UBEC Ta Kaddamar Da Makarantun Zamani 21 A Sassan Nijeriya
Published: 15th, August 2025 GMT
“Sama da yara miliyan 10.1 ne ba su kai makaranta, kashi 70 masu zuwa makarantar kuma ba su da dabarun koyo, kuma fiye da kashi 60 na malaman firamare na gwamnati ba su da ilimin dijital,” in ji ta
Da take yaba wa gwamnatin Koriya ta Arewa bisa tallafin da ta samu ta hannun hukumar raya kasashe ta KOICA, Garba ta ce wannan hadin gwiwa ya taimaka wa kasar wajen sake tunanin koyo, tare da dakile rarrabuwar kawuna, da bai wa makarantu da malamai kwarin gwiwa domin samar da sauyi mai dorewa.
Mataimakin Babban Sakatare na UBEC (Technical), Mista Razak Akinyemi Olajuwon, ya bayyana cewa, wannan shiri ya kara wa malamai kwarin gwiwar yin amfani da su da bunkasa abubuwan da ke cikin ICT da inganta samun nagartattun abubuwan koyarwa da fasahar sadarwa a cikin ajujuwa.
Manajan ofishin KOICA na Nijeriya Dabid Nkwa, ya ce a cikin shekaru biyar da suka gabata aikin ya inganta ilimi a Nijeriya, musamman sakamakon koyo a matakin farko na ilimi.
NELFUND Ta Raba Bashin Naira Biliyan 86.3 Ga Dalibai 450,000
susun Ba Da Lamuni Na Ilimi na Nijeriya ya sanar da cewa ya zuwa yanzu adadin dalibai 449,039 ne suka ci gajiyar shirin bayar da lamuni na dalibai tun bayan kaddamar da shirin a ranar 24 ga Mayu, 2024.
Dangane da sabon rahoton halin yau da kullun da aka fitar a ranar Litinin, 11 ga Agusta, 2025, shirin ya fitar da jimillar Naira biliyan 86,347,458,384 a ranar 6 ga Agusta, 2025.
Ta ce kudaden sun hada da Naira 47,629,338,384 da aka biya kai tsaye ga cibiyoyi 218 a matsayin kudin karatu da kuma Naira 38,718,120,000 da aka bai wa dalibai a matsayin alawus-alawus.
Rahoton ya kara da bayyana cewa dalibai 731,140 ne suka yi rajista a dandalin rancen, inda 720,732 suka samu nasarar samun lamuni, wanda ke wakiltar kashi 98 na nasarar aikace-aikacen.
Bayanai daga dashboard sun nuna karuwar yau da kullun na 933 a cikin adadin masu yin rajista da kuma karin masu nema 1,094.
NELFUND ta lura cewa “shirin yana ba da Ajandar Renew Hope na Shugaba Bola Tinubu na karfafa kowane dalibin Nijeriya ta hanyar samun tallafin ilimi.”
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Yaushe Lamine Yamal Zai Lashe Kyautar Ballon d’Or?
Sai dai duk da cewa Ousmane Dembele na kungiyar kwallon kafa ta PSG ne ya lashe gasar- Yamal ya samu nasarar kyautar gwarzon matashin dan wasa na Ballon d’Or karo na biyu a jere.
Lamine Yamal, ya kasance daya daga cikin fitattun ‘yanwasa mafiya farin jini tsakanin masoya kwallon kafa, musamman ma matasa saboda karancin shekarunsa da kuma yadda yake buga wasa cikin raha.
Shekara da shekaru, duniya ta dauka cewa zama fitacce a fagen kwallon kafa na bukatar jajircewa da sadaukarwa. Saboda kafin dan wasa ya iya lashe wannan kyauta sai ya yi aiki tukuru.
Sai dai duk da nuna kuruciyarsa, hakan bai hana Yamal cimma burinsa a fagen kwallon kafa ba. A baya ya bayyana cewa: yana da burin samun Ballon d’Or masu yawa idan ya samu dama.
Matasa da dama sun so Yamal ya lashe Ballon d’Or a wannan shekara, musamman irin kokarin da ya yi a bara, da kuma lashe kyautar gwarzon matashin danwasa da ya yi a bara. Kuma rashin samun kyautar ba ta yi wa matasa da dama dadi ba.
Ana ganin samun nasara a tawagar ‘yan wasan kasar Sifaniya zai fi ba shi damar lashe kyautar fiye da kungiyarsa ta Barcelona, amma idan har Barcelona ta iya lashe gasar cin kofin zakarun turai tabbas zai iya lashewa.
Amma kuma akan fifita nasarar da dan wasa ya yi a kasarsa fiye da kungiyar da yake bugawa wasa, kuma a bayyane take Kofin Duniya na daya daga cikin manyan abubuwan da zai sa mutum ya lashe kyautar.
Saboda haka idan har Sifaniya ta lashe kofin duniya a shekara mai zuwa ta 2026, Yamal zai iya samun kyautar Ballon d’Or. Kasancewar a yanzu yadda yake da cikakken gurbi a tawagar kasar, babu yadda za a yi Sifaniya ta ci kofin ba tare da kwallayensa ba.
ShareTweetSendShare MASU ALAKA