HausaTv:
2025-11-01@21:56:09 GMT

Kasashen Larabawa da na Musulmi na taron gaggawa kan harin Isra’ila a Qatar

Published: 15th, September 2025 GMT

Jami’an kasashen larabawa da na Musulmi sun bukaci daukar kwararan matakai kan Isra’ila bayan harin da ta kai a birnin Doha, inda suka bayyana harin a matsayin “na matsorata, da muggan laifuka.”

Da yake jawabi a gun taron ministocin harkokin wajen kasashen a birnin Doha, Sakatare-Janar na kungiyar kasashen Larabawa Ahmed Aboul Gheit ya ce harin, ha’inci ne da wauta.

Sakatare-Janar na Kungiyar ya bayyana “cikakken goyon baya” ga Qatar bayan abin da ya kira “cin zarafin Isra’ila”, yana mai jaddada cewa dole ne kasashen duniya su dauki kwakkwaran mataki kan Tel Aviv.

Shi ma da yake jawabi a taron share fagen kasashen musulmin da na Larabawa, firaministan Qatar kuma ministan harkokin wajen kasar Sheikh Mohammed bin Abdulrahman Al Thani ya yi tir da harin da ya danganta da na “ta’addancin kasa” da kuma keta duk wani yunkuri na shiga tsakani.”

Sheikh Abdulrahman Al Thani ya bukaci kasashen duniya da su daina yin Magana mai tamkar harshen damo, su kuma hukunta Isra’ila saboda “laifin” da ta aikata.

Ya yi wannan jawabi ne a wani taron share fage da aka yi a jajibirin taron gaggawa na shugabannin kasashen Larabawa da na Musulunci da Qatar ta shirya bayan da Isra’ila ta kai wani hari irinsa na farko kan kasar a kan shugabannin Hamas a Doha. Yau Litinin ne shugabannin kasashen na Larabawa da na Musulmi zasu hadu a birnin Doha domin tattauna batun.

Share

0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Hamas ta bukaci kasashen musulmi da na Larabawa su dauki mataki mai tsari kan Isra’ila September 15, 2025 Rabin Sojojin Isra’ila da suka ji rauni a yakin Gaza na fama da ciwon damuwa September 15, 2025 Sudan ta soki takunkuman da Amurka ta kakaba mata September 15, 2025 Dakarun Sojin Yamen Sun Kai Hari Kan Filin Jirgin Saman Ramon Na Isra’ila. September 14, 2025 Isra’ila Za ta Gamu Da Mummunar Martani Idan Tayi Gigin Afkawa Iran September 14, 2025 Ministocin Harkokin Wajen Kasashen Larabawa Da Na Musulmi Sun Fara Taro A Qatar. September 14, 2025 Gwamnatin Najeriya Ta Sanar Da Sabon Sharadi Na Bude Asusun Banki September 14, 2025 An Zabi Issa Tchiroma A Matsayin Dan Takara Daya Tilo A Kamaru September 14, 2025 Kasar Iran Ta Yi Fatali Da Zarge-Zargen Da Kungiyar G7 Da Kawayenta Suka Yi Kanta September 14, 2025 Iran Ta Bayyana Shirinta Na Halartar Taron Shekara-Shekara Na Hukumar Makamashin Nukiliya September 14, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci About Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS News Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Explore Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS

উৎস: HausaTv

কীওয়ার্ড: kasashen Larabawa da na Larabawa da na Musulmi

এছাড়াও পড়ুন:

Xi Jinping: Sin Da Amurka Za Su Iya Hada Kai Don Sauke Nauyin Dake Wuyansu Na Manyan Kasashe Da Daukar Ainihin Matakai

 

Xi ya kuma bayyana cewa, saboda bambancin yanayin kasashen Sin da Amurka, ba makawa akwai wasu sabanin ra’ayi, amma baya ga kalubale da takara, ya kamata shugabannin biyu su rike shugabanci, da kuma samar da alkibla mai dacewa, don ba da damar bunkasa dangantakar Sin da Amurka ta ci gaba da tafiya cikin kwanciyar hankali.

 

A nasa bangare, Trump ya ce, yana farin ciki matuka bisa haduwa da dadadden abokinsa. Ya ce, “Za mu tattauna da mai girma shugaban kasar Sin Xi Jinping. Ina da imanin cewa, mun riga mun kai ga cimma matsaya daya, kuma za mu cimma karin matsaya a nan gaba. Xi Jinping wani sahihin shugaba ne mai kima.”

 

Ya kuma ce, “Ba shakka kasashen biyu za su kafa nagartacciyar hulda ta dogon lokaci, ina kuma farin cikin hakan tare da shugaba Xi.”

 

Shugabannin biyu sun shafe sa’a 1 da mintuna 40 suna tattaunwa.

 

A wannan rana kuma, shugaban kasar Xi Jinping ya isa kasar Korea ta Kudu, domin halartar taron kwarya-kwarya na shugabannin kungiyar raya tattalin arzikin kasashen Asia da Pasifik (APEC) karo na 32, bisa gayyatar da shugaban kasar Korea ta Kudu Lee Jae-myung ya yi masa.(Amina Xu)

ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Bai Kamata Gwamnati Ta Ke Ciyo Bashi Bayan Cire Tallafin Man Fetur Ba – Sanusi II October 30, 2025 Manyan Labarai Atiku Ya Soki Gwamnatin Tinubu Kan Sauya Sunayen Waɗanda Aka Yi Wa Afuwa October 30, 2025 Daga Birnin Sin Sakamakon Nazarin CGTN Ya Yabawa Gudunmuwar Sin Ga Dunkulewar Yankin Asiya Da Pasifik October 29, 2025

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • HKI Na Ci Gaba Keta Yarjejeniyar Dakatar Da Bude Wuta A Gaza Inda Take Kashe Falasdinawa
  • Kasashen Pakistan Da Afghanistan Sun Tsawaita Yarjejeniyar Dakatar Da Bude Wuta
  • Sudan Ta Yi Kira Ga Kwamitin Tsaro Da Ya Ayyana RSF A Matsayin Kungiyar ‘Yan Ta’adda
  • Shugaban Lebanon Ya Umarci Sojoji Da Su Fuskanci Kutsen Na Isra’ila A Kudancin Kasar
  • Shugaban Lebanon Ya Umarci Sojoji Da Su Fuskanci Duk Wani Kutse Na Isra’ila A Kudancin Kasar
  • Isra’ila ta amince da fadada matsugunai a Yammacin Kogin Jordan
  • Gaza: hare-haren Isra’ila sun kashe mutane 100 Cikin Kwanaki Biyu
  • Sudan : Kasashen duniya na Allah wadai da cin zarafi a lokacin kama El-Fasher
  • Kungiyar Rapid Support Forces Ta Sanar Da Kafa Kwamitin Bincike Kan Cin Zarafin Al’umma A El Fasher
  • Xi Jinping: Sin Da Amurka Za Su Iya Hada Kai Don Sauke Nauyin Dake Wuyansu Na Manyan Kasashe Da Daukar Ainihin Matakai