Aminiya:
2025-11-27@21:36:13 GMT

Ambaliya: Magidanta da dama sun rasa muhallinsu a Yobe

Published: 15th, August 2025 GMT

Ruwan sama kamar da bakin ƙwarya da aka yi a garin Potiskum a daren Juma’a zuwa safiyar yau Juma’a ya haifar da ambaliya, wanda ya haifar da tashin hankali ga mazauna garin.  

Kamar yadda majiyar da ke garin ta shaidawa Aminiya cewa, ruwan sama kamar da bakin ƙwarya da aka fara shi tun kusan tsakar daren Alhamis ya yi sanadiyyar rugujewar gidaje da dama, inda wasu gine-gine suka ruguje ƙarƙashin ruwan.

An sake ceto matafiya 10 da aka sace a Kogi Tinubu ya bar Abuja zuwa Japan da Brazil

Sakamakon ambaliyar ruwan ya sa mazauna wasu unguwanni da dama suka rasa matsugunansu inda suke hijira ya zuwa gidajen ‘yan uwa da makarantu, inda suke kokawa kan yadda iftala’in ta afku.

Wannan ambaliyar ruwa da ta faru rahotanni na nuna cewa, wasu gine-gine sun ruguje tare da rushewar maƙabarta yayin da wasu kuma suka nutse kamar yadda aka ambata a baya.

Nura Badamasi da ke unguwar bayan tsohon gidan gyaran hali wanda ɗaya ne daga cikin waɗanda abin ya shafa ya tabbatarwa da Aminiya cewa, bai fita da komai ba daga cikin gidansa sai da rigar da ke jikinsa kaɗai sauran kayayyakinsa da na iyalansa duka babu domin ambaliyar ta tafi da su da muhallinsa gaba ɗaya abin ba’a cewar komai sai dai Allah SWT ya kawo musu ɗauki.

Don haka ne ma yake roƙon gwamnatin Jihar Yobe da Ƙaramar hukumar Potiskum da su kawo musu ɗauki da kuma taimaka musu domin shawo kan matsalar ambaliyar ruwan da a kullum suke fuskantar barazana akai, kana su kuma kawo musu ɗaukin gaggawa don tallafa musu.

Unguwanni da wannan ambaliyar tafi shafa sun haɗa da: Unguwar Jigawa da Bayan tsohon gidan yari da Unguwar makafi da wasu unguwannin gabas da Kasuwa.

উৎস: Aminiya

এছাড়াও পড়ুন:

An sako ɗalibai 25 da ’yan bindiga suka sace a Kebbi

Rahotanni na cewa ɗalibai 25 da ’yan bindiga suka sace yayin harin da suka kai a Makarantar Sakandiren Mata da ke garin Maga a Jihar Kebbi sun shaƙi iskar ’yanci.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Gwamnati Za Ta Biya Wasu Kudaden Ariyas Ga Masu Fensho Wannan Wata
  • NAJERIYA A YAU: Amafani Da Karfin Soji Ko Tattaunawa Ne Zai Kawo Matsalar Tsaro A Najeriya?
  • Juyin mulki ya rutsa da Jonathan a Guinea-Bissau
  • Super Falcons za su ƙaurace wa wasannin Nijeriya saboda riƙe musu alawus
  • Tinubu ya ayyana dokar ta-ɓaci kan matsalar tsaro
  • An sako ɗalibai 25 da ’yan bindiga suka sace a Kebbi
  • An buɗe wasu makarantu domin ci gaba da jarawaba a Katsina
  • ’Yan bindiga sun sace mutum 8 a Kano
  • Abin da ya sa nake haxa harkar fim da harkar karatu-Nabila
  • Amarya ta yi wa angonta yankan rago bayan kwana 3 da aurensu a Katsina