2025-09-24@09:57:14 GMT
إجمالي نتائج البحث: 6312

«yan Najeriya»:

    Kamfanin GTCO, mamallakin bankin GT, ya bayyana samun ribar Naira biliyan 601 a watanni shida na farkon shekarar 2025. Sai dai bankin ya ce duk da haka ribar tasa raguwa ta yi a kan ta Naira tiriliyan daya da ya ci a farkon shekarar da ta gabata. Kotun Indiya ta daure dan Najeriya shekara 10...
    Jagoran juyin juya halin Musulunci a cikin jawabinsa ya bayyana cewa: Dangane da hadin kan al’ummar Iran, batu na farko shi ne cewa a lokacin yakin kwanaki goma sha biyu, hadin kai da hadin kan al’ummar Iran ya sanya makiya kunya. Jagoran ya jaddada cewa tun tsakiyar tsakiyar yakin makiya sun gane cewa ba za...
    Ali Larijani, sakataren majalisar koli ta tsaron kasa, ya rubuta a daren Talata a wani sako da ya wallafa a dandalin sada zumunta na X:“Da farko dai Amurka ta fice daga JCPOA, sannan Turai ta kasa cika alkawuran da ta dauka, a karshe ma sun kai harin bama-bamai, yanzu haka jam’iyyu suna yin kamar su...
    Rundunar sojojin ta ce waɗannan hare-hare sun nuna ƙudirin gwamnati wajen yaƙi da rashin tsaro a faɗin ƙasar nan. Ta kuma tabbatar wa ‘yan ƙasa cewa za ta ci gaba da ƙoƙari domin kare al’umma daga ‘yan ta’adda da sauran masu laifi. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da...
    Ministan harkokin wajen kasar Iran ya tattauna da fira ministan Norway game da alakar kasashen biyu da ci gaban kasa da kasa Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araqchi wanda ke ziyara a birnin New York domin halartar taron shekara shekara na Majalisar Dinkin Duniya ya gana da fira ministan kasar Norway Jonas Gahr Støre. A...
    Babban daraktan hukumar kula da makamashin nukiliya ta kasa da kasa ya sanar da cewa: Masu binciken hukumarsa suna kan hanyarsu ta zuwa Iran Babban daraktan hukumar kula da makamashin nukiliya ta kasa da kasa Rafael Grossi ya bayyana cewa: Masu sa ido na hukumar IAEA na kan hanyarsu ta zuwa Iran. Rafael Grossi ya...
    Kasashen Burkina Faso, Nijar, da Mali sun fice daga kotun hukunta manyan laifuka ta duniya Kasashen Burkina Faso, Mali, da Nijar sun sanar a cikin wata sanarwar hadin gwiwa da suka fitar na ficewa daga yarjejeniyar Rome ta kotun hukunta manyan laifuka ta duniya ICC. Sanarwar wadda wakilin gwamnati kuma ministan sadarwa na Burkina Faso,...
    Wata kotu ta musamman a Coimbatore da ke kasar Indiya, ta yanke wa wani dan Najeriya mai suna Samson Chukwunonso hukuncin daurin shekaru 10 a gidan yari kan laifin safarar miyagun kwayoyi. Jaridar Times of India ta ruwaito cewa lamarin ya faro tun a watan Yuli na shekarar 2012, lokacin da jami’an hukumar hana sha...
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Duk da amfanin kifi ga lafiyar jikin mutum da kuma samar da kudin shiga masana sun ce ba a amfani da shi yadda ya kamata a Najeriya.   Baya ga bai wa jiki lafiya, kifi  ka iya samar da kudaden shiga ga daidaikun ’yan Najeriya da ma kasar...
    A yau Talata, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya bukaci hada karfi da karfe wajen gina yankin Xinjiang ya zama mafi kyau a cikin tsarin zamanantar da kasar Sin. Ya bukaci hakan ne yayin da ya gana da wakilai daga dukkan kabilu da sauran fannonin rayuwar al’umma a yankin Xinjiang mai cin gashin kansa na...
