Kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas ta yi kakkausar suka ga harin da Isra’ila ta kai kan Qatar a baya-bayan nan, inda ta bukaci kasashen Larabawa da na musulmi da su dauki matsaya daya kan matakan wuce gona da iri na gwamnatin mamayar.

Basem Naim, mamba a ofishin siyasa na kungiyar Hamas,ne  ya yi wannan kiran a cikin wata sanarwa a ranar Lahadi, yayin da ministocin harkokin wajen kasashen Larabawa da na kasashen musulmi suka halarci taron gaggawa na Doha, domin tattauna harin da Isra’ila ta kai kan shugabannin Hamas a kasar Qatar.

Babban jami’in na Hamas ya yi kira ga shugabannin yankin da ke halartar taron da su mayar da Isra’ila saniyar ware a siyasance da ta fuskar tattalin arziki da kuma gurfanar da jami’an Isra’ila a kotunan duniya domin kawo karshen yakin kisan kare dangi a Gaza.

Naim ya kuma jaddada cewa, harin da Isra’ila ta kai kan tawagar Hamas a birnin Doha, ya zo ne a daidai lokacin da tawagar ke tantance wata sabuwar shawarar tsagaita bude wuta a Gaza.

“Mun nuna sassauci mafi girma na kawo karshen kisan kiyashin da ake yi a Gaza, amma sojojin mamaya ne, ta hanyar amfani da kisa da kuma sanya sharuddan nasu, ke kawo cikas ga duk wata yarjejeniya da za a iya cimma.”

Daga karshe ya bayyana cewa kungiyar Hamas tana sa ran taron zai dauki matsaya guda daya mai ma’ana tsakanin Larabawa da musulmi, da suka hada da tsagaita bude wuta nan take da kawo karshen yakin Gaza, da dage shingen da aka yi, da yanke duk wata alaka da Isra’ila, da gurfanar da isra’ila kan laifuffukan da ta aikata, da samar da falasdinu mai  ‘yancin cin gashin kai, da Al-Quds a matsayin babban birninta, da kuma tabbatar da ‘yancin komawar ‘yan gudun hijira.

Share

0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Rabin Sojojin Isra’ila da suka ji rauni a yakin Gaza na fama da ciwon damuwa September 15, 2025 Sudan ta soki takunkuman da Amurka ta kakaba mata September 15, 2025 Dakarun Sojin Yamen Sun Kai Hari Kan Filin Jirgin Saman Ramon Na Isra’ila. September 14, 2025 Isra’ila Za ta Gamu Da Mummunar Martani Idan Tayi Gigin Afkawa Iran September 14, 2025 Ministocin Harkokin Wajen Kasashen Larabawa Da Na Musulmi Sun Fara Taro A Qatar. September 14, 2025 Gwamnatin Najeriya Ta Sanar Da Sabon Sharadi Na Bude Asusun Banki September 14, 2025 An Zabi Issa Tchiroma A Matsayin Dan Takara Daya Tilo A Kamaru September 14, 2025 Kasar Iran Ta Yi Fatali Da Zarge-Zargen Da Kungiyar G7 Da Kawayenta Suka Yi Kanta September 14, 2025 Iran Ta Bayyana Shirinta Na Halartar Taron Shekara-Shekara Na Hukumar Makamashin Nukiliya September 14, 2025 Jamhuriyar Musulunci Ta Iran Ta Bayyana Rashin Halarta Tawagarta A Kada Kuri’a Kan Batun Falasdinu   September 14, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci About Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS News Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Explore Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS

উৎস: HausaTv

কীওয়ার্ড: da Isra ila Larabawa da

এছাড়াও পড়ুন:

Sudan : Kasashen duniya na Allah wadai da cin zarafi a lokacin kama El-Fasher

Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya ya yi Allah wadai da harin da aka kai wa garin El-Fasher da ke Darfur a ranar Alhamis, da kuma mummunan tasirin da ya yi ga fararen hula.

