2025-08-16@08:27:25 GMT
إجمالي نتائج البحث: 5451

«Al Burhan ya»:

    Wani babban jami’in diflomasiyyar Iran ya ce Jamhuriyar Musulunci ta Iran a shirye take ta ci gaba da tattaunawa da kasashen Turai da kuma kare hakkinta na nukiliya cikin lumana. Mataimakin ministan harkokin wajen Iran Saeed Khatibzadeh ne ya bayyana hakan a wata hira da ya yi da tashar dillancin labaran Turkiyya, a lokacin da yake amsa tambaya kan tattaunawa da aka shirya yi tsakanin Iran da E3 (Faransa, Birtaniya da Jamus) a nan gaba, yayin da kuma an riga an gudanar da zama zagaye na biyu na masana da kwararru a matsayin sharar fage a birnin Istanbul na kasar Turkiyya a karshen watan Yuli. “Yanzu, wadannan shawarwari za su ci gaba, mun yanke shawarar ci gaba, kuma za mu...
    Shugaban majaliasar gudanarwa na kasar Sudan kuma babban hafsan hafsan sojojin kasar Sudan Abdel Fattah al-Burhan, ya yi alkawarin fatattakar dkarun RSF, tare da kawar da “duk wata dama ta yin sulhu.” Kamfanin dillancin labaran Anadolu na kasar Turkiyyay a bayar da rahoton cewa, al-Burhan ya ce sojojin za su ci gaba da yaki ko ta halin kaka, kuma ba za su ci amanar sadaukarwar wadanda aka kashe a rikicin ba. Al-Burhan ya yaba da irin tsayin dakan da sojojin suka yi a manyan garuruwa irinsu El Fasher, Babanusa, da Kadugli, yana mai cewa suna ci gaba da kare kasar ta kowace fuska. Majiyar Al-Mayadeen ta bayar da rahoton cewa, Al-Burhan ya gabatar da wani fayil na tsaro da ke...
    Rundunar sojan Mali ta sanar da kame wasu manyan hafsoshin sojin Mali guda biyu, dan kasar Faransa, da wasu mutane da dama da ake zargi da yunkurin tayar da zaune tsaye a kasar ta hanyar yunkurin juyin mulki, wanda kuma aka yi nasarar dakile shi. Ministan tsaron kasar Janar Daouda Aly Mohammedine ne ya bayyana hakan ta gidan talabijin na kasar a yammacin jiya Alhamis, inda ya ce an shawo kan lamarin gaba daya, kuma an fara gudanar da bincike. Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da tashe-tashen hankula na siyasa, kuma ya biyo bayan jita-jitar da ake ta yadawa a ‘yan kwanakin nan kan tsare jami’an soji. Hukumomi sun bayyana dan kasar Faransa...
    “Mun amshe bukatun, sannan bayan hakan kwamitin yin nazari kan sake yi wa tsarin mulki garambawul wanda mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Jibrin Barau yake jagoranta zai tattance tare da shirya rahoto ga majalisar. “Da zarar rahoton ya kammala, majalisar dattawa tare da hadin gwiwar majalisar wakilai za su gudanar da cikakken jin ra’ayin jama’a. Wannan zai ba da dama ga dukkan masu ruwa da tsaki da suka hada da masu goyon baya da masu adawa su gabatar da hujjojinsu. Bayan haka, majalisun guda biyu za su yanke shawara kan wadannan bukatun. “Batun kirkirar sabbin jihohi abu ne mai matukar muhimmanci wanda ke bukatar duba batutuwan al’umma, yankuna, da samun alkaluman tarihi. A wasu lokuta, ko a cikin jihohin da...
    Tun Farko tawagar gwamnatin ta Isa fadar hakimin Barnawa domin isar da sakon ta’aziyyar gwamnatin jihar kaduna na rashin matashi inda suka tabbatar wa da Hakimin cewa gwamnatin jihar kaduna zatayi duk Mai yiwuwa wajen ganin anyiwa matashi Abubakar adalci da kuma gano dalilin mutuwarsa.   Hakazalika, tawagar gwamnan sun Kai ziyarar jaje gidan mamacin domin jajantawa iyayensa da ‘yan uwansa .   “kwamishinan ya Kara da cewa ‘Mai girma gwamna Uba Sani Yaso yazo da kansa amma bisa wasu abubuwa da suka bijiro hakan ya sanya ya wakilto mu saboda haka gwamna ya kadu matuka da samun labarin rasuwar Abubakar”.   Maiyaki, yace domin ganin an dakile matsalar yawaitar tu’ammali da muyagun kwayoyi, gwamnatin jihar Kaduna ta Kafa wani...
    Daya daga cikin manyan nasarorin da Dakta Bello Matawalle ya samu shi ne kaimi da aka yi wurin yaki da ta’addanci, ta hanyar kyautata hadin gwiwa da Sojojin kasa, da Sojojin sama da sauran hukumomin tsaro. An yi rugu-rugu da matattaran ‘yan ta’adda a Arewa Maso Gabas, wanda hakan ya yi sanadiyar raguwar hare-hare. A Arewa Maso Yamma kuwa, gagarumar gudummawa da ma’aikatar tsaro a karkashinsa ta amfani da karfin soja ya yi mummunar illa ga matattarar ‘yan ta’adda wanda hakan ya kyautata fata da al’umma ke da shi cewa an kusan share musu hawaye.   2. Kula da walwalar sojoji da karfafa musu gwiwa Ganin cewa karfin Sojan Nijeriya ya dogara ne a rundunarta, Dakta Bello Matawalle ya inganta...
    A jiya Alhamis ne aka kaddamar da gasar wasanni ta mutum mutumin inji ta duniya a birnin Beijing na kasar Sin, wadda ke gabatar da sabbin ci gaban da aka samu a bangaren aiki da basira da motsi, wajen kera mutum mutumin inji. Kungiyoyi 280 daga kasashe 16, ciki har da Amurka, da Jamus, da Italia ne za su fafata a gasar da za a yi daga Juma’a zuwa Lahadi, a dakin wasan gudun kankara na kasa. Mutum mutumin injin za su fafata ne cikin wasanni 26 na motsa jiki, kamar gudu, da dogon tsalle, da sarrafa jiki, da kwallon kafa, da ma wasu ayyukan da suka shafi basira a fannoni daban-daban kamar jigilar kayayyaki, da ware magunguna, da aikin...
    Tinubu ya kara da cewa tun bayan karbar mulkinsa, gwamnatinsa ta bayar da fifiko wajen samun damar kudi kuma ta yi alkawarin tallafa wa harkokin kasuwanci da zai habbaka samar da ayyuka da samun kwarewa da kuma masana’antu. Ya yaba wa gwamnatin Kuros Ribas kan kirkiro shirin tattaunawa da fasahar zamani a harkokin kasuwancin jihar, yana mai cewa wannan ya sa jihar ta yi fice a bangaren fasahar zamani. “Fasahar zamani zai bai wa harkokin kassuwanci kanana da matsakaita samun damar intanet mai sauri da mai arha da kayayyakin aiki na zamani da samun hadin gwiwa don koyo da ingantawa, tare da tunawa cewa duniya ta kasance wani fage na bunkasa harkokin kasuwanci a zamanance. “’Yan kasuwa da ke habaka...
    Da safiyar yau Jumma’a, hukumar kididdiga ta kasar Sin ta gabatar da rahoton tattalin arzikin kasar na watan Yuli, inda ta bayyana cewa, kasar Sin ta gaggauta daidaita manufofin tattalin arziki daga manyan fannoni, tare da inganta dunkulewar manyan kasuwanni cikin sassan kasar, ta yadda aka tabbatar da bunkasuwar tattalin arziki cikin tsari, da kara bukatun al’umma, da tabbatar da dorewar samar da aikin yi da daidaiton farashin kaya, da kuma raya sabon karfin samar da hajoji da hidimomi masu karko, inda aka cimma sabbin nasarori kan neman ci gaba mai inganci. A fannin masana’antu kuma, yawan kayayyakin da aka samar ya karu da sauri, kana, aikin kera na’urori da aikin samar da kayayyaki da fasahohin zamani suna bunkasuwa kamar...
    An sami gawar wani sojan HKI wanda ya taba yaki a Gaza wanda kuma ake zaton shi ya kashe kansa. Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Jaridar HKI da yaren Hebru mai suna  Yedioth Ahronoth yana fadar cewa an gano gawar sojan dan shekara 28 wanda ba’a bayyana sunansa ba a dajin dajin sweezland kusa da yankin tiberias a yau Alhamis. Labarin ya kara da cewa, idan ya tabbata sojan ya kashe kansa ne to kuwa shi ne 17 da suka kashe kansu tun bayan fara yaki a gaza a shekara ta 2023. Ahronoth ya cewa sojan ya yi aiki da runduna ta 99 a gaza a cikin yan makonnin da suka gabata. Sannan a halin yanzu...
    Ita ma da take nata jawabin Maryam Bukar Hassan ta ce, akwai bukatar a samar da wani shiri na kawo sauyi wajen samar da zaman lafiya mai dorewa. Hakazalika Maryam ta jaddada cewa, idan har ba zaman lafiya babu yadda za a iya cimma muradun ci gaba mai dorewa (SDGs) kuma zai kasance mara amfani. “Ba maganar talauci idan zaman lafiya da adalci sun tabbata.” Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Kakakin ma’aikatar tsaron kasar Sin Jiang Bin, ya soki lamirin kasar Amurka, dangane da yadda ta wanke Japan daga laifukan da ta tafka, yayin yakin duniya na biyu. Jiang Bin, wanda ya yi sukan a Juma’ar nan, ya kira hakan a matsayin mummunan karan-tsaye ga ainihin abun da ya auku a tarihi, kana tozarta damuwar wadanda mamayar dakarun Japan ta cutar. Jami’in ya yi tsokacin ne a matsayin martani ga sanarwar da ma’aikatar harkokin wajen Amurka ta fitar, inda ta ce, bana shekaru 80 ke nan, bayan da Amurka da Japan suka kawo karshen yaki a yankin tekun Pacific. To sai dai kuma a ta bakin Jiang Bin, yayin yakin duniya na biyu, dakarun Japan ‘yan mamaya sun aikata muggan...
