Aminiya:
2025-11-27@21:07:12 GMT

NAJERIYA A YAU: Halin ƙuncin da ’yan fansho ke ciki a Najeriya

Published: 15th, August 2025 GMT

More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba

A wasu jihohin Arewacin Najeriya, masu karɓar fansho suna cikin mawuyacin hali sakamakon ƙarancin kuɗin da ake biyansu duk wata.

Wasu daga cikinsu sun bayyana yadda suke karbar naira dubu 5 a kowane wata a matsayin kudin fansho bayan kwashe shekaru suna aiki.

NAJERIYA A YAU: Yadda matasa ke bayar da gudunmawa ga ci-gaban al’umma DAGA LARABA: Yadda sinadaran dandanon abinci ke yin illa ga lafiya

Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi nazari ne kan irin halin da ’yan fansho ke ciki a wasu jihohin Arewacin Najeriya.

Domin sauke shirin, latsa nan

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Yan fansho Arewacin Najeriya

এছাড়াও পড়ুন:

Rasuwar Sheikh Dahiru Bauchi ta bar babban gibi a Najeriya – Tinubu

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya bayyana kaduwa da rasuwar fitaccen malamin addinin Musulunci kuma jagoran Tijjaniyya, Sheikh Dahiru Usman Bauchi.

Fitaccen malamin ya rasu a Bauchi ranar Alhamis yana da shekaru 101.

Abubuwa 20 da ya kamata ku sani game da Sheikh Dahiru Bauchi Ɗan bindiga ya harbe sojoji 2 a fadar shugaban Amurka

A cikin wata sanarwa da Kakakin shugaban, Bayo Onanuga, ya fitar, Tinubu ya bayyana Sheikh Dahiru Bauchi a matsayin jagoran da ya sadaukar da rayuwarsa wajen koyarwa, wa’azi da jagorantar al’ummar Musulmi.

Tinubu ya ce rasuwar malamin ba wai asara ce ga iyalansa da almajiransa kawai ba, har ma ga ƙasa baki ɗaya.

“Sheikh Dahiru Bauchi malami ne, uba ne kuma murya ce ta daidaito da hikima. A matsayinsa na mai wa’azi kuma babban mai fassarar Alƙur’ani mai tsarki, ya kasance mai kira ga zaman lafiya da tsoron Allah. Rasuwarsa ta bar babban gibi,” in ji Shugaban Ƙasa.

Ya tuna da albarka da ya samu daga marigayin a lokacin shirye-shiryen zaɓen 2023.

Shugaban Ƙasa ya miƙa ta’aziyya ga almajiran malamin a faɗin Najeriya da wajen ƙasar, yana mai kira da su dawwamar da sunansa ta hanyar bin koyarwarsa ta zaman lafiya, tsoron Allah da kyautatawa ɗan adam.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Wata mata ta kashe ’yar shekara 7 a Ribas
  • Gwamnati Za Ta Biya Wasu Kudaden Ariyas Ga Masu Fensho Wannan Wata
  • Rasuwar Sheikh Dahiru Bauchi ta bar babban gibi a Najeriya – Tinubu
  • Rasha A Shirye Take Ta Taimaka Wa Najeriya A Fada Da Ta’addanci
  • NAJERIYA A YAU: Amafani Da Karfin Soji Ko Tattaunawa Ne Zai Kawo Matsalar Tsaro A Najeriya?
  • Tinubu ya aike wa Majalisar Dattawa sunayen jakadu
  • Tabarbarewar Tsaro na Barazana ga Siyasar Ƙasar Nan Gabanin Zaɓen 2027-Ado Doguwa
  • Matsalar Tsaro: Gwamnonin Arewa sun shirya taron gaggawa
  • China Ta Yi Tir Da Yadda Kasar Japan Ta Girke Makaamai Masu Linzami A Kusa Da Yankin Taiwan
  • NAJERIYA A YAU: Irin Radadin Da Masu Cutar Amosanin Jini Ke Fuskanta