An kashe ’ya’yan magoya bayan Gwamna Zulum
Published: 25th, September 2025 GMT
Wasu da ake kyautata zaton ’yan bangar ’yan siyasa ne sun kashe wasu yara biyu na Zannah Jaridama Bornoye wani mai goyon bayan Gwamnan Borno Babagana Zulum, da na maƙwabcinsa kwanaki kaɗan bayan da Zannan ya fito ƙarara ya caccaki waɗanda ake zargin ’yan siyasa ne a jihar da ke zagon ƙasa ga gwamnatin Zulum.
Kamar yadda rahoton ke nunawa Zannah Jaridama, wanda ya zargi wasu manyan mutane da munafunci da zagon ƙasa ga gwamnatin mai gidansa Gwamna Zulum, ya koka a cikin wani faifan bidiyo.
Zan kare muradun Yarbawa idan aka zaɓe ni a 2027 — Atiku Hajjin 2025: Mun samu nasarori a Yobe — Mai Aliyu BiririYana cewa, wasu mutane na kusa da gwamnan suna nuna cewa masu biyayya ne tare da wadatar da kansu da kwangiloli, muƙamai da dukiyar gwamnati ba tare da nuna kishin gaskiya ga jama’a ko hangen nesa na gwamna ba.
Ya koka da cewa, yayin da Farfesa Zulum ke ɗaukar nauyin mulki da ayyuka da yawa daga cikin waɗanda ke da’awar cewa su ne masu yi masa biyayya, yadda suke gina manyan gidaje na alfarma sai ga shi suna zagon ƙasa ga gwamnatinsa.
Daga bisani ya jajirce kan duk wanda ya ji bai masa daɗi ba ya kai shi kotu, yana mai cewa zai bayyana sunayensu a bainar jama’a nan gaba kaɗan.
Majiyar na cewar, bayan kusan awanni 24 bayan kalaman nasa, wannan kisan gilla na kashe waɗannan yara ya afku.
Waɗannan yara biyu da aka yi wa kisan gilla sun haɗa da Mama yarinya ’yar shekara 14 da Anwar ɗan wata 28 waɗanda daga farko aka neme su aka rasa waɗanda ana zargin an sace su ne a ƙofar gidansu, amma kwanaki kaɗan sai aka tsinci gawarwakin yaran da sanyin safiyar yau Alhamis a boot ɗin motarsa.
Kwamishinan ’yan sandan Jihar Borno, Nazir Abdulmajid wanda ya tabbatar da faruwar lamarin, ya ce an gano gawarwakin yaran a cikin boot ɗin a wata tsohuwar motarsa da aka kulle a harabar gidan.
A yanzu dai haka an baza jami’an rundunar ’yan sanda inda lamarin ya faru kuma an ɗauki hotuna, kuma an kai gawarwakin su zuwa asibitin koyarwa na Jami’ar Maiduguri domin a tantance ko an yi garkuwa da su ne aka kashe su ko kuma sun shiga boot ne suka kulle kansu har suka mutu.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Babagana Umara Zulum
এছাড়াও পড়ুন:
Gwamna Radda Ya Sanya Hannu Kan Kasafin 2026 Ya Zama Doka
Daga Isma’il Adamu
Gwamna Dikko Radda na Jihar Katsina ya sanya hannu kan kudirin kasafin kudin jihar na 2026 na Naira Biliyan 897, makonni uku bayan gabatar da shi a gaban majalisar dokokin jihar.
Yayin rattaba hannu a Fadar Gwamnati da ke Katsina, a gaban ‘yan majalisar dokokin jihar, gwamnan ya jinjinawa majalisar bisa gaggawar amincewa da kasafin, tare da tabbatar da cewa za a aiwatar da shi yadda ya dace.
Ya bayyana cewa kashi 82 cikin ɗari na kasafin an ware shi ne ga manyon ayyuka(capital expenditure), yayin da kashi 18 cikin ɗari aka ware ga ayyukan yau da kullum(recurrent expenditure), rabo wanda ya ce ya fi abin da doka ta baya ta tanada, wadda ke bukatar kada kudaden gudanarwa su haura kashi 30 cikin ɗari.
Gwamna Radda, wanda ya bayyana kasafin a matsayin “kasafin jama’a,” ya ce an tsara shi ne daga shawarwarin da aka tattara a tarukan jin ra’ayin jama’a da aka gudanar a fadin kananan hukumomi 34 na jihar.
Yayin da yake jinjinawa ‘yan majalisar dokokin jihar bisa kyakkyawar alakar aiki da suke da ita da bangaren zartarwa, gwamnan ya bukaci kwamitocin majalisar su gudanar da aikinsu na sa ido don tabbatar da cewa an aiwatar da kasafin yadda ya kamata.
Tun da farko, yayin mika kudirin kasafin domin rattaba hannu, Shugaban Majalisar Dokokin Jihar, Alhaji Nasir Yahaya, ya ce ‘yan majalisar sun duba tare da amince da kasafin cikin makonni uku, lamarin da ya sanya Katsina ta zama jihar farko da ta samu dokar kasafin kudin shekara ta 2026.