      Gavi dai ba zai dawo ba sai a farkon shekarar 2026, shekarar da ake ganin kasar Sifaniya za ta kasance cikin kasashen da suka fi damar lashe gasar cin kofin duniya da za a buga a kasashen Amurka, Mexico da kuma Canada. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu...
    Rundunar ’yan sanda a Jihar Kano ta sanar da cafke wani mutum da ke yi mata sojan-gona yana yaudarar jama’a domin karɓar musu kuɗi. An cafke wanda ake zargin ne a ranar Lahadi, 21 ga Satumbar 2025 a yankin Kofar Dawanau, sanye da kayan ’yan sanda, wanda bayanai suka ce ya daɗe yana aika-aikar. An yi...
    Firaministan kasar Sin Li Qiang, ya isa birnin New York na Amurka da yammacin jiya Litinin, don halartar babban taron mahawara na MDD karo na 80. Yayin da yake birnin na New York, Li zai halarci wasu jerin ayyuka da Sin ta tsara, ciki har da taron manyan jami’ai game da shawarar tsarin shugabancin duniya,...
    Mataimakin shugaban ƙasar ya bayyana cewa tuni gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ta ɗauki manyan matakai na gyara tattalin arziki, ciki har da cire tallafin man fetur, haɗa farashin musayar kuɗi, da kuma sabunta tsarin haraji da kwastam.   Ya ƙara da cewa waɗannan sauye-sauye sun fara samar da yanayi mai kyau ga masu zuba jari,...
    Ya zuwa ranar 23 ga watan Satumba agogon Beijing, kasashe 152 cikin 193 na Majalisar Dinkin Duniya sun amince da Falasdinu a matsayin kasa. A cikin kasashe biyar masu kujerun dindindin a kwamitin sulhun MDD, Amurka ce kadai ba ta amince da kafuwar kasar Falasdinu ba. Wannan guguwar ta amincewa da kafuwar kasar Falasdinu ta...
    Wata Kotun Soji ta yanke wa wasu sojoji uku hukuncin ɗaurin rai da rai kan sayar da makamai da harsasai ba bisa ka’ida ba a Maiduguri, Jihar Borno. Kotun sojin ƙarƙashin jagorancin Birgediya-Janar Mohammed Abdullahi, ta bayyana cewa an yanke wa mutum uku daga cikin sojojin huɗu hukuncin ɗaurin rai da rai yayin da aka...
      Wannan ne dai karo na farko da adadin gejin kuɗin ruwa ya yi ƙasa, wato mafi ƙaranci a cikin shekaru biyar.   Gwamnan na CBN ya ce an yanke shawarar rage kuɗin ruwan ne domin ci gaba da bunkasuwar tattalin arzikin cikin gida (GDP), da karyewar hauhawar farashi, wanda tsawon watanni biyar kenan ana...
    Yarima mai jiran gado na Masarautar Saudiyya, Sheikh Muhammad bin Salman, ya jagoranci sallar jana’izar fitaccen malamin addini, Sheikh Abdulaziz bin Abdullah bin Muhammad Al-Sheikh. Shafin Inside Haramain ya ruwaito cewa an gudanar da jana’izar ce a Masallacin Imam Turki bin Abdullah da ke birnin Riyadh. CBN ya rage kuɗin ruwa zuwa kashi 27 cikin...
    Yawan tashoshin fasahar sadarwa ta 5G a kasar Sin ya kai kusan miliyan 4.65 a karshen watan Agusta, kamar yadda alkaluman mahukunta suka nuna a yau Talata. A cewar ma’aikatar masana’antu da fasahar sadarwa ta kasar Sin, adadin ya kai kashi 36.3 na adadin tashoshin sadarwar wayar hannu a fadin kasar baki daya. A halin...
    A yau talata da yamma ce aka yi jana’izar shahidan Bintijbail na kudancin kasar Lebanon, wanda HKI ta kaisu ga shahada a lokacinda ta cilla makamai masu linzami kan motar da take dauke da su a ranar Lahadin da ta gabata. Tashar talabijin ta Al-Manar ta kungiyar Hizbullah ta bayyana cewa, shahidan mutane 5 biyar...
    Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkiyan ya bayyana cewa dandalin jawabi a MDD wata dama ce ta kasashen duniya su bayyana ra’ayinsu kuma Iran zata bayyana ra’ayinta a gobe Laraba 23 ga watan Satumba na wannan shekara ta 2025. Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta nakalto shugaban yana fadar haka jim kadan fafin ya...
    Daya daga cikin shuwagabannin kungiyar yan ta’adda ta Deash kuma kungiya mafi kiyayya ga Amurka a fadin ta a yau ya kama hanya zuwa NewYork don gabatar da jawabin a babban zauren MDD a karon farko. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa, tun lokacinda tawagar Amurka ta ziyarci kasar Siriya bayan...
    Ana zargin wata matar aure, Rabi Nuhu da ke garin Magama Gumau a ƙaramar hukumar Toro ta Jihar Bauchi, da cin zarafin wata yarinya ’yar shekara biyar ta hanyar ƙone mata al’aura, saboda zargin tana yawan yin fitsarin kwance. Wakilinmu ya gano cewa yarinyar marainiya ce wadda mahaifiyarta ta rasu kusan shekara ɗaya da ta...
    Ana zargin wata matar aure, Rabi Nuhu da ke garin Magama Gumau a ƙaramar hukumar Toro ta Jihar Bauchi, da cin zarafin wata yarinya ’yar shekara biyar ta hanyar ƙone mata al’aura, saboda zargin tana yawan yin fitsarin kwance. Wakilinmu ya gano cewa yarinyar marainiya ce wadda mahaifiyarta ta rasu kusan shekara ɗaya da ta...
    A ranar Alhamis 25 ga watan nan, shugaban kasar Sin Xi Jinping zai halarci wani babban taro a birnin Urumqi, babban birnin yankin Xinjiang na Uygur mai cin gashin kansa, domin murnar cika shekaru 70 da kafuwar yankin. An shirya fara bikin da shugaba Xi zai halarta da karfe 10:30 na safiyar Alhamis, kuma babban...
    Kwamitin da ke kula da tsare-tsare da manufofin kuɗi na Babban Bankin Najeriya (CBN) ya zaftare maki 60 daga nauyin kuɗin ruwa da ke kan masu karɓar basussuka.  Wannan dai shi ne karo na farko cikin shekaru biyar da aka samu babban bankin ya yi rangwamin kuɗin ruwa a ƙasar. CBN ɗin ya ce kwamitin a...
    Haka kuma sun tabbatar da cewa manoma da suka koma gonakinsu kwanan nan sun samu kariya. Babu wanda aka sace ko ɗaya, yayin da jama’ar yankin ke ci gaba da zama lafiya. A ranar 19 ga watan Satumba, Birigediya Janar Ugochukwu Unachukwu, wanda shi ne muƙaddashin kwamandan rundunar sojojin 7 Division, ya kai ziyara Banki...
    An kashe wani ɗan sanda mai muƙamin Sajan a wani hari da ’yan bindiga suka kai wani shingen bincike, inda suka ɗauke bindigarsa bayan sun halaka shi a Jihar Taraba. Wata majiyar ta bayyana cewa lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 10 na dare a garin Tella, cikin Ƙaramar Hukumar Gassol, lokacin da ’yan...
    Wasu ’yan bindiga sun yi garkuwa da ɗan Majalisar Dokokin Jihar Filato, mai wakiltar Mazaɓar Pankshin ta Kudu, Laven Denty Jacob. A yammacin ranar Litinin aka yi garkuwa da shia gidansa da ke Anguwan Kagji, a Unguwar Dong, a Ƙaramar hukumar Jos ta Arewa. Wani na kusa da shi ya tabbatar wa manema labarai cewa...
    Allah Ya yi wa Babban Mai Ba da Fatawa na kasar Saudiyya, Sheikh Abdulaziz bin Abdullah bin Mohammed Al Al-Sheikh, rasuwa. Hukumomin ƙasar Saudiyya sun sanar da cewa Sheikh Abdulaziz bin Abdullah bin Mohammed Al Al-Sheikh ya rasu yana da shekara 82 a duniya. Fadar Masarautar ƙasar da kuma Shugaban Majalisar Malaman Masallata Haraman Makkah...
