‘Da albashin aikin masinja na fara kasuwancin Sahad Store’
Published: 26th, September 2025 GMT
Sahad Store sanannen suna ne a fadin Nijeriya, wanda yawancin wanda ya ji sunan, abin da ke fara zuwa ransa shi ne manyan shagunan sayar da kaya. Amma ba kowa ne ya san tarihin yadda ya faro ba, balle mallakinsa.
Alhaji Ibrahim Mijinyawa, dan kasuwa, haifaffen unguwar Mandawari da ke birnin Kano. A cikin wata hirarsa da gidan Talabijin na Kaftan TV, a shirin Sirrin Nasarar Kasuwanci, attajirin ya bayyana yadda ya fara kasuwancinsa da yadda ya samar da sunan Sahad.
Alhaji Mijinyawa wanda mahaifinsa dan unguwar Tamarmara ne da ke kusa da Mandawari, ya ce rayuwarsa cike take da dinbin abubuwan mamaki, wadanda lokaci ba zai bayar da damar ya iya zayyana su a dan takaitaccen lokaci ba.
Ya ce an haife shi ne bayan iyayensa sun dade ba su taba samun haihuwa ba sai a kansa, kuma bayan an haife shi yana karami wani sanadi ya faru mahaifinsa ya rabu da mahaifiyarsa, wadda ita ma ita kadai kakarsa ta haifa.
Ganin haka sai ita kakar, Mari Mai Koko ta dauke shi. Hakan ya sa ya girma a gabanta ba tare da ta sa shi a makarantar Islamiyya ko boko ba, sai da ya girma ya fara sanin muhimmancin ilimi sannan ya sanya kansa a makarantar allo cikin yara har ya samu ilimi daidai gwargwado.
Shi ne kuma ya kai kansa wata makarantar boko ta wasu ’yan kabilar Ibo da suke koyarwa da yamma, mai suna Festibal. Kuma babu wani mai taimaka masa sai ita kakar tasa wacce duk wanda yake da shekaru a lokacin ya san ta domin sananniya ce a unguwar Mandawari.
Yaushe ka fara kasuwanci?
Lokacin da na fara kasuwanci shi ne, na fara aikin masinja ne a wani kamfani lokacin ana biya na Fam 7 da 10 a wata. Ina aikin ban shekara ba, wata 9 kawai na yi, ina samun albashi ina tara ’yan kudade a Antikurya, wani aljihu ne cikin aljihu irin na mutanen da, wanda idan kaga an kwace ma kudin nan sai dai idan shake ka aka yi. Suna taruwa kawai sai na ce na bar aiki, sai na fara kasuwancin sayar da yadi. Sannan ina da keken hawa sai na fara tallar yadi a kan keke. A lokacin akwai wani yadi da ake dinka wando da shi, muna zuwa wurin ’yan gwanjo muna sayen guntu-guntun yadinsa ina kai talla Tashar Kuka da Tashar Nasarawa. A lokacin kuma aka jarrabu da rashin ciniki domin za ka iya share kwanaki uku ba tare da ka yi ciniki ba.
Ina tallar yadin ne sai Allah Ya kawo wata shekara da na bude Kes na katako wanda ni ne na fara bude irinsa na farko, domin duk inda ka ga Kes na lemon kwalba be ko kunun zaki ake sayarwa.
Ni Kuma basirata ta nuna min na canja tsarin Kes zuwa kantin sayar da yaduna. Sai ciniki ya bude sai na sake neman wani waje a Kasuwar Kantin Kwari wajen ’Yan Tebur na fara kasa kaya a nan. Cikin ikon Allah ban dade ba sai aka yi wani Kantoma mai suna Uba Adamu, ya ce dole kowa ya tashi a koma Kasuwar Kofar Wambai, inda mu ne muka fara bude ta, aka ba mu rumfunan kasuwa. A lokacin sai na sayar da nawa na kara zuba jari a Kes dina, sai na yi wata dabara, ina fita talla da safe a kekena, da yamma na dawo na kasa a Kes dina da ke nan a unguwar Mandawari.
Da sayar da yadin ya bunkasa sai na fara tafiye-tafiye ina sayo kayayyaki irin leshin mata da ’Yar Ingila da sauran manyan zannuwa da a lokacin duk Kano ni kadai nake irin su.
Za ka iya tuna a wane lokaci ne ka yi wannan gwagwarmaya?
A lokacin shugaban kasa na farar hula, Shehu Shagari ne.
Ya aka yi ka samu sunan Sahad?
Sunan ya samo asali ne a lokacin yakin Saddam Hussein — tsohon Shugaban Kasar Iraki, lokacin da sunan kantina Fahad ne a lokacin. Ana yaki kuma Nijeriya ba ta goyon bayan daya kasar kuma ina da shago sai jama’a suka ce min ko na canza sunan kantina ko kuma duk abin da ya samu kantina ni na jawo wa kaina.
