HausaTv:
2025-08-15@17:45:42 GMT

Duniyarmu A Yau: Ranar 40 na Imam Hussain (a) Na Bana

Published: 15th, August 2025 GMT

Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na duniyarmu a uau shiri wanda yake kawo mako labarai masu muhimmanci a makon da ya gabata, wadanda suka shafi siyasa tattalin arziki zamantakrwa , tsaro da sauransu. Sannan mu yi masu Karin bayani daga karshe mu ji ra’ayin masana dangane da su da fatan masu saurarozasu kasance tare da mu a cikin shirimmu nay au.

////…Madallah, masu sauraro shirimmu nay au zai dubi “ranar 40 na Imam Hussain(a) wanda ya fado a ranakun Alhamis ko jumman da suka gabata, a nan Iran da kuma Iraki, kowa da yadda suke yi lissan watan Safar a wajensu. Ranar 40 na Imam Hussain (a) ita  ce ranar 20 ga watan Safar na ko wace shekara tun bayan shahadar Imam Husain (a) a ranar 10 ga watan Muharram shekara ta 61 bayan hijira. Wato daga 10 ga watan muhaharran na ko wace shekara zuwa 20 ga watan Safar na shekarar ne yace cika kwanaki 40 daga shahadarsa.

Shadar Imam h

Hussain (a) wanda hadisan manzon All…(S) da dama sun bayyana aukuwarsa da kuma abinda musulmi zasu yi idan haka ya auku. Muna da hadisai wadanda suka tabbatar da cewa manzon All..(s) ya yi kukan shahadar Hussain (a) a ranar da aka haifeshi, da aka tambayeshi sai yace al-ummata zasu kasheshi.

A waniahadisi dana Umma salamamatar manzon All..(s) tana cewa wata rana manzon All..yana kuka sai ta tambaye shiabinda ya sa yake kuka, sai yace yanzu din nan Jibrilu ya tashi daga waje ne ina wata da dana Hussai sai yace mani kanason ce ne, sai yace ina sonsa, sai yace masa amma al-ummanka zasu kashe a wani wurida aki kira karbala, sai ya mike ya debomani kasarya bani a hannu na, sai ya nuna mata kasar. Shi yasa yake kuka, sannan y ace mata ta ajiye wannan kasar a duk lokacinda ta ya zama jini to an kashe Husain.

A wani hadisin manzon All..(s) yana Magana kan hussain(a). ya sanshi bakin ciki saboda kasansa alamane na Imani, yana cewa:  Lalle, kissan Hussain yana da kuna a cikin zuciyar mumini, ba zai dushe ba har’abada.

A wani hadisin yana cewa: Hussain daga gareni yaki, ni kuma daga gareshi nake, All..ya so wanke yake son Hussaini, Hussain jika ne daga jikokin (annabawa).

Da kuma wasu hadisai da dama. Kafin haka yana daga cikin wadanda aka tsarkaka a aytar Tathir, yana daga cikin ayar Mubahala, yana daga cikin wadanda All..a cikin alkur’ani mai girma ya wajabta sonsu, kuma hakan shi ne, ladar annabcin manzon All..(s), yana daga cikin wadanda aka saukar da suratu Hal’ata a kansu.

Ayoyin alkur’ani da dama sun sauka suna yabonsu, wato iyalan gidan manzon All..(s). Rayuwar Imam Hussain da dukka Alhlu baitin manzon All…(s) yana da dangantaka da makoman Al-ummar manzon All..(s).      Kuma iyalan gidansa sun zama cikin jirrabawar da All…ya jarribi wannan al-ummar da su don ya ga abinda al-ummar zata ya sau.

Lalacewa al-ummar manzon All..(s) ya kai ga, bayan da aka kwace iko daga hannun wasiyyinsa na farko ko mahaifin sauran wasiyyan, al-umma ta kasa dawo mata da hakkinsa, har zuwa lokacinda, mutanen suka yi tawaye suka kashe khalifa na uku saboda zaluncin da danginsa sukewa al-ummar, sannan bayan sun kashe shi, sun tilasta masa ya zama shugabansu, yi ki amincewa, har sai ya ga cewa abinda bai karba ba to zai ga abinda yafi halin da ake ciki muni, sannan suka taimaka masa ya murkushe boren da aka yi masa na farko, amma bayan yakin siffin da Nehrawan, sun kasa taimaka masa, y agama da mu’awiya har sai da abubu suka fita hannu, bayan shahadarsa dans ana farko ya karbi jagoranci, amma suka ki taimaka masa, har aka tilasta masa yin sulhu da Mu’awiya dan Abusufyan.