    A daidai lokacin da aka shiga cikin kwanaki na 718 da fara yakin Gaza, HKI tana ci gaba da yi wa Falasdinawa kisan kiyashi da makamai da kuma yunwa. Majiyar Falasdinawa ta tabbatar da cewa daga safiyar yau Talata zuwa tsakiyar ranaFalasdinawa masu yawa sun yi shahada. Majiyar dai ta ce, jiragen yakin ‘yan sahayoniyar...
    Ya ce Kano na cikin hatsari saboda cunkoson jama’a da kuma zirga-zirgar mutane daga wurare daban-daban. KNCDC ta gudanar da cikakken bincike a Ungogo, inda aka duba unguwar da marar lafiyan yake da kuma asibitocin da ya ziyarta. Duk wanda aka bincika yana cikin ƙoshin lafiya kuma babu wanda ya kamu da cutar. Farfesa Abbas...
    Hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) ta yi wa tsohon Ministan Shari’a kuma Antoni-Janar na Gwamnatin Tarayya, Abubakar Malami, tambayoyi a kan harin da aka kai wa ayarin motocinsa a Jihar Kebbi. An gudanar da tambayoyin ne a ofishin hukumar na Birnin Kebbi a ranar Litinin, inda Malami ya bayyana cewa an yi masa tambayoyin...
    Ya ce Kano na cikin hatsari saboda cunkoson jama’a da kuma zirga-zirgar mutane daga wurare daban-daban. KNCDC ta gudanar da cikakken bincike a Ungogo, inda aka duba unguwar da marar lafiyan yake da kuma asibitocin da ya ziyarta. Duk wanda aka bincika yana cikin ƙoshin lafiya kuma babu wanda ya kamu da cutar. Farfesa Abbas...
    An bayyana dan wasan a matsayin wanda ya lashe kyautar ne a bikin da aka gudanar ranar Litinin 22 ga watan Satumban 2025 a dakin taro na Theatre du Chatelet da ke birnin Paris a kasar Faransa. Ballon d’Or kyauta ce da akan bai wa dan wasan da ya nuna gwaninta a kowace shekara, inda...
    Rundunar ’Yan sandan Jihar Kebbi ta cafke wasu mutum huɗu a yankin Kamba da ke jihar, bisa zargin su da shigar da babura uku da suka saya daga Jamhuriyar Benin domin kai wa kungiyar ta’addanci ta Lakurawa. Haka kuma an kama wani Mubarak Ladan bayan ya yi tayin cin hancin naira dubu dari shida (₦600,000)...
    An ba shi kyautar ne a daren ranar Litinin a Theatre du Chatelet da ke birnin Paris, inda ya doke matashin Barcelona, Lamine Yamal, wanda ya lashe kyautar matashin ɗan wasa mafi ƙwazo. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin...
    Hukumar Ƙididdiga a Najeriya, NBS ta ce arzikin cikin gida da kasar ke samu ya karu da kashi 4.23 cikin 100 a rubu’i na biyu na shekarar 2025 da muke ciki. Sabbin alkaluman da hukumar ta fitar sun nuna cewa an samu karin kashi 3.48 idan aka kwatanta da irin wannan lokacin a 2024, lamarin...
    Mohammad Eslami mataimakin shugaban kasar Iran kuma shugaban hukumar makamashin nukiliya na kasar Iran ya bayyana cewa Tehran da mosko  za su rattaba hannu kan wata sabuwar yarjejeniya akwanaki masu zuwa ta gina tashar nukiliya domin kara fadada alakarsu a wannan bangaren na makamashi. Wannan sanarwar tana zuwa ne adaidai lokacin da iran ke fuskantar...
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Kisan jami’an tsaro na cigaba da zama ruwan dare a Najeriya, lamarin da ya daɗe yana tayar da hankali, amma a ‘yan kwanakin nan abin ya ƙara muni.   Misali, kwanan nan a an kashe wasu jami’an ‘yan sanda a kananan hukumomin Katsina-Ala da Ukum a jihar Benue, inda...
    Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Guo Jiakun ya bayyana a yau 22 ga wannan wata cewa, a yayin da ake raya duniya bisa tsarin bai daya, musayar kwararru a tsakanin kasa da kasa ta sa kaimi ga raya fasahohi da tattalin arzikin kasashen duniya. Kasar Sin tana maraba da kwararru daga bangarori da sana’o’i...
      29. Florian Wirtz (Liverpool)   28. Virgil van Dijk (Liverpool)   27. Declan Rice (Arsenal)   26. Erling Haaland (Man City)   25. Denzel Dumfries (Inter Milan)   24. Fabian Ruiz (PSG)   23. Jude Bellingham (Real Madrid)   22. Alexis Mac Allister (Liverpool)   21. Serhou Guirassy (Borussia Dortmund)   20. Lautaro Martinez...
    Ɗan wasan gaban PSG da Faransa, Ousmane Dembélé ya lashe kyautar Ballon d’Or ta bana. Balon d’or dai ita ce lambar yabo mafi girma a duniyar ƙwallon kafa wacce ake bai wa gwarzon ɗan wasa na shekara.
    Faransa ta bi sahun Birtaniya, Australia da Canada da sauran ƙasashen duniya sama da 140 da suka amince da Falasɗinu a matsayin ƙasa mai ’yanci. Shugaban Faransa, Emmanuel Macron ne ya tabbatar da amincewar gwamnatinsa na kafa ƙasar Falasdinu a hukumance. Tattalin arzikin Najeriya ya ƙara haɓaka — NBS NEF za ta ƙaddamar da taron...
    Hukumar Ƙididdigar a Najeriya, NBS ta ce arzikin cikin gida da ƙasar ke samu ya ƙaru da kashi 4.23 cikin 100 a rubu’i na biyu na shekarar 2025 da muke ciki. Sabbin alƙaluman da hukumar ta fitar sun nuna cewa an samu ƙarin kashi 3.48, idan aka kwatanta da daidai wannan lokacin a 2024, lamarin...
    Sanarwar ta ƙara da cewa, Gwamna Lawal ya jaddada cewa tsarin dimokuraɗiyyar Kanada, ƙarfafan tattalin arziƙi, hakar ma’adinai ta hanyar da ta dace, da kuma harkokin kasuwanci masu zaman kansu masu kirkire-kirkire sun sanya ta zama abokiyar haɗin guiwar da ta ta dace ga Afrika.   Ya ce, “Idan Afrika za ta cika burinta gaba...
    Kungiyar Dattawan Arewa (NEF) ta ce a karon farko za ta shirya taron zuba jari da samar da masana’antu na Arewacin Najeriya, wanda aka shirya gudanarwa a ranakun 29 da 30 ga watan Satumba a Abuja. Taron wanda aka shirya tare da hadin gwiwar jihohin arewa 19 da kuma kamfanin raya yankin – NNDC, na...
    Dangane da halin da ake ciki game da rikicin Falasdinu da Isra’ila, mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Guo Jiakun ya bayyana a yau Litinin 22 ga wata cewa, karfin soja ba zai iya samar da zaman lafiya ba, kuma tashin hankali ba zai iya samar da tsaro ba. Kasar Sin tana...
    Tawagar jami’an diflomasiyyan Falasɗinu ta gudanar da bikin ɗaga tutar ƙasar a Litinin ɗin nan a birnin Landan kamar yadda kafar labarai ta DW ta ruwaito. Bikin ɗaga tutar na zuwa ne kwana guda bayan da Birtaniya ta amince da Falasɗinu a matsayin kasa mai cin gashin kanta. CAC ta soma yi wa kamfanoni rijista...
    Kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas ta yi maraba da amincewar da kasashen Birtaniya, Australia, da Canada suka yi wa kasar Falasdinu, tana mai bayyana hakan a matsayin wani muhimmin mataki na tabbatar da hakkin al’ummar Palasdinu na kasarsu. A cikin wata sanarwa da ta fitar jiya Lahadi, kungiyar ta yi kira ga kasashen duniya da...