Kuma a lokacin ba ni da karfi, kuma idan za ka rubuta sunan shagonka kalmomin da rubutu mai amfani da hasken lantarki ake yi, kuma yana da tsada ni. Kuma a lokacin ba ni da kudin da zan canja duka. Sai na shiga lissafin yaya za a yi, sai na zauna na dauko kalmomi daban-daban ina gwadawa domin harafin farko kawai na ‘F’ na cire zan canza.
Na dauko harafin ‘A’ Ahad na ga bai yi ba, na cire na dauko B, Bahad, nan ma bai yi min ba. Ina sa ‘S’, Sahad sai na ji ya yi min dadi sunan, shi ne na canza zuwa Sahad daga Fahad.
Wata baiwa ta Allah kuma, tun daga lokacin sai na kara samun budi har gidajen rediyo suna ta zuwa daukar bayanai cewa wani babban shago ya canza suna daga Fahad, ya koma Saddam, ba su gane cewa Sahad ba ne. Sai Kantin ya kara karbuwa.
Ana nan sai wani iftila’i ya faru, aka yi wani gwamna, Abubakar Rimi, sai ya zama ya raina Shugaban kasa Shagari, yana ce masa Shagarai, sai shi kuma ya fusata ya sa jami’an hukumar Kwastam su takura kowa har Kantin Kwari, duk mai kayan kasar waje su kama.
Hakan ya caja mana kai, ana haka sai na yi shawarar cewa tunda an fara samun matsala, me zai hana na canja wata sana’a. A nan ne na sayi wani fili a nan titin Mandawari na gina kantin da sunan ‘Super Market’ mai suna Fahad, kafin wancan labari da na ba ka na yadda sunan ya koma Sahad.
Muna ci gaba da kasuwancimu sai Buhari ya yi juyin mulki, ya ce duk wata rumfa a ko’ina a rushe ta, a nan ne na cire kantina na koma shagon da na kama ban koma ba na gidan Malam Nasir Kabara. Daga gidan Malam Nasir Kabara sai na koma na sayi shago a Kantin Kwari. Ina nan sai aka zo da yayin wata atamfa [mai suna] Batik, nan ma na shahara a kanta har Allah kuma Ya sa na kai ga bude shago a Babban Birnin Tarayya, Abuja. A lokacin kuma da Naira miliyan takwas na je na sayi fili na gina na zuba kaya a nan Zone 4, inda na gina gidana a sama, kasa kuma shagunan kasuwanci, har komai ya kara habaka.
Kuma wani abin ma shi ne, ba na bayar da bashi, amma ina rage kudin kaya. Idan ana sayar da kaya Naira dubu daya ni zan iya sayar da nawa Naira dari tara da hamsin ko da tamanin, amma ba na bayar da bashi, da haka na mamaye kwastomomina.
Bayan Kano da Abuja ko kana da wasu kantuna a wasu jihohi?
Ina da kanti a Jigawa wanda Sule Lamido ya ba ni fili na gina, ina da shi a Minna, Jihar Neja da Maiduguri, da Bauchi wadanda na kusa bude su. Akwai ma a Kaduna, nan ma El-Rufa’i ne ya ba ni waje na gina.
Akwai labarin cewa kana da asibiti, ya aka yi kuma aka karkata zuwa harkar kiwon lafiya?
E, ina da asibiti amma shi ban gina shi don neman kudi ba, don neman lada na gina, wanda ko na mutu ya zama ina da hanyar samun lada mai gudana. Akwai makaranta ma da masallaci saboda kar lada ya yanke min lokacin da nake bukatar ta sosai.
Ko kana da ra’ayin tsallakawa zuwa wata kasa don kara fadada kasuwancinka?
Bani da ra’ayin haka. Saboda ko danka ka ajiye wajen kasuwanci sai ka hada da hakuri, muddin babu hakuri ba za a kai ga samun nasara ba, kuma ina son ’yan kasata su amfana da arzikina.
Yaya batun Iyali?
Ina da mata 4 da ’ya’ya 19 kuma cikinsu akwai wadanda na sa suka karanci Likitanci saboda gudanar da asibitin.
An san dan kasuwa da yawo, ko ba a tambaya ba. Shin za ka iya sanin kasashe nawa ka je a duniya?
Duk da ban yi boko sosai ba kuma ban iya turanci ba, babu kasar da ban je ba a duniya.
Kuma ba wai zuwa na je-ka -ka-dawo ba, zuwa sosai, na yi mu’amula sosai na dawo. Duk kasar da na je, na san ta sosai fiye da yadda kake tsammani.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Ibrahim Mijinyawa fara kasuwanci
এছাড়াও পড়ুন:
‘Yansanda Sun Tabbatar Da Mutuwar Wata Ba’amurkiya Da Ta Ziyarci Saurayinta A Jihar Delta
Rundunar ‘yansanda ta tabbatar da cewa ana gudanar da cikakken bincike domin gano ainihin musabbabin mutuwarta.
ShareTweetSendShare MASU ALAKA