A yau Lahadi ne wakilan kasashen Sin da na Amurka, sun isa birnin Madrid na kasar Sifaniya, domin gudanar da tattaunawa game da batutuwan tattalin arziki da cinikayya.

Cikin kwanaki masu zuwa, sassan biyu za su zanta game da batutuwan da suka hada da matakin Amurka na kakaba haraji, da karya ka’idar kayyade fitar da hajoji, da batun dandalin TikTok, kamar dai yadda kakakin ma’aikatar cinikayyar Sin ya tabbatar a ranar Jumma’a.

(Saminu Alhassan)

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

উৎস: Leadership News Hausa

এছাড়াও পড়ুন:

Jihar Jigawa Ce Ta Fara Biyan Kudaden Kujerun Aikin Hajjin 2026- NAHCON

Hukumar Aikin Hajji ta Kasa NAHCON ta yi kira ga jihohin kasar nan da su yi koyi da Gwamna Umar Namadi na Jihar Jigawa wajen tare kujerun aikin hajji domin baiwa Maniyatan su damar sauke farali.

Kwamishina a hukumar mai kula da shiyyar arewa maso yamma , Sheikh Muhammad Bin Usman yayi wannan kiran a lokacin da ya kai ziyarar aiki a Dutse, babban birnin Jihar.

Sheikh Muhammad Bin Usman yayi bayanin cewar, ya zama wajibi ga sauran hukumomin Alhazan kasar nan da su yi koyi da Gwamna Umar Namadi wajen bai wa hukumomin Alhazai bashin kudade domin tare kujerun aikin Hajji ga maniyata.

Yana mai nuni da cewar, a halin yanzu, jihar Jigawa ce ta farko wajen biyan kujerun aikin Hajjin 2026 a fadin kasar nan.

Babban malamin ya kuma yabawa Darakta Janar na Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Jigawa Alhaji Ahmed Umar Labbo bisa namijin kokarin sa wajen shirye shiryen aikin Hajji akan lokaci.

Da ya waiwayi batun hadaya kuma, Sheikh Bin Usman yace a duk fadin kasar nan, jihar Jigawa ce take da lasisin yin Hadaya ga maniyata.

Ya ce ita kadai ce tilo take samarwa da maniyatan ta masauki a kusa da harami sabanin wasu hukumomin alhazai da suke yayatawa.

A na shi jawabin, Darakta Janar na Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Jigawa, Alhaji Ahmed Umar Labbo ya ce wannan shi ne karo na uku da Gwamna Umar Namadi ke bai wa hukumar rancen kudi domin tare kujerun aikin hajji.

Ya ce makasudin bada rancen kudaden shi ne domin bai wa maniyatan jihar damar sauke farali.

A don haka, Labbo yace tuni hukumar ta ci gaba da rijistar maniyatan aikin Hajjin 2026 tare da bada tabbacin hukumar na ci gaba da rike kambunta wajen gabatar da aikin hajjin.

Kazalika, Alhaji Ahmed Umar Labbo, ya shawarci sauran hukumomin Alhazai su kara himma wajen biyan kudaden kujerun da aka ware musu akan lokaci.

Ya kuma yaba wa NAHCON da Gwamnatin jihar bisa hadin kai da goyon bayan da suke baiwa hukumar a kowanne lokaci.

 

Usman Mohammed Zaria

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Babban Burina Zama Fitacciyar Jaruma A Duniya —Aisha Umar
  • Kwamitin Tsaron MDD ya goyi bayan shirin Morocco game da yankin Yammacin Sahara
  • M D Duniya Tayi Gargadi Game Da Gwajin Nukiliya Da Amurka Ta Sanar Za ta yi
  • Ya Kamata Sin Da Amurka Su Zama Kawayen Juna Ba Abokan Gaba Ba
  • Real Madrid zata nemi diyyar Dala bilyan 4 daga UEFA
  • Ana zargin ɗa da kashe mahaifinsa a Kano saboda hana shi ƙara aure
  • Sin Ta Fitar Da Jerin Sakamakon Tattaunawar Tattalin Arziki Da Cinikayya Da Tawagar Kasar Da Ta Amurka Suka Cimma 
  • Borno ta fara fitar da kayan robobi zuwa ƙasashen waje – Zulum
  • Jihar Jigawa Ce Ta Fara Biyan Kudaden Kujerun Aikin Hajjin 2026- NAHCON
  • Amurka Ta Hana Marubuci Dan Nigeria Wole Soyinka Izinin Shiga Amurka