    Ruwan sama kamar da bakin ƙwarya da aka yi a garin Potiskum a daren Juma’a zuwa safiyar yau Juma’a ya haifar da ambaliya, wanda ya haifar da tashin hankali ga mazauna garin.   Kamar yadda majiyar da ke garin ta shaidawa Aminiya cewa, ruwan sama kamar da bakin ƙwarya da aka fara shi tun kusan tsakar daren Alhamis ya yi sanadiyyar rugujewar gidaje da dama, inda wasu gine-gine suka ruguje ƙarƙashin ruwan. An sake ceto matafiya 10 da aka sace a Kogi Tinubu ya bar Abuja zuwa Japan da Brazil Sakamakon ambaliyar ruwan ya sa mazauna wasu unguwanni da dama suka rasa matsugunansu inda suke hijira ya zuwa gidajen ‘yan uwa da makarantu, inda suke kokawa kan yadda iftala’in ta afku....
    “Sama da yara miliyan 10.1 ne ba su kai makaranta, kashi 70 masu zuwa makarantar kuma ba su da dabarun koyo, kuma fiye da kashi 60 na malaman firamare na gwamnati ba su da ilimin dijital,” in ji ta Da take yaba wa gwamnatin Koriya ta Arewa bisa tallafin da ta samu ta hannun hukumar raya kasashe ta KOICA, Garba ta ce wannan hadin gwiwa ya taimaka wa kasar wajen sake tunanin koyo, tare da dakile rarrabuwar kawuna, da bai wa makarantu da malamai kwarin gwiwa domin samar da sauyi mai dorewa. Mataimakin Babban Sakatare na UBEC (Technical), Mista Razak Akinyemi Olajuwon, ya bayyana cewa, wannan shiri ya kara wa malamai kwarin gwiwar yin amfani da su da bunkasa abubuwan...
    Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na duniyarmu a uau shiri wanda yake kawo mako labarai masu muhimmanci a makon da ya gabata, wadanda suka shafi siyasa tattalin arziki zamantakrwa , tsaro da sauransu. Sannan mu yi masu Karin bayani daga karshe mu ji ra’ayin masana dangane da su da fatan masu saurarozasu kasance tare da mu a cikin shirimmu nay au. ////…Madallah, masu sauraro shirimmu nay au zai dubi “ranar 40 na Imam Hussain(a) wanda ya fado a ranakun Alhamis ko jumman da suka gabata, a nan Iran da kuma Iraki, kowa da yadda suke yi lissan watan Safar a wajensu. Ranar 40 na Imam Hussain (a) ita  ce ranar 20...
    Jami’an tsaro sun kuɓutar da wasu fasinjoji 10 da aka yi garkuwa da su a hanyar Itobe – zuwa Ochadamu – Anyigba a Ƙaramar hukumar Ofu a Jihar Kogi. Fasinjojin da aka kuɓutar an yi garkuwa da su ne a ranar 11 ga watan Agusta a ƙauyen Ugbakpedo da ke kan titin, lokacin da wata mota ta yi wa fasinjojin kwanton ɓauna. Tinubu ya bar Abuja zuwa Japan da Brazil Matsalar ƙofa ta hana fasinjoji 58 hawa jirgin Abuja zuwa Landan Jami’an tsaron da suka haɗa da: ’yan sanda da ’yan banga da mafarautan yankin sun bayyana cewa sun afkawa dajin da ke yankin kafin ceto matafiyan. “A ranar 13 ga watan Agusta da misalin ƙarfe 4:30 na Asubahi ne...
    Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na duniyarmu a uau shiri wanda yake kawo mako labarai masu muhimmanci a makon da ya gabata, wadanda suka shafi siyasa tattalin arziki zamantakrwa , tsaro da sauransu. Sannan mu yi masu Karin bayani daga karshe mu ji ra’ayin masana dangane da su da fatan masu saurarozasu kasance tare da mu a cikin shirimmu nay au. ////…Madallah, masu sauraro shirimmu nay au zai dubi “ranar 40 na Imam Hussain(a) wanda ya fado a ranakun Alhamis ko jumman da suka gabata, a nan Iran da kuma Iraki, kowa da yadda suke yi lissan watan Safar a wajensu. Ranar 40 na Imam Hussain (a) ita  ce ranar 20...
    “Manufar ita ce a ninka adadin likitoci, ma’aikatan jinya, masu hada magunguna, kwararrun dakunan gwaje-gwaje da sauran kwararru a fannin kiwon lafiya. Wannan ko shakka babu zai kara habaka harkokin kiwon lafiya a kasar,” in ji shi. Tsohon gwamnan Jihar Katsinan ya bayyana cewa, a bana, TETFund ta samu tallafinta mafi girma na Naira Tiriliyan 1.6, wanda ya haura daga kaso 3 na harajin ilimi da aka dora wa ribar kamfanonin da ke kasuwanci a Nijeriya kamar yadda dokar TETFund ta tanada. Masari ya bayyana cewa, daga cikin Naira Tiriliyan 1.65, an fitar da Naira biliyan 225 zuwa asusun bayar da lamuni na ilimi na Nijeriya (NELFUND), domin shirin rancen daliban gwamnatin tarayya. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna...
    Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu, ya bar Abuja domin ziyarar aiki zuwa ƙasashen Japan da Brazil. Ya tashi daga Filin Jirgin Sama na Nnamdi Azikiwe da misalin ƙarfe 11:15 na safiyar Juma’a, inda zai tsaya a Birnin Dubai na Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa. Matsalar ƙofa ta hana fasinjoji 58 hawa jirgin Abuja zuwa Landan Matsalar tsaro na iya hana mu ci gaba da rijistar masu zabe a Borno – INEC Manyan jami’an gwamnati da suka raka shi, sun haɗa da Mai Bai wa Shugaban Ƙasa Shawara kan Harkar Tsaro, Nuhu Ribadu. Sauran sun haɗa da Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Ƙasa, Femi Gbajabiamila; da Ministan Kuɗi, Wale Edun. A Japan, Shugaba Tinubu zai halarci Taron Ci Gaban Afirka karo na tara (TICAD9)...
    Hukumar ƙididdiga ta ƙasa (NBS) ta bayyana cewa ƙimar hauhawar farashin kayayyaki a Nijeriya ta sauka zuwa kashi 21.88% a watan Yuli 2025, daga kashi 22.22% da aka samu a watan Yuni 2025. Wannan na nuni da raguwa da kashi 0.34% idan aka kwatanta da watan da ya gabata. Rahoton ya nuna cewa hauhawar farashin abinci na shekara-shekara a watan Yuli 2025 ya kai kashi 22.74%, wanda ya ragu da maki 16.79% idan aka kwatanta da kashi 39.53% da aka samu a Yulin 2024. NBS ta danganta wannan raguwa mai yawa da sauyin shekarar wajen lissafi. Hauhawar Farashin Kayayyaki Ya Kai Kashi 34.80 A Disamban 2024 – NBS Manzon Allah (SAW) Zai Cika Shekara 1,500 Da Haihuwa A Shekarar Nan...
    Shugaban hukumar kula da wasanni ta ƙasa (NSC), Bukola Olopade, ya ƙaryata rahotannin da ke cewa Super Falcons ba su samu kuɗin alawus ɗin da aka yi musu alƙawari ba, yana mai cewa an riga an biya duk ƴan wasan, sai kaɗan daga cikinsu da ke da matsalar asusun banki. Ya ce ya tabbatar da hakan ne daga shugabar ƙungiyar, Rasheedat Ajibade, da kuma hukumar kwallon ƙafa ta ƙasa (NFF). Olopade ya ce ba daidai ne a yi iƙirarin cewa ba a biya kuɗin ba, inda ya ƙara da cewa bai kamata a jefa Ajibade cikin matsalar musanta kalaman da ba ta faɗa ba. Ya bayyana cewa waɗanda ke da matsalar asusun banki su kaɗai ba su samu ba, amma...
    Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) ta ce matsalar tsaro na iya hana ta gudanar da aikin rijistar masu zabe a kananan hukumomin jihar Borno guda hudu. Kananan hukumomin da lamarin zai iya shafa su ne Abadam, Guzamala, Marte da Kala-Balge. Jama’a ba sa yaba wa kokarinmu na hana aikata laifi – Babban Sufeton ’Yan Sanda NAJERIYA A YAU: Halin ƙuncin da ’yan fansho ke ciki a Najeriya Bayanin hakan dai ya fito ne daga bakin Kwamishinan Zabe na jihar, Abubakar Ahmad Ma’aji a jawabin sa ga manema labarai a Maiduguri, a wani vangare na shirye-shiryen fara gudanar da aikin rijistar masu kada kuri’a a ranar Litinin da ke tafe. A cewar shi, INEC ta mayar da rijistar masu zaben a...
    Ina mika sakon gaisuwata zuwa ga Mahaifana, da ‘yan’uwana Fatima Muhammad, Sadiya Muhd, Tahir Muhammad, sai kawayena na tsohuwar makarantarmu da na unguwarmu kamai Zainab Abdulkadir, Shamsiyya Muhammad, Marakisiyya Shu’aib, da fatan sun yi Juma’a lafiyya. Saki daga Kassim Bello Muhammad Makarfi daga Jihar Kaduna Ina yi wa ‘yan’uwa musulmi na fadin duniya fatan alheri, da ilahirin ahalina na kusa da na nesa kamar su Amir Saleh, Amina Bello Makarfi, Sa’adatu Muhammad Kanwa, Kamal Sagir Garba, da dai sauransu. Da fatan sun yi juma’a lafiyya, Amin. Halima Galadima Bebeji daga jihar Kano Idna gaishe da Mahaifiyata Hajiyya Zahra’u Mamman, da mahaifina Alhaji Muhammad Galadima Babeji. Sai sakon gaisuwata zuwa ga al’ummar ‘DYZ Group’ kamar su Khadijah Ibrahim Umar Jambulo(Deeja J),...
    Babban Sufeton ’Yan Sanda na Najeriya, Kayode Egbetokun, ya ce galibin jama’a ba sa yaba wa kokarin jami’ansu na hana aikata laifi a cikin al’umma, duk da yana daya daga cikin manyan ayyukansu. Kayode, wanda Mataimakin Babban Sufeto mai kula da sashen sayo kayayyaki na rundunar, A.A. Hamza ya wakilta, ya fadi hakan ne a Abuja ranar Alhamis, yayin taron kaddamar da wani littafi mai suna “Fraud unmasked”, wanda Dr Preal Ogbulu ya wallafa. Kotun kasar Kanada ta ayyana APC da PDP a matsayin kungiyoyin ta’addanci NAJERIYA A YAU: Halin ƙuncin da ’yan fansho ke ciki a Najeriya A cewarsa, “Duk laifin da aka dakile aikatawa, dole akwai namijin kokarin da aka yi a kan hakan. Kundin tsarin mulki da...