A cikin sanarwar da ya fitar, kwamitin ya nuna matukar damuwarsa game da karuwar tashin hankalin da ke faruwa a El-Fasher da kewaye, wanda Rundunar Taimakon Gaggawa (RSF) ta kwace iko da shi kwanan nan, kuma ya yi Allah wadai da ta’addancin da ake zargin dakarun RSF sun yi wa fararen hula, ciki har da kisan gilla da tsare mutane ba bisa ka’ida ba.

Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta ce ta “firgita da rahotannin kisan sama da marasa lafiya 460 da abokan aikinsu a asibitin haihuwa na El-Fasher a Sudan.”

A cikin wani bidiyo da aka fitar a ranar Laraba a shafukan sada zumunta, Janar Hemedti ya amince cewa sojojinsa sun aikata cin zarafi.

Da yake magana daga wani wuri da ba a bayyana ba, janar din, sanye da kayan soja, cewa “Na lura da keta haddi a El-Fasher,” inda ya sanar da kafa kwamitin bincike nan take.

Ya yi alƙawarin cewa za a kama duk wani soja da aka samu da laifin cin zarafi kuma a gurfanar da shi a gaban kotu.

Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya António Guterres ya bukaci bangarorin da su hanzarta shiga tattaunawa a cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na sada zumunta.

kungiyar likitocin Sudan, ta ce “Adadin wadanda suka mutu ya wuce 2,000 a cikin kwanaki biyu na farko bayan da RSF ta shiga El-Fasher.

Share

0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Iran Ta Jaddada Bin Hanyar Diflomasiya Ko Da A Lokacin Yaki Ne Amma Ba Zata Amince Da Bin Umarni Ba October 30, 2025 Qalibaf: Amurka Tana Yaudarar Duniya Da Zaman Lafiya, Alhalin Tana Ci Gaba Da Kai Harin Wuce Gona Da Iri October 30, 2025 Ci Gaba Da Killace Gaza Bayan Tsagaita Bude Wuta Ya Janyo Mutuwar Mutane 1000 A Yankin October 30, 2025 Kungiyar Rapid Support Forces Ta Sanar Da Kafa Kwamitin Bincike Kan Cin Zarafin Al’umma A El Fasher October 30, 2025 An Kafa Dokar Ta Baci A Darul-Salam Saboda Tarzoman Zaben Shugaban Kasa A Tanzania October 30, 2025 Rasha Da Amurka Sun Sake Dawo Da Gwaje-gwajen Makaman Nukiliya October 30, 2025 Kasar Czech Ta Hana Wa Wani Sojan HKI Shiga Kasar Bisa Gargadin  Faransa October 30, 2025  Sojojin HKI Sun Kutsa Kudancin Lebanon October 30, 2025 Adadin Falasdinawan Da Su Ka Yi Shahada A Cikin Sa’o’i 24 Sun Haura 100 October 30, 2025 Amurka Ta Hana Marubuci Dan Nigeria Wole Soyinka Izinin Shiga Amurka October 30, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci About Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS News Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Explore Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Amurka : zamu dauki matakin soja idan Najeriya ta gaza kawo karshen kashe Kiristoci
  • Hamas ta musanta zargin Amurka na cewa tana sace kayan agaji a Gaza
  • Isra’ila Ta Kashe Mutane 4 Tare Da Jikkata Wasu Guda 3 A Kudancin Labanon
  • Iran Ta Gargadi Isra’ila Kuma Tasha Alwashin Kare Shirinta Na Nukiliya
  • Kasashen Pakistan Da Afghanistan Sun Tsawaita Yarjejeniyar Dakatar Da Bude Wuta
  • Shugaban Lebanon Ya Umarci Sojoji Da Su Fuskanci Kutsen Na Isra’ila A Kudancin Kasar
  • Shugaban Lebanon Ya Umarci Sojoji Da Su Fuskanci Duk Wani Kutse Na Isra’ila A Kudancin Kasar
  • Isra’ila ta amince da fadada matsugunai a Yammacin Kogin Jordan
  • Gaza: hare-haren Isra’ila sun kashe mutane 100 Cikin Kwanaki Biyu
  • Sudan : Kasashen duniya na Allah wadai da cin zarafi a lokacin kama El-Fasher