An sake ceto matafiya 10 da aka sace a Kogi
Published: 15th, August 2025 GMT
Jami’an tsaro sun kuɓutar da wasu fasinjoji 10 da aka yi garkuwa da su a hanyar Itobe – zuwa Ochadamu – Anyigba a Ƙaramar hukumar Ofu a Jihar Kogi.
Fasinjojin da aka kuɓutar an yi garkuwa da su ne a ranar 11 ga watan Agusta a ƙauyen Ugbakpedo da ke kan titin, lokacin da wata mota ta yi wa fasinjojin kwanton ɓauna.
Jami’an tsaron da suka haɗa da: ’yan sanda da ’yan banga da mafarautan yankin sun bayyana cewa sun afkawa dajin da ke yankin kafin ceto matafiyan.
“A ranar 13 ga watan Agusta da misalin ƙarfe 4:30 na Asubahi ne yayin wani gagarumin farmaki tare da amfani da hayaƙi mai sa hawaye, masu garkuwa da mutanen suka yi watsi da waɗanda kama suka gudu.
“An ceto dukkan mutane 10 da aka yi garkuwan da su ba tare da sun samu rauni ba, kuma tuni aka haɗa su da iyalansu,” in ji wani rahoton tsaro kan lamarin.
Rahoton jami’an tsaro ya ƙara da cewa, ana ƙara tattara bayanan sirri da sa ido da kuma ganowa tare da yunkurin kama waɗanda ake zargin da suka tsere inda zargin masu garkuwa da mutane ne.
Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ’yan sandan Jihar (PPRO), SP William Aya ya tabbatar da ceto matafiya da aka yi garkuwa da su a ranar Juma’a a Lokoja.
Ya ce, an kuɓutar da matafiyan ne tare da haɗin gwiwa jami’an tsaro, tare da ‘yan banga da mafarauta wanda ya yi nasarar ceto waɗanda aka sace.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: yan banga Yan Sanda
এছাড়াও পড়ুন:
Tabarbarewar Tsaro na Barazana ga Siyasar Ƙasar Nan Gabanin Zaɓen 2027-Ado Doguwa
Daga Salihu Tsibiri
Tsohon shugaban masu rinjaye na Majalisar Wakilai, Alhassan Ado Doguwa, ya bayyana tabarbarewar tsaro da ake fuskanta, wato ta’addanci, garkuwa da mutane da kuma hare-haren ’yan bindiga, a matsayin barazana ga siyasar ƙasar nan gabanin zaɓen 2027.
Ya yi wannan tsokacin ne a jawabinsa yayin bude zaman taron musamman na yini biyu da Majalisar Wakilai ta shirya kan halin tsaro da ƙasar ke ciki.
Alhassan Ado Doguwa, wanda ya yaba da ayyukan da hukumomin tsaro ke ci gaba da gudanarwa, ya ce halin da Arewa ke ciki abin takaici ne ƙwarai, la’akari da yawan mutanen da ke hannun masu garkuwa da kuma waɗanda ke rayuwa cikin tsananin rashin tabbas.
Tsohon shugaban ya jaddada cewa duk da cewa su ma gwamnoni suna da alhakin tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin jama’a tare da gwamnatin tarayya, lokaci ya yi da za a duba batun tsaro a matsayin barazana da ba ta da alaƙa da jam’iyya, addini ko ƙabila.
Ya kara da cewa idan matsalar tsaro ta ci gaba da ta’azzara, akwai bukatar a rufe majalisa gaba ɗaya tare da ayyana dokar ta-baci, har sai an ɗauki matakin gaggawa don kare ƙasar daga halin da take ciki.
A nasa bangaren, shugaban kwamitin majalisar kan harkokin ’yan sanda, Makki Abubakar Yalleman, ya bayyana tsaro a matsayin alhakin kowa, inda ya yaba wa umarnin shugaban ƙasa na janye ’yan sanda daga wasu manyan mutane domin ƙara ƙarfi a yaki da laifuka a fadin ƙasar.
Sai dai Makki Yalleman ya yi kira da a samar da isasshen kuɗi da na’urorin zamani domin inganta ƙwarin gwiwa da ƙwarewar rundunar ’yan sandan Najeriya a yakin da take yi da ta’addanci, garkuwa da mutane da kuma ’yan bindiga.
A nasa bangaren, shugaban marasa rinjaye na majalisar, Kingsley Chinda, ya danganta matsalolin tsaro da ake fuskanta ga gazawar bangarorin gwamnati uku wajen tabbatar da bin tanade-tanaden kundin tsarin mulki, musamman kan ta’addanci, garkuwa da mutane, ’yan bindiga da kuma masu yi wa gwamnati tawaye.