    Bugu da kari kuma, gudummawar da Nijeriya ke bayarwa ga kokarin wanzar da zaman lafiya a duniya ba za su misalta tu ba, wanda hakan ke jaddada aniyarta na inganta zaman lafiya da kwanciyar hankali a duniya. Manufofinta na kasashen waje a al’adance suna nufin ingantawa da kuma kare muradun Nijeriya tare da tallafa wa hadin kan Afirka. Gabatar da ajandar “4D”, a sakamakon haka, yana wakiltar sauyin da aka samu a lokacin da ya dace, wanda hakan zai bude damar karfafa hadin gwiwar da kasashen duniya, tabbatar da zaman lafiya na duniya, da kuma bunkasa matsayin Nijeriya a idon duniya. Sai dai, nasarar wadannan manufofin ya ta’allaka ne a kan aiwatarwar su mai inganci. Ya kamata a lura da...
    Akwai wasu tsaffin ‘yan siyasa daga yankin Arewacin Najeriya,wadanda ke ci da gumin ‘yan Arewa. Wadannan tsaffin ‘yan siyasa, yanzu alkadarinsu ya riga ya karye, ba su da wani abu da ya rage illa su rungumi siyasar kabilanci da bangaranci. Ba tsaffin ‘yan siyasa kawai ba ne. Gungu-gungu ne. Wasun su, tsaffin ‘yan boko ne. Wasu ‘yan Kasuwa. Wasu ma ba wata sana’a ko wani aiki da suka taba yi a rayuwarsu da ya wuce ci da gumin Arewa . Wani abu da ya hade su shi ne, mafi yawansu sun samu damar da za su taimaki Arewa ko mutanen Arewa, amma suka ki. Misali, a cikin irin wadannan mutane, babu maras sa kunya,irin wadanda suka rike mukamai a gwamnatin...
    Wata kotun tarayya a kasar Kanada ta ayyana manyan jam’iyyun Najeriya na APC da PDP a matsayin kungiyoyin ta’addanci yayin da ta hana wani tsohon dan siyasa, Douglas Egharevba, mafaka a kasar saboda alakarsa da jam’iyyun. Jaridar Peoples Gazette ta rawaito cewa alkalin kotun, Phuong Ngo, a hukuncin da ta yanke ranar 17 ga watan Yunin 2025, ta hana dan siyasar izinin shiga kasar bayan samun shi da gaza cika sharudan dokar shige da fice ta kasar. A cewar alkalin, “Dabi’ar wasu ’yan siyasa ’yan PDP, wadanda wasu daga cikinsu ma kusoshi ne a jam’iyyar, da wadanda suka aikata laifukan siyasa ko aka yi da yawunsu, ta yi yawan da ba zai yiwu a ki alakanta shugabancin jam’iyyun da ita...
    Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran ya jaddada cewa: Suna buƙatar kawar da makaman nukiliya da kuma kawo ƙarshen maganganun rashin jin daɗi Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran, Ismail Baqa’i, ya yi kira da a dauki matakin gaggawa kan kawar da makaman nukiliya da kuma amincewa da laifukan tarihi a hukumance kamar harin bam din da aka kai kasar Japan. Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ya nakalto wasu bayanai daga cikin sanarwar da masu rajin kare hakkin bil’adama na Majalisar Dinkin Duniya suka fitar kan bikin cika shekaru 80 da hare-haren nukiliyar da Amurka ta kai a garuruwan Hiroshima da Nagasaki na kasar Japan. Hare-haren nukiliya na Amurka, wanda ya kashe mutane 150,000 a Hiroshima da 80,000 a Nagasaki, ba...
    Laifukan da ake gudanarwa a gabar tekun Siriya: Cin zarafin ya kai ga laifukan yaki! Rahotonni sun bayyana cewa; Kwamitin Majalisar Dinkin Duniya kan kasar Siriya ya fitar ya ce: Rikicin kabilanci da ya faru a gabar tekun Siriya ya kunshi cin zarafi da ya kai ga laifukan yaki. Rahoton ya kara da cewa; Rikicin addini ya shafi mabiya darikar Alawiyya ne, inda aka kashe fiye da mutane 1,400 Alawiyyawa a rikicin addini da suka hada da daukacin iyalai da mata da yara da kuma tsofaffi a gabar tekun Siriya. Bugu da kari, an samu rahotannin kone-kone, sace-sace da kuma wulakanta gawarwakin da wasu ‘yan bindiga suka aikata. Rahoton ya bukaci gwamnatin rikon kwarya ta Siriya da ta fadada kokarin...
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba A wasu jihohin Arewacin Najeriya, masu karɓar fansho suna cikin mawuyacin hali sakamakon ƙarancin kuɗin da ake biyansu duk wata. Wasu daga cikinsu sun bayyana yadda suke karbar naira dubu 5 a kowane wata a matsayin kudin fansho bayan kwashe shekaru suna aiki. NAJERIYA A YAU: Yadda matasa ke bayar da gudunmawa ga ci-gaban al’umma DAGA LARABA: Yadda sinadaran dandanon abinci ke yin illa ga lafiya Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi nazari ne kan irin halin da ’yan fansho ke ciki a wasu jihohin Arewacin Najeriya. Domin sauke shirin, latsa nan
      Alkaluman sun nuna cewa, cikin wa’adin, yawan sakwannin da aka yi jigilarsu a cikin birni daya sun kai biliyan 9.26, adadin da ya karu da kaso 6.5 bisa dari a mizanin shekara, yayin da wadanda aka yi jigilarsu daga birni guda zuwa wani na daban, suka kai biliyan 100.43, karuwar da ta kai ta kaso 19.9 bisa dari cikin wa’adin na watanni bakwai. (Saminu Alhassan)   Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Gwamnan Katsina, Dikko Umaru Radda, ya sanar da miƙa wa mataimakinsa, Malam Faruk Jobe, ragamar mulkin jihar, inda shi kuma zai tafi hutun mako uku domin duba lafiyarsa. Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da kwamishinan yaɗa labaran jihar, Bala Salisu Zango, ya fitar a ranar Alhamis. Sanarwar ta bayyana cewa hutun zai fara ne daga ranar Litinin, 18 ga watan Agusta, 2025. An zabi sabuwar firaminista a Luthuania Mun shirya wa zaben ciki gurbi a Kano —INEC A cewar Gwamna Radda, hutun zai ba shi damar samun kulawar likitoci da kuma tabbatar da cewa zai ci gaba da gudanar da ayyukansa cikin koshin lafiya. “Cikin matakan da nake ɗauka don kula da lafiyata da kuma ganin na yi...
    A yayin da yake martani kan suka da ake yi masa na rashin gabatar da kudirori a gaban majalisar, ya bayyana cewa, “tun da na je Majalisar, ba bu wani dan mazabata da ya rubuto min wani kudiri ko bukata da zan gabatar a gaban Majalisa, duk zarge-zargen karya ne suke yi min, kuma idan har akwai, wani ya fito ya kalubalance ni,” inji shi.   “Hatta gabatar da kudirori da korafe-korafe a majalisar, wasu sai sun amso cin hancin kimanin naira miliyan 1, ko naira miliyan 2, ko naira miliyan 3, domin karantawa a zauren majalisar, bayan an karanta kudirin, kuma dole sai sun bibiyi ‘yan majalisa sama da 360 domin su goyi bayan a amince da kudirin.”  ...
      Tabbas fannonin zamanintar da kai na Sin na iya zama babbar taswira da kasashen Afirka ka iya bi, wajen kaiwa ga bunkasa yankuna, da kyautata zamantakewar al’ummunsu, da samar da isassun damammaki na gudanar da kyakkyawar rayuwa mai cike da walwala ga al’ummun nahiyar.(Saminu Alhassan) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    A yayin da yake martani kan suka da ake yi masa na rashin gabatar da kudirori a gaban majalisar, ya bayyana cewa, “tun da na je Majalisar, ba bu wani dan mazabata da ya rubuto min wani kudiri ko bukata da zan gabatar a gaban Majalisa, duk zarge-zargen karya ne suke yi min, kuma idan har akwai, wani ya fito ya kalubalance ni,” inji shi.   “Hatta gabatar da kudirori da korafe-korafe a majalisar, wasu sai sun amso cin hancin kimanin naira miliyan 1, ko naira miliyan 2, ko naira miliyan 3, domin karantawa a zauren majalisar, bayan an karanta kudirin, kuma dole sai sun bibiyi ‘yan majalisa sama da 360 domin su goyi bayan a amince da kudirin.”  ...
    Bugu da kari, idan an lura da yawan kamfanonin masana’antar samar da kayayyakin lantarki, yawan kamfanonin masana’antar samar da kayayyakin a shekarar 2024 ya kai kusan 42000, wanda ya karu da kusan kashi 9 bisa dari a shekarar 2023.   A farkon rabin wannan shekara, masana’antar lantarki ta kasar ta ci gaba da kiyaye ingantaccen yanayin ci gaba. Kudaden shiga da manyan kamfanonin masana’antar samar da kayayyakin lantarki suka samu ya kai yuan triliyan 8.04, wadanda suka karu da kashi 9.4 bisa dari idan aka kwatanta da na makamancin lokacin bara. (Safiyah Ma) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp...
    “Kowa ya sani wadatar abinci yana ɗaya daga cikin alamun da ke nuna kyautatawar tattalin arziki na ƙasa baki ɗaya, don haka ne muka himmatu wajen ba da namu gudunmawar ta wannan fannin.”   Ya kara da cewa, an kafa gidauniyar ne domin taimakawa a ɓangaren kiwon lafiya, ilimi, tattalin arziki wanda rabon takin na daga cikin shirin gidauniyar na bunƙasa tattalin arziki, da kuma kyautata ci gaban al’umma.   “Wannan shi ne karo na huɗu da wannan gidauniyar ta ke rabon taki duk shekara ga manoma masu ƙaramin ƙarfi da ba za su iya sayen takin a irin wannan lokacin da gona ke buƙata ba.”   “An ware buhun taki guda 6,000 da za a rabar wa manoma masu...
