Matsalar tsaro na iya hana mu ci gaba da rijistar masu zabe a Borno – INEC
Published: 15th, August 2025 GMT
Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) ta ce matsalar tsaro na iya hana ta gudanar da aikin rijistar masu zabe a kananan hukumomin jihar Borno guda hudu.
Kananan hukumomin da lamarin zai iya shafa su ne Abadam, Guzamala, Marte da Kala-Balge.
Jama’a ba sa yaba wa kokarinmu na hana aikata laifi – Babban Sufeton ’Yan Sanda NAJERIYA A YAU: Halin ƙuncin da ’yan fansho ke ciki a NajeriyaBayanin hakan dai ya fito ne daga bakin Kwamishinan Zabe na jihar, Abubakar Ahmad Ma’aji a jawabin sa ga manema labarai a Maiduguri, a wani vangare na shirye-shiryen fara gudanar da aikin rijistar masu kada kuri’a a ranar Litinin da ke tafe.
A cewar shi, INEC ta mayar da rijistar masu zaben a karamar hukumar Abadam zuwa kan hanyar Baga, daura da ofishin Yerwa Peace.
Kazalika, ya ce a karamar hukumar Guzamala an mayar da wurin yin rajistar sashen kashe gobara na rukunin gidaje 1,000.
Ya ce sauran kananan hukumomin kamar karamar hukumar Kala-Balge an mayar da aikin ya koma zuwa makarantar firamare ta Goni Kachalari da ke birnin Maiduguri.
Shi kuma aikin rijistar masu kada kuri’a na qaramar hukumar Marte an mayar da shi ya zuwa Kachamai, wadanda dukkansu suna cikin birnin Maiduguri ne.
Don haka kwamishinan ya yi kira ga mutanen kananan hukumomin da su yi hakuri da wannan canji da aka samu, inda ya ce an yi ne da kyakkyawar manufar da duk wanda abin ya shafa zai samu rijistarsa cikin kwanciyar hankali.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: matsalar tsaro rijistar masu
এছাড়াও পড়ুন:
Zulum ya ba kowanne ɗalibin Borno da ke karatu a Indiya tallafin N500,000
Gwamnan Jihar Borno, Babagana Umara Zulum, a ranar Litinin ya ziyarci ɗaliban jihar da ke karatu a ƙasar Indiya, inda ya ba kowannen su tallafin Naira 500,000.
Gwamnan, wanda ke ziyarar aiki a Indiya, ya fara ganawa da waɗanda suka ci gajiyar shirin tallafin karatu na jihar a Jami’ar Sharda da ke Noida.
Ko sisi ba a biya ’yan bindiga ba kafin su saki ɗaliban da suka sace – Gwamnan Kebbi Kotu ta yanke wa mutum 5 hukuncin rataya a Oyo saboda aikata kisan kaiYa tabbatar musu da jajircewar gwamnatinsa wajen kula da walwalarsu domin samun nasarar karatunsu, sannan ya gargade su da su mai da hankali kan karatun nasu.
Ya ce, “Na zo nan yau saboda dalili ɗaya, don tunatar da ku cewa gwamnatin Jihar Borno na alfahari da ku, wadda kan haka take saka hannun jari a kan makomarku.
“Kuna da muhimmanci ga ci gaba da sake gina jiharmu. Ilimin da ƙwarewar da kuke samu a nan zai amfani, ga jama’arku da kuma kannenku masu zuwa,” in ji Zulum.
Gwamna Zulum ya bayar da tallafin kuɗi na Naira 500,000 ga kowane ɗalibi, abin da ya jawo farin ciki matuƙa ga ɗaliban.
Daga nan, gwamnan ya tafi zuwa yankin Lucknow a ƙasar Indiya, inda ya yi irin wannan taimako ga ɗaliban Jihar Borno a Jami’ar Integral.
Ya kuma ba da umarni a bai wa waɗanda suka ci gajiyar tallafin karatu na Jihar Borno da ke karatu a ƙasar Malesiya irin wannan tallafin kuɗi, yana mai jaddada alkawarin yin adalci ga dukkan ɗaliban da ke amfana da shirin tallafin karatu.
Ɗaliban sun yaba wa gwamnan saboda ziyarar, inda bayyana shi a matsayin shugaba mai tausayi da kulawa.
A cikin tawagar gwamnan akwai Babban Sakataren Fadar Gwamnatin Borno, Barista Mustapha Busuguma da Babban Sakataren Hukumar BOGIS, Injiniya Adam Bukar Bababe.