.
“Wannan matsala ba sabuwa ba ce, kuma sarakunan gargajiya sun san da ita. Muna fatan a samu adalci ga waɗanda abin ya shafa, kuma gwamnati ta kawo ƙarshen wannan rikici,” in ji shi.
Rundunar ’yan sanda a jihar ba ta tabbatar da faruwar lamarin ba domin jami’in hulda da jama’a na rundunar, CSP Nafiu Abubakar, ba a iya samun sa a waya ba lokacin da ake haɗa wannan rahoto.