’Yan bindiga sun kashe mutum 5 a Masallaci a Zamfara
Published: 26th, September 2025 GMT
Aƙalla mutum biyar ne suka rasu lokacin da ’yan bindiga suka kai hari wani Masallaci, yayin da ake tsaka da sallar Asuba a garin Yandoto da ke Ƙaramar Hukumar Tsafe a Jihar Zamfara.
Harin ya faru ne da safiyar ranar Juma’a, lamarin da ya girgiza al’ummar yankin.
‘Da albashin aikin masinja na fara kasuwancin Sahad Store’ Ganduje ya gindaya wa Kwankwaso sharadin shiga APCShaidu sun ce maharan sun kutsa cikin Masallacin inda suka fara harbi ba tare da ƙaƙƙautawa ba, inda suka kashe mutum biyar nan take tare da jikkata wasu da dama.
Wani mazaunin yankin da ya nemi a sakaya sunansa, ya ce maharan sun kuma yi awon gaba da wasu Masallata.
Ya bayyana lamarin a matsayin “rashin imani da ta’addanci.”
Ya ƙara da cewa wasu daga cikin waɗanda suka ji rauni yanzu haka suna asibiti ana kula da su.
Da aka tuntuɓi kakakin rundunar ’yan sandan Jihar Zamfara, DSP Yazid Abubakar, ya ce ba shi da labarin faruwar lamarin.
Harin na zuwa ne mako guda bayan makamancin irinsa a ƙauyen Gidan Turbe, wanda shi ma ke Ƙaramar Hukumar Tsafe, inda aka yi garkuwa da aƙalla Masallata 40 yayin da suke tsaka da sallar asuba.
A wani labarin kuwa, masu haƙar ma’adinai 100 ta ɓarauniyar hanya ake fargabar sun rasu bayan rami ya rufta musu a kauyen Kadauri da ke Ƙaramar Hukumar Maru, a jihar Zamfara.
Majiyoyi sun bayyana cewa lamarin ya auku a ranar Alhamis, inda ramin ya rufe mutane da dama.
Kafin ceto waɗanda suka maƙale, rai ya yi halinsa, sakamakon ɗaukar lokaci da suka yi a ƙarƙashin ƙasa.
A halin yanzu, an tono gawarwakin mutum takwas; dukkaninsu mazauna ƙauyen Mekwanugga.
An kai garinsu domin yi musu jana’iza, kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Yan Bindiga hari Masallaci Sallar Asuba Zamfara
এছাড়াও পড়ুন:
Kotu ta yanke wa mutum 5 hukuncin rataya a Oyo saboda aikata kisan kai
Babbar Kotun Jihar Oyo da ke Ibadan, babban birnin jihar, a ranar Litinin ta yanke hukuncin kisa ta hanyar rataya ga mutum biyar da ta samu da laifin kashe wani direban tasi.
Kotun dai ta sami mutanen ne da laifin kashe direban mai suna Akeem Shittu a lokacin mummunan rikici a shekarar 2024.
DAGA LARABA: Shin Ya Kamata A Biya Kudin Fansa Ga Masu Garkuwa Da Mutane? An sako ɗalibai 25 da ’yan bindiga suka sace a KebbiYayin yanke hukunci, alkalin kotun, Mai Shari’a Oyeyemi Ajayi ya bayyana cewa Segun Taiwo (36), Kehinde Ademola (46), Yahaya Adeniyi (45), Chinonso Samson (41), da Opadotun Michael (32) sun yi tarayya wajen yin hadin baki da kuma kisan Shittu.
“Na yi la’akari da cewa kotu za ta iya tabbatar da hadin baki a cikin ayyukan da suka kai ga mutuwar Shittu,” in ji shi.
Saboda haka, ya yanke wa kowanne daga cikin su hukuncin shekaru 20 a kurkuku saboda makirci, sannan ya yanke hukuncin kisa ta hanyar rataya saboda laifin kisan kai.
“A kan tuhuma ta biyu, kowanne daga cikin waɗanda ake tuhuma an yanke masa hukuncin kisa ta hanyar rataya,” in ji alkalin.
Tun da farko, Lauyar gwamnatin Jihar, K. K. Oloso, ta bayyana yadda ƙaramin hatsarin hanya ya rikide zuwa mummunan hari.
Ta ce a ranar 10 ga Afrilu, 2024, da misalin ƙarfe 8:30 na dare, a kan titin Elepe, Arulogun Road, yankin Ojoo na Ibadan, waɗanda ake tuhuma tare da wasu da har yanzu ba a kama ba sun kai wa Shittu hari bayan ya yi karo da babur mai ɗauke da fasinjoji biyu.
“An ce ɓangarorin sun tafi wata mashaya kusa domin sasanta lamarin. A can, ƙungiyar masu babur ta nemi N50,000 don yin magani, amma Shittu ya iya bayar da N8,000 kawai. An hana shi barin wurin, aka cire masa kaya, kuma duk da cewa ya yi ƙoƙarin tserewa na ɗan lokaci, daga baya aka kewaye shi aka yanka shi da adda har lahira.”
Masu bincike daga baya sun gano motar tasi dinsa da mayafinsa a gaban shagon matar ɗaya daga cikin waɗanda aka yanke wa hukuncin.
Lauyar gwamnatin ta jaddada cewa laifukan sun sabawa sashe na 316 kuma laifuka ne a ƙarƙashin sashe na 319 da na 324 na Dokar Laifuka ta Jihar Oyo ta 2000, wadda ta tanadi hukunci mai tsanani ga makirci da kisan kai.