    Shugabar Kungiyar Cinikayya ta Duniya (WTO), Ngozi Okonjo-Iweala, ta bayyana cewa Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu ya cancanci yabo kan daidaita tattalin arzikin ƙasar nan da yake ci gaba da yi.  Okonjo-Iweala ta shaida wa manema labarai hakan ne ranar Alhamis bayan ta gana da shugaban ƙasar a Abuja. Motar tifa ta murƙushe ɗalibai biyu har lahira a Bayelsa Akwai buƙatar samar da sauyin zaman lafiya mai ɗorewa — Maryam Bukar “Shugaban ƙasa [Tinubu] da muƙarrabansa sun yi ƙoƙari sosai wajen daidaita tattalin arzikin Nijeriya. “Wannan namijin ƙoƙarin na Tinubu abu ne da ya zama dole a yaba masa da ba kowa zai iya yi ba. Tsohuwar Ministar Kuɗin ta Nijeriyar ta ƙara da cewa, yanzu aikin da ke gaban...
    Shugaban kungiyar Ansarullah na kasar Yemen Sayyeed Abdulmalik Badruddeen Huthi , a jawabinsa na mako-mako da ya saba gabatarwa, dangane da Falasdinu da kuma sabbin al-amura da suka faru ko suke faruwa a yankin da kuma duniya gaba daya ya tabo al-amura da dama. Tashar talabijin ta Al-Alam wacce take watsa shirye shiryenta da harshen larabci a nan Tehran ta bayyana cewa, shugaban Ansarullah, ya yi gargadi kan cewa, ida HKI tana son dabbaka shirinta na Isra’ila babba, a cikin wannan halin da kasashen larabawa suke rarrabe, hakan zai zama musiba babba. Labarin ya kara da cewa sojojin kasar Yemen sun aiwatar da ayyukan soje a kan HKI a dama a cikin makon da ya gabata, daga cikin cilla makamai...
    Jami’an kwana-kwana a birnin London na kasar Burtaniya sun bukaci marasa lafiya da likitoci da sauran masu aikin a asbitin Guy da su fice daga asbitin saboda hatsarin samuwar wasu sinadarai masu cutarwa a cikinsa. Jaridar da Nation ta kasar Amurka ta bayyana cewa , da masalin karfe 8.49 ne aka shaidawa jami’an kwana-kwana batun hatsarin, sannan a lokacinda suka karasa cikin asbitin sun yi kokarin samar da iska ne a cikin sa don baje sinadarai masu hatsari ga lafiyar mutane da suke zatun sun sulale sun shiga wurare da dama daban a cikin asbitin. Labarin ya bayyana cewa na fidda mutane kimani 150 daga cikin asbitin. Kuma hotunan da aka watsa ta wayoyi sun nuna mutane a wajen asbitin...
      A yankin Arewa-maso-Gabas, ya ce sojojin, sun kawar da ‘yan ta’adda da dama, sun lalata sansanonin kayan aikinsu, sun kwato makamai, sun wargaza hanyoyin hada-hadarsu tare da samar da amintaccen wuri don sake tsugunar da ‘yan gudun hijira.   A cewar Kangye, sojojin sun kama mutane 37 da ake zargin ‘yan ta’adda ne, tare da kubutar da mutane biyar da aka yi garkuwa da su, tare da kwato makamai, alburusai, kayayyakin masarufi, motoci da babura, sannan kuma sun warware wasu bama-bamai cikin nasara a yankin.   Da yake ba da rahoto kan yankin Arewa maso Yamma, Kangye ya ce sojoji sun kama mutane 11 da ake zargin ‘yan ta’adda ne tare da kubutar da mutane 17 da aka yi...
    Rundunar ’yan sandan Jihar Gombe ta kama wani Mai Unguwa mai shekara 55 a garin Zambuk da ke Ƙaramar Hukumar Yamaltu Deba, bisa zargin yi wa wata yarinya ’yar shekara 12 fyaɗe. Kakakin rundunar ’yan sandan Jihar, DSP Buhari Abdullahi ne ya tabbatar da kamen a wata sanarwa da ya fitar ranar Laraba, inda ya bayyana wanda ake zargin Mohammed Tukur da ke ƙauyen Sabon Gari da ke Zambuk. Motar tifa ta murƙushe ɗalibai biyu har lahira a Bayelsa An kama mai babur ɗauke da ƙoƙunan kan mutane a Ogun A cewar rundunar ’yan sandan, lamarin ya faru ne a ranar 9 ga watan Agusta, da misalin ƙarfe 9 na dare, inda ake zargin Mai Unguwar ya yaudari yarinyar (wacce...
    Hukumar kula da kumbuna ta kasar Sin ta ce nan ba da jimawa ba, ‘yan sama jannatin kumbon Shenzhou-20 dake cibiyar binciken sararin samaniya ta kasar, za su gudanar da zagaye na 3 na ayyuka a wajen cibiyar. ‘Yan sama jannatin 3 da suka hada da Chen Dong da Chen Zhongrui da Wang Jie, sun gudanar da irin wannan aiki har sau biyu, a watannin Mayu da Yuni. Baya ga haka, sun kammala ayyukan nazarin muhalli da kula da tantance da kayayyakin aiki a cikin cibiyar da jigilar kayayyaki. (Mai fassara: Fa’iza Mustapha) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp...
    A yayin da yake martani kan suka da ake yi masa na rashin gabatar da kudirori a gaban majalisar, ya bayyana cewa, “tun da na je Majalisar, ba bu wani dan mazabata da ya rubuto min wani kudiri ko bukata da zan gabatar a gaban Majalisa, duk zarge-zargen karya ne suke yi min, kuma idan har akwai, wani ya fito ya kalubalance ni,” inji shi.   “Hatta gabatar da kudirori da korafe-korafe a majalisar, sai an biya kimanin naira miliyan 1, ko naira miliyan 2, ko naira miliyan 3, domin karantawa a zauren majalisar, bayan an karanta kudirin, sai ka bibiyi ‘yan majalisa sama da 360 domin su goyi bayan a amince da kudirin.”   Dan majalisar ya kuma yi...
    Sabuwar mai bada shawara kan harkokin lafiya ta Majalisar Ɗinkin Duniya, Maryam Bukar-Hassan (Alhan_islam) ta bayyana cewa samar da dauwamammen zaman lafiya a duniya shi ne fatansu. Maryam ta bayyana hakan ne a lokacin da babban jami’in kula da ayyukan jin ƙai na Majalisar Ɗinkin Duniya a Nijeriya, Mohammed Malick Fall, ke maraba da ita a ofishin majalisar da ke Abuja. An kama mai babur ɗauke da ƙoƙunan kan mutane a Ogun Gwamnati ta amince a kafa sabbin jami’o’i masu zaman kansu guda 9 Mohammed ya jaddada muhimmancin samar da zaman lafiya, yana mai cewa zaman lafiya wani abu ne da ake buƙata don jin daɗin rayuwar ɗan Adam, kuma idan ba a same shi ba, ci gaban dimokuraɗiyya da...
    Rundunar ’yan sanda a Jihar Ogun ta ce, ta kama wani mai babur mai suna Kadir Owolabi, yana ɗauke da ƙoƙon kan mutane uku. Mai magana da yawun rundunar, CSP Omolola Odutola ce ta bayyana hakan a wata sanarwa da ta fitar a Abeokuta ranar Talata. Gwamnati ta amince a kafa sabbin jami’o’i masu zaman kansu guda 9 Bello Turji bai miƙa wuya ba har yanzu — DHQ Odutola ta ce, binciken da jami’an ’yan sandan tafi da gidanka suka yi a jakar wanda ake zargin, ya kai ga gano wasu kan mutane guda uku. Ta ce, jami’an tsaro ne suka gudanar da aikin bincike na yau da kullum daga rundunar ’yan sanda na tafi da gidanka na 71 PMF,...
    Hedikwatar Tsaro ta Ƙasa (DHQ), ta ce rahotannin da ake yaɗawa cewar ƙasurgumin ɗan bindiga Bello Turji, ya miƙa wuya ba gaskiya ba ne. Daraktan Yaɗa Labarai na Rundunar Tsaro, Manjo Janar Markus Kangye ne, ya sanar da hakan ga manema labarai a Abuja a ranar Alhamis yayin bayani kan ayyukan sojoji. Rashin Lantarki: Babu wanda za mu zaɓa a 2027 — Jama’ar Talasse Ba a ba mu dala 100,000 da gwamnati ta mana alƙawari ba — Super Falcons Ya ce: “Turji bai miƙa wuya ba. Har yanzu muna neman sa.” Turji na daga cikin manyan ’yan bindigar da ake nema ruwa a jallo a Najeriya. Turji ya jagoranci kai wa al’umma hare-hare a Jihohin Zamfara da Sakkwato, inda suka...
    Kyaftin ɗin ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta mata ta Najeriya, Super Falcons, Rasheedat Ajibade, ta ce har yanzu ba a ba su dala 100,000 da Gwamnatin Tarayya ta yi musu alƙawari bayan sun lashe gasar WAFCON a ƙasar Maroko ba. Ajibade, ta bayyana takaicinta game da jinkirin biyan kuɗin da aka musu alƙawari. Amurka za ta sayar wa Najeriya makaman N530bn don yaƙi da ta’addanci ’Yan ci-rani 26 sun nitse a teku suna ƙoƙarin tsallakawa Turai “Ba mu karɓi kuɗin ba tukunna, amma ina fata za a biya mu. Duk alƙawuran da aka mana, yanzu dai ba mu samu komai ba.” Ajibade ta jagoranci tawagar zuwa ga nasara, inda suka sake lashe kofin WAFCON a bana. Bayan nasarar, Shugaba Bola Tinubu...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Ministan harkokin wajen kasar Iran ya yi tsokaci kan furucin Netanyahu game da kafa ‘Babban Kasar Isra’ila’ Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araqchi ya bayyana a safiyar yau alhamis cewa: Kafafen yada labaran yammacin duniya a al’ada na zargin duk wanda ya ambaci ra’ayin ‘yan sahayoniyya na kafa “Babban kasar Isra’ila” da kiyayya ga wata al’umma. Bayanin Araqchi, wanda aka yi da sanyin safiyar Alhamis a shafinsa na yanar gizo na dandalin sada zumunta na X, yana mai mayar da martani ga kalaman fira ministan gwamnatin mamayar Isra’ila Benjamin Netanyahu game da batun kafa “Babban kasar Isra’ila.” A cikin shafinsa na yanar gizo, Araqchi ya yi tambaya cewa: “Shin suna daukan furucin Netanyahu kansa a matsayin mai adawa da wata...
