Gaza: A cikin sa’o’i 24 Mutane da dama sun yi shahada daruruwa sun jikkata a hare-haren Isra’ila
Published: 17th, August 2025 GMT
Ma’aikatar lafiya ta Falasdinu a Zirin Gaza ta sanar a yau cewa akalla mutane 70 suka yi shahada da suka hada da 8 da aka gano gawarwakinsu, yayin da wasu 385 suka jikkata a cikin kasa da sa’o’i 24 da suka gabata, sakamakon hare-haren da Isra’ila a sassa daban-daban na yankin.
Ma’aikatar ta yi nuni da cewa, adadin wadanda abin ya shafa na ci gaba da karuwa, kasantuwar akwai wadanda suke makale a karkashin baraguzan gine-gine da kuma kan tituna, saboda motocin daukar marasa lafiya da jami’an agaji sun kasa kai musu dauki kawo ya zuwa yanzu.
Bisa kididdigar da aka fitar a hukumance, adadin wadanda suka shahada a yakin ya karu zuwa 61,897, yayin da 155,660 suka jikkata, tun daga ranar 7 ga Oktoba, 2023, yayin da adadin wadanda suka yi shahada ko jikkatar tun ranar 18 ga Maris, 2025, ya zuwa yau ya kai 10,362 , sai kuma wadanda suka jikkata adadinsu ya kai 43,619.
A cikin sa’o’i 24 da suka gabata, an kashe mutane 26 tare da raunata 175 yayin da suke yunkurin samun kayan abinci, abin da ya kawo adadin mutuwar mutane 1,924 da kuma jikkata sama da 14,288 tun bayan fara kai hare-hare kan yankunan rabon kayan agaji da jin kai.
Asibitocin Gaza sun yi rahoton mutuwar mutane 11 masu nasaba da yunwa da suka hada da yaro daya a cikin sa’o’i 24 da suka gabata, wanda ya kawo adadin wadanda yunwa ta kashe zuwa 251, daga cikinsu akwai kananan yara 108.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka An kashe mutane 17 a harin da dakarun RSF suka kai a El Fasher, Sudan August 17, 2025 Kasashen Larabawa Da Na Musulmi Sun Yi Allah Wadai Da Kalaman Netanyahu Kan Mamaye Yankunan Kasashe August 16, 2025 Iran Ta Yi Allah Wadai Da Furucin Jami’ar Kotun ICJ Na Goyon Bayan Isra’ila August 16, 2025 Araqchi Ya Gode Wa Gwamnatin Iraki Da Al’ummarta Kan Kyakkyawar Tarbar Masu Ziyarar Arba’een August 16, 2025 Hamas Ta Yi Allah Wadai Da Sanya Ta Cikin Jerin Sunayen Bakin Littafin MDD August 16, 2025 Sojojin Mamayar Isra’ila Suna Ci Gaba Da Tafka Muggan Ayyukansu A Yankin Zirin Gaza August 16, 2025 Mataimakiyar Shugaban Kotun ICJ Ta Ce Tana Goyon Bayan HKI August 16, 2025 Burtaniya Zata Gurfanar Da mutane 60 Saboda Goyon Bayan Falasdinawa August 16, 2025 Qalibof: Dole Ne Musulmi Su Hada kai Don Matsin Lamba Ga HKI August 16, 2025 Aragchi: Yiyuwan Sake Shiga Yaki Da HKI Nan Kusa Yana Da Wuya August 16, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: adadin wadanda
এছাড়াও পড়ুন:
Mutane 2 sun rasu a rikicin manoma da makiyaya a Kebbi
Aƙalla mutane biyu ne suka mutu a rikicin da ya ɓarke tsakanin manoma da makiyaya a unguwar Dambo, wani kauye da ke da tazarar ’yan kilomita daga Birnin Kebbi, babban birnin Jihar Kebbi.
Wani mazaunin yankin mai suna Ɗanladi Usman ya ce rikicin ya fara ne bayan an kashe wani mutum mai suna Sule yayin da yake aiki a gonarsa.
“Kashe Sule ya tayar da hankulan al’umma, inda manoma suka ɗauki fansa suka kashe wani makiyayi da har yanzu ba a gano sunansa ba,” in ji shi.
Ya ƙara da cewa makiyayan sun sha faɗa da manoma a kwanakin baya bayan sun aike musu da sako cewa su hanzarta girbe amfanin gonakinsu domin za su riƙa wucewa da shanunsu ta gonakin nan ba da daɗewa ba.
An yi jana’izar sojojin da ’yan bindiga suka kashe a Kebbi Rashin wutar lantarki ya rusa harkoki a Kaduna, Kano da Katsina“A lokacin da wasu manoma suka je gonakinsu domin yin aiki, sai makiyaya suka kai musu hari, daga nan ne aka shiga tashin hankali,” in ji shi.
Wani mazaunin yankin, Abubakar Aliyu, ya roƙi gwamnati da ta kawo ƙarshen wannan rikici na dogon lokaci tsakanin manoma da makiyaya.
“Wannan matsala ba sabuwa ba ce, kuma sarakunan gargajiya sun san da ita. Muna fatan a samu adalci ga waɗanda abin ya shafa, kuma gwamnati ta kawo ƙarshen wannan rikici,” in ji shi.
Rundunar ’yan sanda a jihar ba ta tabbatar da faruwar lamarin ba domin jami’in hulda da jama’a na rundunar, CSP Nafiu Abubakar, ba a iya samun sa a waya ba lokacin da ake haɗa wannan rahoto.