Jauro Jatau: Al’umma sun roƙi gwamnati ta samar musu da wutar lantarki
Published: 17th, August 2025 GMT
Al’ummar unguwar Jauro Jatau da ke hanyar Bypass a Ƙaramar Hukumar Akko, Jihar Gombe, sun koka kan tsawon watannin da suka shafe ba tare da wutar lantarki ba.
Sun roƙi gwamnati, ’yan siyasa da masu hannu da shuni su kawo musu ɗauki cikin gaggawa.
Gwamnonin Arewa sun yi ta’aziyyar rasuwar Sarkin Zuru Adam A.Zango ya auri jarumar Kannywood
Sun bayyana cewa tun watan azumin Ramadan da ya gabata suke cikin duhu saboda rashin tiransufoma, lamarin da ya jefa su cikin ƙunci da wahala.
Muhammad Idris Gargajiga, wanda ya yi magana da wakilinmu a madadin mazauna yankin, ya ce duk lokacin da suka kai ƙorafi sai a ce musu yankin ba shi da rumfar zaɓe, abin da suka kira da rashin adalci.
“Yawancinmu mun fito daga birnin Gombe muka koma zama a nan. Amma duk da haka ana tauye mana haƙƙoƙi, ana nuna mana kamar ba mu da cikakken matsayi a yankin,” in ji shi.
Al’ummar yankin sun ce rashin wuta ya haifar musu da tsaiko a harkokin kasuwanci da rayuwar yau da kullum.
Wakilinmu ya yi ƙoƙarin tuntuɓar hukumar Jos Electricity Distribution Company (JED), amma haƙarsa ba ta cimma ruwa ba.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Lantarki Rashin Wuta
এছাড়াও পড়ুন:
Gwamnati Na Ƙoƙarin Tsoratar Da Ni Don In Shiga APC – Sanata Tambuwal
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp