Gwamnatin Kano Ta Mika Ƙorafe-Ƙorafe Kan Sheikh Lawan Triumph Zuwa Majalisar Shura
Published: 26th, September 2025 GMT
Gwamnatin Jihar Kano ta bayyana cewa ta karɓi ƙorafe-ƙorafe da dama da kuma martani daga ƙungiyoyin addinin Musulunci kan kalaman da Sheikh Lawan Triumph ya yi kwanan nan a jihar.
A cewar sanarwar da ofishin Sakataren Gwamnatin Jihar ta fitar ta hannun mai magana da yawunsa, Musa Tanko, Gwamna Abba Kabir Yusuf ya amince a miƙa batun ga Majalisar Shura ta Jihar Kano domin yin nazari da tattaunawa.
Ƙungiyoyin da suka shigar da ƙorafe-ƙorafen sun haɗa da Safiyatul Islam of Nigeria, da Tijjaniya Youth Enlightenment Forum, da Interfaith Parties for Peace and Development, da Sairul Qalbi Foundation, da Habbullah Mateen Foundation, da Limaman Masallatan Juma’a ƙarƙashin Qadiriyya Movement, da Kwamitin Malaman Sunnah na Kano, da kuma Multaqa Ahbab Alsufiyya.
Sakataren Gwamnati, Alhaji Umar Farouk Ibrahim, ya ce gwamnatin jihar ta jajirce wajen tabbatar da zaman lafiya, da haɗin kai da mutunta juna tsakanin dukkan ƙungiyoyin addini, tare da kira ga jama’ar Kano da su kasance cikin kwanciyar hankali kuma su ci gaba da gudanar da harkokinsu na yau da kullum ba tare da tashin hankali ba.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppকীওয়ার্ড: Lawan Triumph
এছাড়াও পড়ুন:
Allah Ya yi wa Sheikh Dahiru Bauchi rasuwa
Fitaccen malamin addinin Musulunci nan daga Jihar Bauchi, Sheikh Dahiru Usman Bauchi, ya rasu.
Ɗansa, Sayyadi Ali Dahiru Usman Bauchi ne, ya tabbatar wa Aminiya rasuwar malamin.
Juyin mulki ya rutsa da Jonathan a Guinea-Bissau Ɗan bindiga ya harbe sojoji 2 a fadar shugaban AmurkaYa ce sun karɓi wannan ƙaddara tare da gode wa Allah bisa rayuwar da malamin ya yi.
“Tabbas Sheikh ya koma ga Mahaliccinsa. Daga Allah muke, kuma gare Shi za mu koma,” in ji Sayyadi.
“Lokacin Sheikh ya yi. Mun gode wa Allah Maɗaukaki. Ya bai wa Sheikh tsawon rai, kuma rayuwarsa ta yi kyau. Alhamdulillah,” in ji shi.
Sayyadi, ya ce zuwa yanzu ba su yanke inda za a yi jana’izar malamin ba.