Aminiya:
2025-11-27@21:57:42 GMT

An ceto mutum 5 bayan gini ya rufta da su a Legas

Published: 25th, September 2025 GMT

Wani gini mai hawa biyu da ake ginawa ya rufta da safiyar ranar Alhamis a yankin Alimosho da ke Jihar Lagos, inda ya danne ma’aikata da dama.

Ginin, wanda yake a titin Modupeola kusa da madakatar mota ta Mangoro, ya rushe da misalin ƙarfe 4 na safe.

Muhimman abubuwa 7 da Najeriya ta fada yayin jawabinta a taron MDD FBI ta sanya la’adar N15m kan dan Najeriyar da take nema ruwa a jallo

Mutane da jami’an agajin gaggawa sun garzaya wajen domin ceto waɗanda suka maƙale a ƙarƙashin baraguzan ginin.

Bayan wani lokaci, an ceto maza biyar da ransu, sannan an garzaya da su asibiti.

Ɗaya daga cikinsu, mai shekara 44 wanda ya samu munanan raunuka, an tura shi zuwa LASUTH.

Gwamnatin Jihar Legas ta fara bincike don gano musabbabin rushewar ginin, tare da yin alƙawarin ɗaukar matakan da suka dace domin hana aukuwar irin wannan a nan gaba.

Shugabar Hukumar Kashe Gobara na Jihar Legas, Margaret Adeseye, ta ce sun samu kiran gaggawa da misalin ƙarfe 5:39 na safe kuma suka isa wajen da misalin 6 6:24 na safe.

Ta bayyana cewa ainahin ginin tsarin ƙasa ne, amma ana ƙoƙarin mayar da shi bene mai hawa biyu.

“An ceto ma’aikatan da ke ginin maza guda biyar duk sun samu rauni, babu wanda ya rasu,” in ji ta.

Jami’an kashe gobara daga Ikeja da Agege sun isa wajen domin gudanar da aikin ceto.

উৎস: Aminiya

এছাড়াও পড়ুন:

An ceto ’yan mata 24 d aka yi garkuwa da su a makaranta a Kebbi

An ceto ’yan matan nan 24 da ’yan bindiga suka yi garkuwa da su a Makarantar sakandaren Gwamnati ta GGCSS da ke yankin Maga da ke Jihar Kebbi.

Gwamnan jihar Kebbi Nasiru Idiris a taron manema labarai a ranar Talata fadar gwamnatin jihar ya tabbatar da an karɓo ɗalibban da aka sace a farkon makon nan.

Ya ce “an karɓo ɗiyanmu ’yan makaranta waɗanda aka yi garkuwa da su a Maga. Shugaban ƙasa ya baiwa jami’an tsaro umarni a tafi a gano inda yaran suke kuma a karɓo su muna tabbatar wa uwayen yara da al’ummar Kebbi yara sun dawo.

“Muna godiya ga shugaban ƙasa da jami’an tsaro musamman sojoji da ’yan sanda da Sibil difens da sauransu da suka tsaya aka karɓo yaran nan cikin ƙoshin lafiya.

“Mu gwamnatin Kebbi ba mu biya kuɗin fansa don a saki yaran ba, a binciken da muka yi ba wanda ya biya kuɗin fansar yaran, mu ba mu ba da ko kwabo ba,” a cewar Gwamnan Idiris.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Gwamnati Za Ta Biya Wasu Kudaden Ariyas Ga Masu Fensho Wannan Wata
  • Tinubu ya ayyana dokar ta-ɓaci kan matsalar tsaro
  • ’Yan bindiga sun sake kai hari a Kwara, sun sace mutum 11
  • An ceto ’yan mata 24 d aka yi garkuwa da su a makaranta a Kebbi
  • Tinubu Ya Nuna Farin Cikinsa Bisa Bayyanar Daliban Kebbi, Ya Bukaci a Ceto Sauran
  • Kano Pillars ta kawo ƙarshen wasanni 8 ba tare da nasara ba
  • An buɗe wasu makarantu domin ci gaba da jarawaba a Katsina
  • Yan Majalisar Kudu Sun Nemi Gafarar Tinubu Ga Nnamdi Kanu
  • ’Yan bindiga sun sace mutum 8 a Kano
  • ’Yan Majalisar Kudu sun roƙi Tinubu ya yi wa Nnamdi Kanu Afuwa