NAJERIYA A YAU: Dalilan Da Suke Sa Dalibai Cin NECO Fiye da WAEC
Published: 25th, September 2025 GMT
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba
Yayin da dalibaI da dama da suka rubuta jarrabawar kammala karatun sakandare suka fitar da zaton samun gurbi a makarantun gaba a bana bisa la’akari da sakamakon WAEC, sai ga sakamakon NECO ya taho musu da sabon albishiri.
Yayin da sakamakon WAEC ya bar baya da kura, inda galibi suka kasa samun makin da ake bukata a mafi karancin adadin darussa, na NECO ya yi nuni da cewa galibi sun tsallake wannan siratsi.
Ko wadanne dalilai ne sukan sa wasu dalibai faduwa jarrabawar WAEC amma su samu ta NECO? NAJERIYA A YAU: Abin Da Doka Ya Ce Kan Kisan Jami’an ‘Yan Sanda DAGA LARABA: Abin Da Ya Sa ’Yan Najeriya Ba Sa Cin Kifi Yadda Ya Kamata
Wannan shi ne batun da shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi nazari a kai.
Domin sauke shirin, latsa nan
উৎস: Aminiya
এছাড়াও পড়ুন:
Yaushe Lamine Yamal Zai Lashe Kyautar Ballon d’Or?
Sai dai duk da cewa Ousmane Dembele na kungiyar kwallon kafa ta PSG ne ya lashe gasar- Yamal ya samu nasarar kyautar gwarzon matashin dan wasa na Ballon d’Or karo na biyu a jere.
Lamine Yamal, ya kasance daya daga cikin fitattun ‘yanwasa mafiya farin jini tsakanin masoya kwallon kafa, musamman ma matasa saboda karancin shekarunsa da kuma yadda yake buga wasa cikin raha.
Shekara da shekaru, duniya ta dauka cewa zama fitacce a fagen kwallon kafa na bukatar jajircewa da sadaukarwa. Saboda kafin dan wasa ya iya lashe wannan kyauta sai ya yi aiki tukuru.
Sai dai duk da nuna kuruciyarsa, hakan bai hana Yamal cimma burinsa a fagen kwallon kafa ba. A baya ya bayyana cewa: yana da burin samun Ballon d’Or masu yawa idan ya samu dama.
Matasa da dama sun so Yamal ya lashe Ballon d’Or a wannan shekara, musamman irin kokarin da ya yi a bara, da kuma lashe kyautar gwarzon matashin danwasa da ya yi a bara. Kuma rashin samun kyautar ba ta yi wa matasa da dama dadi ba.
Ana ganin samun nasara a tawagar ‘yan wasan kasar Sifaniya zai fi ba shi damar lashe kyautar fiye da kungiyarsa ta Barcelona, amma idan har Barcelona ta iya lashe gasar cin kofin zakarun turai tabbas zai iya lashewa.
Amma kuma akan fifita nasarar da dan wasa ya yi a kasarsa fiye da kungiyar da yake bugawa wasa, kuma a bayyane take Kofin Duniya na daya daga cikin manyan abubuwan da zai sa mutum ya lashe kyautar.
Saboda haka idan har Sifaniya ta lashe kofin duniya a shekara mai zuwa ta 2026, Yamal zai iya samun kyautar Ballon d’Or. Kasancewar a yanzu yadda yake da cikakken gurbi a tawagar kasar, babu yadda za a yi Sifaniya ta ci kofin ba tare da kwallayensa ba.
ShareTweetSendShare MASU ALAKA