    Gwamanatin Sudan ta yi maraba da sanarwar da Majalisar Dinkin Duniya ta yi na yin Allah wadai da shirin kafa gwamnatin hadaka a kasar Sudan Sudan ta yi marhabin da sanarwar da kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya fitar a jiya Laraba, inda ta yi watsi da shirin dakarun kai daukin gaggawa na kafa gwamnatin hadaka a yankunan da ke karkashinta. Sanarwar ta yi gargadin cewa wannan matakin na barazana ga hadin kan kasar, kuma yana iya yin kasadar kara ta’azzara rikicin, yayin da aka dakile wani hari da dakarun kai daukin gaggawa na kungiyar Rapid Support Forces suka kaddamar a yankin kudu da kudu maso yammacin birnin El Fasher. A cikin wata sanarwa da ma’aikatar harkokin wajen kasar...
    Ƙasar Amurka ta amince ta sayar wa Najeriya makaman da kuɗinsu ya kai Dala miliyan 346, kwatankwacin Naira biliyan 530 don yaƙi da ta’addanci. Makaman da za a siyar sun haɗa da bama-bamai da na’urorin kakkabo jiragen sama da jirage marasa matuka da sauran su. NDLEA ta lalata gonar tabar wiwi a Gombe ’Yan ci-rani 26 sun nitse a teku suna ƙoƙarin tsallakawa Turai A cewar Kamfanin Sarrafa Makamai na Amurka (DSCA), za a sayar wa Najeriya makaman ne domin tallafa wa shirinta na yaki da ’yan ta’adda da masu safarar miyagun ƙwayoyi. Kamfanin ya sanar da cinikin ne a cikin wata sanarwa ranar Laraba. A cewar sanarwar, Najeriya ta buƙaci sayen bama-bamai guda 1,002, na’urar kakkabo jirage guda 1,002,...
    Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi ta Ƙasa (NDLEA) a Jihar Gombe ta ce ta lalata wata babbar gonar Tabar wiwi a Karamar Hukumar Kaltungo a jihar Gombe. Hukumar ta kuma ce ta kama miyagun kwayoyi da darajarsu ta kai miliyoyin naira tsakanin watan Yuni zuwa Agustan 2025. ’Yan ci-rani 26 sun nitse a teku suna ƙoƙarin tsallakawa Turai Dalilan ƙaruwar mace-mace a hanyoyin Najeriya Kwamandan Hukumar a jihar, Mallam Maijama’a Muhammad ne ya bayyana hakan a yayin wata ziyarar kulla zumunci da ya kai wa Darakta-Janar na kafar yada labarai mallakar jihar Gombe (GMC), Ibrahim Isa. Ya ce an kama mutum 69 maza da mata da suke kokarin shigar da miyagun kwayoyi cikin jihar a wasu lokuta. Muhammad...
    Akalla ’yan ci-rani 26 sun mutu bayan jiragen ruwan da suke ciki guda biyu sun nitse a teku a kusa da tsibirin Lampedusa na ƙasar Italiya. Hukumar Kula da ’Yan Gudun Hijira ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce ana hasashen ƙarin wasu mutanen kuma sun ɓace yayin da ake ci gaba da aikin ceto su. Allah zai kunyata masu ɗaukar nauyin ta’addanci a Zamfara — Gwamna Dauda Dalilan ƙaruwar mace-mace a hanyoyin Najeriya Galibi dai ’yan ci-ranin da suka fito daga ƙasashen Afirka na ƙoƙarin tsallakawa nahiyar Turai ne domin samun ingantacciyar rayuwa. Ko a ranar Laraba dai ma’aikatan ceto sun ce sun ceto mutum 60 da ransu, wadanda suka hada da maza 56 da kuma mata hudu, sannan aka...
    Masar ta yi Allawadai da kalaman Benjamin Netanyahu game da abin da ya kira shirinsa na kafa babbar kasar yahudawa ko kuma Isra’ila Babba. Wannan dai ya zo ne a cikin wata sanarwa da ma’aikatar harkokin wajen Masar ta fitar, bayan da firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya yi magana kan wanann batu, wanda ya tayar da hankulan Larabawa kuma suka yi watsi da shi. Ma’aikatar harkokin wajen Masar ta ce “tana tabbatar da aniyarta ta abbatar da zaman lafiya a yankin Gabas ta Tsakiya tare da yin Allah wadai da abin da wasu kafafen yada labaran Isra’ila suka ruwaito dangane da abin da ake kira Isra’ila Babba. Ya yi bayanin cewa, “ya bukaci a yi karin haske kan hakan, bisa...
    Wasu da ake zargin ’yan bindiga ne sun kashe wani tsohon malami kuma manomi, Andrew Imuekheme, a Jihar Edo. Lamarin ya faru ne a ranar Talata a garin Ikabigbo, da ke Masarautar Uzairue, a Ƙaramar Hukumar Etsako ta Yamma. Allah zai kunyata masu ɗaukar nauyin ta’addanci a Zamfara — Gwamna Dauda Dalilan ƙaruwar mace-mace a hanyoyin Najeriya Rahotanni sun ce Malam Andrew na kan hanyarsa daga gona lokacin da maharan suka tare shi, tare da ɗauke shi zuwa daji. Wata mata da ta tsere daga hannun maharan ta koma cikin gari tare da sanar wa mafarauta, waɗanda suka fara bincike nan take. Tuni jami’an tsaro suka umarci manoma da ke da gonaki a kusa da yankin da su koma gidajensu...
    Ministan harkokin wajen Yemen Jamal Amer a ranar Laraba ya karbi wata wasika daga Dr. Khalil al-Hayya shugaban kungiyar Hamas a Gaza, wanda wakilin kungiyar a Sanaa, Moaz Abu Shamala ya mika. A cikin wasiƙar nasa, al-Hayya ya bayyana matuƙar godiyar Hamas ga sadaukarwa da tsayin dakan al’ummar Yemen, yana mai bayyana su a matsayin “‘yan’uwa na gaskiya, Ansar Allah,” a tinkarar mamayar Isra’ila da kawayenta duk da gagarumar sadaukarwa, barazana, da hare-hare. Ya tabbatar da cewa nisan da kasar Yamen ke da shi da Falasdinu ya kara dankon kusancinta da al’ummar Palastinu ne kawai da kuma kudurinta na ci gaba da ba da taimako da taimako da kuma kare Gaza da Palastinu. Share 0 0 votes Article Rating Subscribe...
    Wani mazaunin Safana, Iliyasu Sani, ya ce sulhun ya kawo sauƙi ga rayuwar jama’a, domin yanzu suna iya zuwa kasuwa da yin noma ba tare da fargaba ba. Masani a fannin tsaro, Kabiru Adamu, ya ce talauci da rashin tsaro ne suka sa jama’a neman mafita da kansu. Ya kuma bayyana cewa idan duk ɓangarorin suka tsaya kan alƙawarin da aka yi, wannan sulhu na iya zama mataki na farko na samun zaman lafiya na dindindin a yankin. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Duk da kara wayar da kan direbobi da fasinjoji da Hukumar Kiyaye Hadura ta Kasa (FRSC) ta ce tana yi, ana kara samun ƙaruwar wadanda ke rasa rayukansu sakamakon hadura a titunan kasar nan. A shafinta na internet, FRSC ta ce a watanni uku na farkon 2024, mutane 1,471 ne suka rasa rayukansu sakamakon hatsarin mota. Kazalika, a watanni uku na farko na wannan shekara ta 2025, adadin ya haura zuwa mutane 1,593 — karin mutum 122, ko kuma kashi 8.3 cikin dari. NAJERIYA A YAU: Yadda matasa ke bayar da gudunmawa ga ci-gaban al’umma DAGA LARABA: Yadda sinadaran dandanon abinci ke yin illa ga lafiya Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci...
    Gwamna Dauda Lawal na Jihar Zamfara, ya ziyarci wasu garuruwa a Ƙaramar Hukumar Kauran Namoda, bayan jerin hare-haren ’yan bindiga da suka yi sanadiyyar mutuwar mutane da dama. Gwamnan, ya la’anci kisan gillar, tare da bayyana shi a matsayin marasa imani, kuma Allah zai fallasa su ya kunyata su. Majalisar Zartaswa ta dakatar da ƙirƙirar sabbin manyan makarantu a Nijeriya Tinubu zai tafi ziyarar ƙasashe 3 A ranar Laraba, ya ziyarci ƙauyuka biyar da abin ya fi shafa; Banga, Sakajiki, Kuryar Madaro, Maguru, da Tambarawa, inda mutane da dama suka rasa ’yan uwansu. Bayan samun labarin hare-haren, nan da nan ya tura mataimakinsa ya je ya jajanta wa mutanen da abin ya shafa. Bayan dawowarsa Gusau, ya je da kansa...
    A yayin ziyarar, Gwamna Lawal ya jajantawa iyalan waɗanda suka rasa ‘yan uwansu tare da tabbatar wa al’ummar yankin ƙudurinsa na tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyi.   A nasa jawabin, gwamnan ya yi kakkausar suka ga hare-haren da ’yan bindiga ke kai wa a baya-bayan nan, yana mai cewa da gangan maƙiya ke nufin waɗannan munanan ayyuka don yaɗa tsoro a tsakanin al’umma.   “Na ziyarci garin Banga ne domin jajanta wa jama’a game da harin da ‘yan bindiga suka kai a kwanakin baya.   “Lokacin da abin takaicin ya faru, na kasance ba na kusa, amma daga samun labarin, na umarci mataimakin gwamna da ya jagoranci wata babbar tawaga domin ziyarar jaje.   “A jiya ne na dawo...
    Muryoyi daga ko’ina cikin duniya sun nemi a warware matsalar bisa turbar adalci. Shugabannin tarayyar Turai sun yi ta kira ga kasashen Sin da Amurka da su kiyaye bude kasuwanni da gudanar da gasa ta gaskiya. Kasashen kudu maso gabashin Asiya, sun ba da shawarar tabbatar da kwanciyar hankali. Kasashen Afirka da na Latin Amurka sun nuna damuwa da halin da ake ciki saboda barazanar da lamarin yake yi ga damarmakin zuba jari da kasuwancin kasashensu. Gyaruwar dangantakar tattalin arziki tsakanin Sin da Amurka za ta iya haifar da wani sabon zamani na hadin gwiwa, da kirkire-kirkire, da ci gaban da ya kunshi kasashen duniya baki daya. A wannan duniyar tamu wadda bukatar hada hannu da juna ke kara bayyana,...
    Gwamnatin Tarayya ta yanke shawarar dakatar da ƙirƙirar sabbin manyan makarantu har na tsawon shekaru bakwai masu zuwa a duk faɗin Nijeriya. Dakatarwar ta shafi ƙirƙirar sabbin jami’o’i, kwalejojin ilimi da kuma kwalejojin kimiyya da fasaha na tarayya kamar yadda Majalisar Zartarwa ta Tarayya (FEC) ta tabbatar. Tinubu zai tafi ziyarar ƙasashe 3 An naɗa sabon Sarkin Alkaleri a Bauchi Wannan mataki, a cewar Ministan Ilimi Dakta Olatunji Alausa, an ɗauke shi ne domin rage yawan makarantun da ba a amfani da su yadda ya kamata, lamarin da zai ba da damar mayar da hankali wajen gyara da inganta waɗanda ake da su yanzu. Da yake zantawa da manema labarai bayan taron na FEC a fadar shugaban ƙasa ranar Laraba,...
    130-Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka  barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na kissoshin rayuwa shirin wanda yake kawo maku kissoshi wadanda suka zo cikin alkur’ani mai girma ko kuma cikin wasu littafai wadanda suka hada da littafin Dastane Rastantan na Aya. Shaheed Murtadan Muttahary ko kuma cikin littafin mathnawi na Maulana Jalaluddeen Rumi ko kuma cikin wasu littafan, da fatan masu sauraro za su kasashence tare da mu a cikin shirimmu na yau. ///… Madallah, masu sauraro idan kuna tare da mu a cikin shirimmu da ya gabata a kuma cikin sirar Imam Al-Hassan Al-Mutaba, (a) dan Fatima (s) diyar manzon All..(s) da muke kawo maku, a cikin shirimmun da ya gabata mun bayyana yadda Amirulmuminina Aliyu...
    129-Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka  barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na kissoshin rayuwa shirin wanda yake kawo maku kissoshi wadanda suka zo cikin alkur’ani mai girma ko cikin wasu littafai wadanda suka hada sa littafin Dastane Rastantan ko kuma cikin littafin mathnawi na maulana jalaluddeen Rumi ko kuma cikin wasu littafan da fatan masu sauraro zasu kasashence tare da mu a cikin shirimmu na yau. ///… Madallah, masu sauraro idan kuna tare da mu a cikin shirimmu da ya gabata a kuma cikin sirar Imam Al-Hassan Al-Mutaba, (a) dan Fatima (s) diyar manzon All..(s) da muke kawo maku, a cikin shirimmu da ya gabata. Mun bayyana yadda Imam Ali (a) ya kammala hujja a kan mutanen...
    127-Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka  barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na kissoshin rayuwa shirin wanda yake kawo maku kissoshi wadanda suka zo cikin alkur’ani mai girma ko cikin wasu littafai wadanda suka hada sa littafin Dastane Rastantan ko kuma cikin littafin mathnawi na maulana jalaluddeen Rumi ko kuma cikin wasu littafan da fatan masu sauraro zasu kasashence tare da mu a cikin shirimmu na yau. ///… Madallah, masu sauraro idan kuna tare da mu a cikin shirimmu da ya gabata a kuma cikin sirar Imam Al-Hassan Al-Mutaba, (a) dan Fatima (s) diyar manzon All..(s) da muke kawo maku, a cikin shirin munyi maganar yadda Imam Ali (a) da dansa Imam Al-Hassan(a) tare da rundunarsu suka iso...
    125-Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na kissoshin rayuwa shiri wanda yake kawo maku kissoshi wadanda suka zo cikin alkur;abi mai girma ko cikin wasu littafan wadanda suka hada da Dastane Rastan na Aya. Shahid Murtada muttahari ko littafin Mathnawa na maulana Jalaluddin rumi ko kuma cikin wasu littafai. Da fatan masu sauraro zasu kasance tare da mu a cikin shirimmu nay au. ////…Madallah masu sauraro, idan kuna tare da mu a cikin shirimmu da ya gabaya, a kuma cikin sirar Imam Hassan Akmujtaba (a) dan Fatima (s) diyar manzon All…(s). da muke kawo maku. A shirimmu na karshe mun kawo maku yadda amirulmuminina (A) ya yi zango a wani wuri da...
    Alausa ya ce dakatarwar, wacce ta shafi dukkan nau’o’in manyan makarantun gwamnatin tarayya an yi hakan ne da nufin dakatar da maimaici da barnatar da dukiyar gwamnati, inda za a yi amfani da kudin domin inganta makarantun da ake da su. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Dakarun Sojin Bataliya ta 3 da ke sansanin FOB Rann, a Ƙaramar Hukumar Kala-Balge a Jihar Borno, sun daƙile wani hari da ISWAP suka kai. Bayan tafka artabu, sojojin sun gano gawar ’yan ta’adda uku, ciki har da babban kwamandansu, Amirul Fiya. Gwamnatin Gombe za ta ƙirƙiri sabbin ƙananan hukumomi 13 Majalisar Kano ta dakatar da ciyaman kan zargin karkatar da taki Sojojin sun bayyana cewa wannan nasara ta zama naƙaso ga shugabancin ISWAP a yankin. Rundunar, ta ƙara jadadda ƙudirinta na kawo ƙarshen ta’addanci a Arewa maso Gabas. Sojoji da sauran haɗin gwiwar jami’an tsaro na ci gaba da fatattakar ’yan ta’adda a yankin Arewa Maso Gabas.
    Shugaban Ƙaramar Hukumar Gombe, Barista Sani Ahmad Haruna, ya gode wa Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya saboda ɗaukar matasan da aka horar ƙarƙashin shirin GOSTEC aiki a matsayin cikakkun ma’aikata. Ya ce wannan mataki ya nuna jajircewar gwamnati wajen taimaka wa matasa domin rage zaman banza da kuma ba su damar dogaro da kai. Jama’a sun koka kan rashin kammala aikin titi a Kafanchan Gwamnatin Gombe za ta ƙirƙiri sabbin ƙananan hukumomi 13 Ya ƙara da cewa, yanzu wasu daga cikin matasan sun za su hidimata wa al’umma, saɓanin halin da suke ciki a baya. Ya roƙi matasan su zama masu gaskiya, riƙon amana da kishin ƙasa, inda ya bayyana cewa su ne ginshiƙin ci gaban kowace al’umma. Ɗaya daga cikin...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Majalisar Dokokin Jihar Kano, ta dakatar da Shugaban Ƙaramar Hukumar Rano, Muhammad Nazir Yau, na tsawon wata uku domin gudanar da bincike kan zargin yin amfani da kujerarsa ba bisa ƙa’ida ba. Kansilolinsa sun zarge shi da karkatar da kayayyaki da kuma almundahana wajen tafiyar da dukiyar jama’a. Kullum a Kamaru muke kwana, mu yini a Najeriya – Mazauna ƙauyen Borno Lafiyar Tinubu kalau – Soludo An yanke wannan hukunci ne bayan majalisar ta karɓi rahoto daga kwamitin karɓar koke-koke na jama’a, wanda shugaban marasa rinjaye na majalisar, Hussaini Lawan Cediyar Yangurasa, ya jagoranta a zaman ranar Laraba. Majalisar ta kuma umarci ma’aikatar ƙananan hukumomi da harkokin masarautu ta jihar da ta bai wa mataimakin shugaban ƙaramar hukumar damar riƙon...
    Dubban mazauna garin Kirawa da ke jihar Borno da mayakan Boko Haram suka raba da gidajensu, sun ce yanzu kullum a kasar Kamaru suke saboda gudun harin ’yan Boko Haram cikin dare. Mutanen, wadanda yanzu haka ke samun mafaka a kauyukan kasar ta Kamaru, sun kuma koka da halin kuncin da suke ciki a yanzu. ‘Zan iya shiga mummunan yanayi idan Dangote bai aure ni ba’ Lafiyar Tinubu kalau – Soludo Mazauna yankin shin shaida wa wata kafar yada labarai a ranar Talata cewa tun bayan harin da aka kai ranar Asabar da ya kai ga janye sojoji daga yankin mazauna kauyuka da dama sun bazu a kauyukan da ke kan iyaka da Kamaru. Sun kuma ce a sakamakon haka,...
    Gwamna Umar Namadi ya kaddamar da bikin makon shari’a na shekarar 2025 wanda ƙungiyar Lauyoyi ta Najeriya (NBA) reshen jihar Jigawa ya shirya, inda ya yi kira da a ƙara ƙarfafa bin ƙa’idojin aikin shari’a da hanzarta gudanar da shari’a a duk fadin jihar. A jawabinsa wajen bikin bude taron a Dutse, Gwamna Namadi ya yaba wa shugabannin NBA bisa hadin kai da kwarewarsu wajen gudanar da aiki. “Na shafe watanni da dama ina bin diddigi da sha’awar yadda kuka kafa, tare da gudanar da ayyukan kungiyar  reshen jihar,  cikin haɗin kai da ƙarfafawa, inda ya zama wata gagarumar kafa wacce ke kare muradun aikin lauya da mambobin ƙungiyar a Jigawa  ma da wajen ta.” In ji shi. “Na...
    Wata ’yar siyasa a jihar Bauchi mai suna Aishatu Haruna, ta ce ta shafe shekaru shida tana dakon soyayyar attajirin nan na Afirka, Alhaji Aliko Dangote a ranta, inda ta ce za ta iya shiga mummunan hali idan bai aure ta ba. Ta ce sau uku tana yin mafarkin ta aure shi, kuma ba ta jin za ta iya auren wani ba shi ba a duniya. A cikin wata tattaunawarta da gidan rediyon Albarka da ke jihar Bauchi, Aishatu, wacce aka fi sani da Gimbiyar Mawakan Bauchi, ta kuma ce sau uku tana zuwa kamfanin attajijin na Obajana, ko za ta hadu da shi a can. Ranar Hausa ta duniya: Za a yi gagarumin biki a fadar Sarkin Daura Lafiyar...
    An yi kira ga kwararrun kafafen yada labarai da su tabbatar da madogararsu domin tabbatar da samar da kyakykyawan rahoton abubuwan da ke faruwa a cikin al’umma.   Babban Limamin Masallacin Al-Waheed Central, Imam Mustapha Luqman ne ya yi wannan kiran a lokacin da yake jawabi a wajen taron hadin gwiwa da kungiyar ‘yan jarida ta NUJ ta shirya domin fara taron makon manema labarai na shekara ta 2025, da kuma bikin cika shekara 45 daka guda a Ilorin jihar Kwara   Ya shawarce su da su bi ka’ida wajen gudanar da ayyukansu na yada labarai.   Imam Lukman ya bukaci masu aikin yada labarai da su kasance masu adalci da kyautatawa a tsakaninsu .   A nasa jawabin, Fasto...
    Gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf ya jaddada kudirin gwamnatinsa na samar da kyakkyawar alaka da kafafen yada labarai.   Gwamna Yusuf ya bayyana haka ne a lokacin da ya karbi bakuncin shugaban kungiyar ‘yan jarida ta kasa (NUJ), Kwamared Alhassan Yahaya, da ‘yan majalisar zartaswar NUJ na kasa (NEC) da suka je Kano domin taronsu.   Gwamnan wanda mataimakinsa, Kwamared Aminu Abdussalam Gwarzo ya wakilta, ya yaba wa kungiyar ta NUJ bisa zabar Kano a taron ta na kasa, yana mai jaddada cewa wannan shaida ce ta kyakkyawar alakar aiki tsakanin gwamnatin jihar Kano da kafafen yada labarai.   Ya ce gwamnatinsa ta samu gagarumar nasara wajen inganta rayuwar jama’a, da kuma tabbatar da cewa dole ne a cika...
    Kungiyar Manyan Ma’aikatan Jami’o’in Najeriya (SSANU), Jami’ar Jihar Taraba Jalingo, ta bayar da wa’adin makonni biyu ga gwamna Agbu Kefas da shugabannin jami’ar da su gana da ita ko kuma ta shiga yajin aikin.   A cikin sanarwar da aka fitar a karshen taron majalisar da aka gudanar a ranar 7 ga wata. Agusta 2025, kuma shugaban kwamitin, Comr. Bitrus Joseph Ajibauka, da sakatare, Mamki Joshua Atein, kungiyar ta bayyana rashin jin dadin ta kan yadda gwamna Kefas ya kasa mutunta yarjejeniyar da kungiyar ta cimma da Gwmanati a wata ganawa da shugabannin kungiyar tare da samar da samfuri da tsarin biyan basussukan da ake bin su a makon farko na watan Fabrairu, 2025, sun bayyana matakin da gwamnan ya...
    Biyo bayan wani rahoto da ma’aikatar lafiya ta tarayya ta fitar na cewa sama da likitoci 16,000 ne suka bar Najeriya a cikin shekaru bakwai da suka gabata domin neman aiki a wasu kasashe, gwamnatin tarayya ta kaddamar da wani sabon shiri na cike gurbin da likitocin suka haifar.   Da yake zantawa da manema labarai a Katsina, Shugaban Hukumar Kula da Ilimi ta Kasa (TETFund), Alhaji Aminu Bello Masari, ya ce hukumar ta kaddamar da wani shiri na musamman domin horar da karin likitoci, ma’aikatan jinya, masu harhada magunguna da kwararrun dakin gwaje-gwaje a manyan makarantun kasar nan.   Ya ce tuni hukumar ta TETFUND ta zuba sama da Naira biliyan 100 a manyan makarantu goma sha takwas domin...
    Wani sabon rikici ya barke a jihar Sokoto inda ‘yan bindiga sun kai hari a wani masallaci a kauyen Marnouna da ke karamar hukumar Wurno, inda suka kashe akalla mutum daya tare da yin awon gaba da wasu da ba a tantance adadinsu ba a lokacin da ake sallar isha.   Shugaban jam’iyyar APC reshen jihar Sokoto, Alhaji Isah Sadik Achida, wanda ya fito daga yankin ya tabbatar da faruwar harin inda ya jaddada cewa maharan sun kuma kashe shugaban kungiyar masu sayar da babura na yankin a yayin farmakin.   Achida ya ci gaba da cewa, kwana biyu kacal kafin harin masallacin, ‘yan bindigar sun kai farmaki kauyuka biyu da ke makwabtaka da su, Gidan Taru da Kwargaba, inda...
    Gwamnatin jihar Katsina ta ce shirye-shirye sun kankama domin bin sahun sauran sassan duniya a yayin bikin Ranar Hausa ta Duniya a za ake gudanarwa ranar 26 ga watan Agustan kowacce shekara. Shugaban Hukumar Kula d Tarihi da Al’adu ta jihar, Dr Kabir Ali-Masanawa ne ya bayyana hakan yayin wani jawabi ga manema labarai a Katsina ranar Talata. Ya ce za a yi taron ne a Fadar Sarkin Daura da ke jihar, kuma ana sa ran manyan baki daga kasashe akalla 24 za su halarta. Masanawa ya ce wannan shi ne karo na farko da gwamnati ta shiga cikin shirya bikin, inda ya ce hatta Gwamnan jihar, Dikko Umaru Radda ya tsaya tsayin daka wajen ganin bikin ya yi nasara....
    Shugaban EFCC, Ola Olukoyede, ya ce, “Idan ba a zarge ni wajen binciken gwamnoni da ministocin jam’iyyar da ke mulki ba, bai kamata a zarge ni idan na binciki ’yan hamayya ba.” Duk da haka, mutane da dama a kafafen sada zumunta sun nuna shakku, tare da tambayar dalilin da ya sa EFCC ba ta ɗauki mataki kan manyan ’yan siyasa na jam’iyyar APC kamar tsohon Gwamnan Delta Ifeanyi Okowa, tsohon Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje, da tsohon Gwamnan Kogi Yahaya Bello ba. Wasu sun zargi EFCC da yin aiki ƙarƙashin ikon gwamnatin da ke mulki, yayin da wasu suka yi tsokaci ta hanyar buƙtar shugaban EFCC ya bayyana bayanan asusun bankinsa na yanzu. Daga kanmu, magana ta ƙare....
    Babban kwamandan sojojin kasar Iran Manjo Janar Amir Hatami ya tabbatar da cewa, Isra’ila da Amurka ne suka bukaci  a tsagaita bude wuta cikin gaggawa bayan da suka fuskanci martani mai tsanani a lokacin da suka kaddamr da hare-hare kan kasar Iran. A yayin da yake karbar bakuncin babban kwamandan rundunar tsaron kasar a Afirka ta Kudu, Janar Hatami ya ce, hukumomin Isra’ila da Amurka sun yi amfani da dukkan karfinsu wajen kai wa Iran hari, amma sun kasa cimma burinsu. Har ila yau, ya bayyana matakin da Afirka ta Kudu ta dauka  na shigar da kara kan Haramtacciyar Kasar Isra’ila a kotun kasa da kasa a matsayin wata babbar Jarunta, yana mai jaddada cewa tarihi zai tabbatar da wannan...
    Ministan Ruwa na Habasha Habtamu Etfa ya jaddada cewa, babbar madatsar ruwa ta kasarsa amfanin dukkanin kasashen yankin ne. Etfa ya bayyana hakan ne a wani sako da ya wallafa a shafinsa na Facebook, kamar yadda shafin yanar gizo na Ethiopian Monitor ya bayyana cewa, ” kwararar kogin Blue Nile ya karu a lokacin noman rani, yayin da muka ga raguwar ambaliya da kuma jinkiri fiye da wata guda.” Ya jaddada cewa abin da muke hasashe kuma muke bayyanawa  yau da kullun ya tabata a aikace.” Ya kara da cewa, “Grantin Renaissance Dam na Habasha ba kawai ya kara yawan filayen noma da ake nomawa a kasashen da ke gabar kogin Blue Nile ba, har ma ya taimaka wajen kare...
    Bankin Duniya ya amince da bayar da dala miliyan 300 domin aiwatar da wani sabon shiri da zai inganta rayuwar ’yan gudun hijira da kuma al’ummomin da suka ba su matsugunni a Arewacin Nijeriya. Bankin ya bayyana cewa a ƙarƙashin shirin mai suna Solutions for the Internally Displaced and Host Communities Project wato SOLID, wanda aka amince da shi a ranar 7 ga Agusta, za a lalubo hanyoyin da za a bi wajen taimakon ’yan gudun hijira, da ma garuruwan da suke rayuwa a ciki. Ya bayyana cewa shirin SOLID zai ruɓanya ƙoƙarin da gwamnati ke yi da ma wanda sauran abokan hulɗa suka riga suka gudanar, ciki har da Shirin Farfado da Yankunan Da Rikici Ya Shafa (MCRP). Haka...
    Gwamnan jihar Anambra, Farfesa Charles Soludo, ya ce ranar Litinin ya ziyarci Shugaban Kasa Bola Tinubu, kuma sabanin yadda ake ta rade-radi, shugaban na nan cikin koshin lafiya kuma babu abin da ke damun shi. A ’yan kwanakin nan dai ana ta samun jita-jitar cewa shugaba Tinubu na can kwance magashiyyan yana fama da rashin lafiya a daidai lokacin da aka shafe sama da mako guda ba a ji motsin shi ko an gan shi a wajen wani taro ba. DAGA LARABA: Yadda sinadaran dandanon abinci ke yin illa ga lafiya Fursunoni 16 sun tsere daga gidan yarin Keffi Sai dai da yake zantawa da ’yan jaridar Fadar Shugaban Kasa da ke Abuja bayan ya gana da shi, Gwamnan ya...
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba A yau, yawancin mutane suna amfani da sinadaran dandano wajen girki domin ƙara wa abinci ɗanɗano da ƙamshi. Amma, binciken masana ya nuna cewa ana yawan amfani da su fiye da yadda ake bukata, musamman irin waɗanda aka sarrafa a masana’antu. Wannan rashin kiyaye ƙa’ida yana iya jawo matsaloli ga lafiya. Sau da yawa mutane kan manta cewa a cikin waɗannan sinadarai akwai gishiri mai yawa da wasu ƙarin abubuwan da idan aka tara su a jiki na dogon lokaci, suna iya haifar da illa. NAJERIYA A YAU: Yadda matasa ke bayar da gudunmawa ga ci-gaban al’umma DAGA LARABA: Me Ke Sa Matasa Zama Karnukan Farautar ‘Yan Siyasa A Kafafen Sadarwa Na Zamani?...
