An kama manyan shugabannin ’yan ta’addan ƙungiyar Ansaru — Ribadu
Published: 17th, August 2025 GMT
Jami’an tsaro sun kama manyan shugabannin ƙungiyar ’yan ta’adda ta Ansaru, ciki har da shugaban ƙungiyar, Mahmud Muhammad Usman wanda aka fi sani da Abu Baraa.
An daɗe ana zarginsa da kitsa hare-hare masu yawa a Najeriya.
’Yan sanda sun kama matashin da ya yi garkuwa da kansa a Ondo Majalisar dokokin Gombe ta fara duba ƙudirin ƙirƙirar sabbin gundumomi 13Mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro, Nuhu Ribadu ne, ya tabbatar da kamen a wani taron manema labarai da ya gudanar a Abuja, a ranar Asabar.
Ya bayyana cewa an cafke Abu Baraa a watan Yuli bayan shafe tsawon watanni ana bin diddiginsa.
Haka kuma an kama wani shugaban ƙungiyar, mai suna Abubakar Abba.
Ribadu, ya ce wannan nasara babban ci gaba ne a yaƙi da ƙungiyar Ansaru, wacce ta ɓalle daga tsagin Boko Haram a shekarar 2012.
Duk da cewa a farko ta bayyana kanta a matsayin “ƙungiya mai tausayin jama’a” daga baya ta zama mai aikata mummunan ayyukan ta’addanci.
Ta kai wa sojoji, fararen hula da kuma gine-ginen gwamnati hare-hare.
Tsawon shekaru, ƙungiyar ta samar wa kanta maɓoya a cikin birane da kuma dazuka, musamman a kusa da yankin Kainji da ke tsakanin Jihohin Neja da Kwara har zuwa Jamhuriyar Benin.
A cewar Ribadu, Abu Baraa shi ne ke da alhakin shirya ayyukan ta’addanci a sassan Najeriya da kuma sace mutane da fashi don samun kuɗaɗen da suke amfani da su wajen aikata ta’addanci.
Mataimakinsa, Mahmud al-Nigeri wanda aka fi sani da Mallam Mahmuda, ya samu horo a ƙasar Libya tsakanin shekarar 2013 zuwa 2015, inda ya ƙware wajen amfani da makamai da kuma haɗa bama-bamai.
Ribadu, ya danganta su da wasu manyan laifuka da suka haɗa da ɓalle gidan yarin Kuje a 2022, da harin da suka kai wajen haƙar ‘uranium’ a Jamhuriyar Nijar.
Har ila yau, suna da hannu a sace injiniyan Faransa Francis Collomp a 2013, da kuma sace manyan mutane kamar Alhaji Musa Umar Uba na Daura a 2019 da Sarkin Wawa na Jihar Neja.
Ribadu, ya ce wannan kamen babban nasara ce a ƙoƙarin Najeriya na kawar da ta’addanci.
Ya ƙara da cewa jami’an tsaro sun samu muhimman bayanai daga hannunsu, kuma ana bincike a kansu domin kawo ƙarshen ƙungiyar.
Ya jinjina wa dakarun soja da sauran hukumomin tsaro bisa jajircewarsu, inda ya bayyana wannan babban ci gaba ne wajen rushe ƙungiyar Ansaru gaba ɗaya.
Ministan Watsa Labarai, Mohammed Idris, ya roƙi ’yan Najeriya da su ci gaba da bai wa jami’an tsaro bayanai masu amfani domin kawo ƙarshen ta’addanci, tare da tabbatar da tsaro da ci gaban tattalin arziƙi.
Wannan nasara na zuwa ne bayan shekara tara da kama wani tsohon shugaban Ansaru, Khalid al-Barnawi, a shekarar 2016.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: yan ta adda Ansaru Boko Haram hare hare Ƙungiya
এছাড়াও পড়ুন:
Gwamnatin Tarayya Ta Gargaɗi ASUU Kan Yajin Aiki, Ta Ce “Babu Aiki, Babu Albashi”
ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Tinubu Ya Isa Birnin Rome Don Halartar Taron Tsaro Na Aqaba October 12, 2025
Manyan Labarai An Sauya Kwamishinan Ƴansandan Abuja Saboda Rashin Tsaro October 12, 2025
Tsaro Sojoji Sun Kashe Kwamandan IPOB ‘Alhaji’, Da Wasu 26, Sun Kama 22 October 12, 2025