    Nijeriya da Isra’ila sun sake jaddada aniyarsu ta karfafa haɗin gwiwar tsaro a fannoni daban-daban, kamar batun yaƙi da ta’addanci, musayar bayanan sirri, samar da kuɗin tsaro da kuma bayar da horo na musamman ga jami’an tsaron Nigeria. Hakan na ƙunshe cikin wata sanarwar haɗin gwiwa wadda Ƙaramar Ministar Harkokin Wajen Nijeriya, Bianca Odumegwu-Ojukwu, da Mataimakiyar Ministan Harkokin Waje ta Isra’ila, Sharren Haskel-Harpaz suka fitar bayan wani taro na musamman da suka gudanar a Abuja. Sanarwar, wadda mai magana da yawun Ofishin Ƙaramar Ministar Harkokin Wajen, Dokta Magnus Eze ya fitar, ta ce taron ya nuna alaƙa mai ɗorewa da muhimmanci tsakanin bangarorin biyu. A  yayin taron, wakilan bangarorin biyusun tattauna batutuwan da suka shafi tsaro a duniya, musamman yaƙi...
    Da yake tabbatar da faruwar lamarin ga LEADERSHIP a ranar Talata, Kakakin Rundunar ’Yansandan Jihar Bauchi, CSP Ahmed Wakil, ya ce rundunar ‘yansandan ta samu kiran waya da misalin karfe 9:20 na safe daga CLO, inda ya ce Chukwuebuka mai lambar jiha BA/25A/2069 bai farka ba daga barcinsa, yayin da sauran ’yan uwansa Kiristocin ke shirin tafiya wurin bauta a ranar Lahadi.   “CLO ya je don ya tayar da shi daga barci amma sai ya gano cewa, ba ya numfashi, nan take ya kai rahoton lamarin ga hedikwatar ‘yansanda ta Dambam,” in ji Wakil.   Biyo bayan umarnin kwamishinan ‘yansandan jihar Bauchi, CP Sani Omolori-Aliyu, jami’in ‘yansanda na sashen ya jagoranci tawagarsa zuwa wurin.   An garzaya da Chukwuebuka...
    Ana fargabar cewa wasu fursunoni 16 sun tsere daga gidan yarin Keffi da ke Jihar Nasarawa bayan wani kwantan bauna da suka yi wa gandirebobi. Wata sanarwa da mai magana da yawun Hukumar Kula da Gidajen Gyaran Hali a Nijeriya, Umar Abubakar, ta ce fursunonin da ke gidan sun yi wa ma’aikatan da ke tsaronsu rubdugu, lamarin da ya bai wa mutane 16 damar guduwa a safiyar wannan Talatar. An kama ɗan shekara 18 kan zargin fashi da makami a Gombe An kama basarake kan zargin yi wa ’yar shekara 12 fyaɗe a Gombe Sanarwar ta ce biyu daga cikin jami’ai biyar da suka ji rauni a yayin harin na cikin mawuyacin hali, kuma yanzu haka ana duba lafiyarsu a...
    Da aka tambaye shi dalilin da ya sa ya fito ƙarara ya goyi bayan shugaban ƙasa wanda ba a cikin jam’iyyarsu yake, Soludo ya ce goyon bayansa ga Tinubu ba sabon abu ba ne.   “An samar da waɗannan huluna tun lokacin da Shugaban Ƙasa ya ziyarci Jihar Anambra kuma kun ga allunan talla da sauran abubuwa da ke bayyana cewa masu ra’ayin kowa ci gaba suna aiki tare ne da juna,” in ji Soludo.   “Bayan haka, wannan wata babbar manufa ce da na yi imani da ita sosai, cewa ya kamata dukkan jam’iyyun siyasa da ke ikirarin ra’ayin ci gaba su haɗu a ƙarƙashin wata babbar ƙawance don zurfafa tunani da kawo ci gaba ba kawai a tafarkin...
      A matsayinta na mai jagorantar zamanantar da duniya, Sin tana gabatar da ilimin da ya danganci fasahar zamani ga kasashen Afrika domin su tsaya da kafarsu tare da samun kyakkyawar makoma. Wannan zai samarwa matasa dama mara iyaka ta fadada ilimi da fahimta da samun aikin yi da zai kai su ga yin kirkire kirkiren da za su tallafawa al’ummar da cike gibin dake akwai tsakanin masu ilimi da marasa shi. Kuma yayin da duniya ta dunkule wuri guda saboda fasahohin zamani, matasa a nahiyar Afrika za su kara fahimtar yanayin da duniya take cike da fahimtar juna da kara wa juna sani tsakaninsu da takwarorinsu na kasashen waje, lamarin da zai share fagen gogayyar ilimi da samar da...
    Rundunar ’Yan Sandan Jihar Gombe ta cafke wani basarake, Mohammed Tukur mai shekaru 55, a kauyen Sabon Gari da ke yankin Zambuk na Ƙaramar Hukumar Yamaltu Deba, bisa zargin yi wa wata yarinya ’yar shekara 12 fyaɗe. Mai magana da yawun rundunar, DSP Buhari Abdullahi, ya tabbatar da faruwar lamarin cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Talata. EFCC ta saki Tambuwal Bankin Duniya zai kashe $300m domin inganta rayuwar ’yan gudun hijira a Arewacin Nijeriya Ya ce abin ya faru ne da misalin ƙarfe 9:00 na daren ranar 9 ga Agusta, 2025, lokacin da ake zargin ya yaudari yarinyar wadda ya kaita wani wuri da babu idon jama’a ya aikata ta’asar. Bayan samun rahoton faruwar lamarin ne, jami’an...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Bankin Duniya ya amince da bayar da dala miliyan 300 domin aiwatar da wani sabon shiri da zai inganta rayuwar ’yan gudun hijira da kuma al’ummomin da suka ba su matsugunni a Arewacin Nijeriya.  Bankin ya bayyana cewa a ƙarƙashin shirin mai suna Solutions for the Internally Displaced and Host Communities Project wato SOLID, wanda aka amince da shi a ranar 7 ga Agusta, za a lalubo hanyoyin da za a bi wajen taimakon ’yan gudun hijira, da ma garuruwan da suke rayuwa a ciki. Dasuki: Kotu ta bai wa Gwamnatin Tarayya wa’adin kammala shari’ar kuɗin makamai Nijeriya ta sake ƙulla alaƙar tsaro da Isra’ila Ya bayyana cewa shirin SOLID zai ruɓanya ƙoƙarin da gwamnati ke yi da ma wanda...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Ministan harkokin wajen kasar Armenia Ararat Mirzoyan ya tabbatarwa JMI kan cewa yarjeniyar sulhu da suka cimma da kasar Azairbaijan ba zai shafi bukatun kasar Iran ko kuma hanata wani hakkinta a yankin kaukas ba. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto ministan harkokin wajen kasar Armenia yana fadar haka a safiyar yau Talata, ta wayar tarho a lokacinda yake zantawa da tokwaransa na kasar Iran Abbas Aragchi. A cikin wannan makon ne shugaban kasar Amurka Donal Trump ya jagoranci yarjeniyar zaman lafiya tsakanin kasashen Azarbaijan dangane da yankin karabakh a fadar White House. Sannan akwai labarin cewa za’a gina wani babban titi wanda zai ratsa kasashen bitu. Kasashen dai suna makobtaka da kasar Iran, don haka dangantakarsu...
    Nijeriya da ƙasar Isra’ila sun sake jaddada aniyarsu ta ƙarfafa haɗin gwiwar tsaro a fannoni masu muhimmanci kamar yaƙi da ta’addanci, musayar bayanan sirri, samar da kuɗin tsaro da kuma horaswa ta musamman. Hakan na ƙunshe cikin wata sanarwar haɗin gwiwa wadda Ƙaramar Ministar Harkokin Wajen Nijeriya, Ambasada Bianca Odumegwu-Ojukwu, da Mataimakiyar Ministan Harkokin Waje ta Isra’ila, Sharren Haskel-Harpaz suka fitar bayan wani taro na musamman da suka gudanar ranar Litinin a Abuja. Tinubu na amfani da EFCC ya muzguna wa ’yan adawa — Atiku Amurka da China sun dakatar da harajin da suka ƙaƙaba wa juna Sanarwar, wadda mai magana da yawun Ofishin Ƙaramar Ministar Harkokin Wajen, Dokta Magnus Eze ya fitar, ta ce taron ya nuna alaƙa mai ɗorewa...
    Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, ya zargi gwamnatin Bola Tinubu da amfani da Hukumar EFCC wajen yi wa masu adawa da ita barazana. Saƙon da ɗan takarar shugaban ƙasa a Zaɓen 2023 ya wallafa wannan Talatar a shafinsa na X, na zuwa ne bayan tsare tsohon Gwamnan Sakkwato, Sanata Aminu Waziri Tambuwal da EFCCn ta yi. Amurka da China sun dakatar da harajin da suka ƙaƙaba wa juna Harin ’yan fashi: An rufe Federal Poly Bauchi Bauchi A cewar Wazirin Adamawa, “dalilin da EFCC ta tsare tsohon Gwamnan Sakkwato, Sanata Aminu Waziri Tambuwal, shi ne saboda yana cikin jam’iyyar adawa ta haɗaka. “Wannan yana ƙara nuna yadda gwamnatin Tinubu ke ci gaba da yaɗa manufofinta na musgunawa, tsoratarwa, da...
    Hakan ya gudana a ƙarƙashin jagorancin hukumomin da ke lura da yadda ake tafiyar da gasar da kuma kare haƙƙin masu amfani da kaya (FCCPC), hukumar kula da tallace-tallace ta Nijeriya (ARCON), da hukumar kula da harkokin caca da wasanni ta Jihar Legas (LSLGA). Zaɓen ya kasance cikin gaskiya da adalci, inda waɗanda yi nasara suka bar Naira 10,000 a cikin asusun ajiyarsu na Stanbic IBTC ko @ease Wallet har tsawon kwanaki 30. Daga mata ‘yan kasuwa, zuwa ɗalibai, har zuwa ma’aikatan da suka yi ritaya, waɗanda suka yi nasara yanzu suna iya biyan kuɗin makaranta, fara ƙananan sana’o’i, ko kuma tafiyar da buƙatun gidajensu cikin sauƙi. An ƙara sanya wasu mutane takwas cikin farin ciki a zaɓen babbar garaɓasar...