A nan ne suka fara gane kurakuransu, amma lokaci ya kure, wasu sun dawo wajen imam Hassan kafi yayi shahada, sai suka ce masa mun yi kuskure da bamu taimaka maka ba. Sai yace ai kuma kunyi lattin. Shi ma ya yi shahada, a lokacinda al-amarin ya kai Imam Hussain(a), lalacewar ta kai ga abinda zai ya farkar da mutanen daga bacci mai zurfi da suka daga kare addinin All..ya bada jininsa, sai an kashe shi a daga kansa an kashi ana yawo da shi gari gari.

A ce wannan bakhawarije ne wan ya ki bai’a ga yazid, amma daga karshe su gano cewa ai jikan manzon All..(a) ne dan Fatimah dayar manzon All…wanda All..ya daukaka larabawa da shi, ya aiko da addinin karshe kuma yayi alkawalin wannan addinin sai ya mamaye duniya, kuma shi ne addinin gaskiya wanda All..ya yarda ya zama addini.

Shin wannan shi ne sakamakon da kuma ladar da zaku yiwa wannan annabin, ku yanka kansa kuna yawo da shi a cikin garuruwanku?.

Da wannan Imam Hussain (a) ya farkar da zukata wadanda basu mutuba, limamai da suka zo mayansa suka karfafa batun makokin Imam hussain da nufin jaddada makakin a cikin zukatan musulmi, mai yuwa wanda zai farka ya farka. Kuma a duk tsawon tarihin musulunci an samun masu farkawa saboda raya al-amarin Imam Hussain(a) raya tasuaa da Ashoora. Raya 40 na Imam Hussain.

A hidisi Imam Sadika(a) yana cewa :  Ku ziyarci junan ku, ku zauna ku tattauna dangane da Al-Amarimmi (wato shugabanci da jagoranci) ku raya al-amarimmu wao Ahlul baiti(a).

Imam Rida (a) yana cewa: Ya kai dan Shubaib, idan zaka yi kuka kayi kokan Hussain dan Aliyu dan Abitalib (a) Al-Hussain, lalle shi an yankashi kamar yadda ake yanka rago.

Don haka raya shahadar Imam Husain(a) ya hada da ranakun tasu’a da Ashoora da 40 da kuma ko yaushe a duk lokacinda suka aka sami danar yin haka. Dukkaninsu a kawai Hadisan manzon All..(a) da kuma lilamamai masu tsarki (a).

Sannan a duk tsawon tarihin musulunci azzaluman sarakunan sun yi iya yinsu yinsu, don hana Mabiya iyalan gidan manzon All..(a) raya wadannan kwanaki, ko kuma ziyartar kabarin Imam Hussain (a). wasu sun rusa hubbaren da akan kabarinsa, suka maida wurin gona, wasu sarakunan sun yanka kafa da hannayen duk wanda ya yi kokarin ziyarar kabarin Imam Hussain(a).

Amma duk kokarinsu ya tashi a banza, don ba wanda ya isa ya hana abinda All..ya kaddara sai ya faru.

Don haka raya wadannan ranakun sun bunkasa, sosai a wannan zamanin ha rya kaiga miliyoyin mutanene daga ciki da wajen Iraki suke ziyartar kabarin Imam Hussain (a).

Marigayi Imam Khomaini(q) wanda ya kafa JMI yana cewa: duk abinda muka samu daga Ashora ne, yana cewa duk rana ashoora ce kuma duk kasa karbala ce.

Don hala a wannan zamanin, musamman bayan nasarar da aka samu a JMI na kafa daula wacce take bin iyalan gidan manzon All..(a) a Iran, 40 na Imam Hussain (a) ya bunkasa, ya kuma fi daukar bangaren siyasa a kan sauran bangarorin kamar na samun kusanci ga All..T, saboda mafi yawan kasashen musulmi suna karkashin azzaluman sarakuna ko kuma karkashin iko kafirai. Wanda suke azbatar da su.

Don haka lamarin Imam Hussain (a) ya zama ramzi ne na samun yenci ya yakar azzalumai ko kafirai wadanda suke mamaye da kasashen musulmi da kuma

Al-amarin Imam Hussain(a) ya zama a wannan zamani lokaci ne na nuna karfin musulmi da hadin kansa, musamman tsakanin mabiya mazhabar Ahlulbaiti (a). Musamman kuma tsakanin Iran da Iraki, wadanda sune lasashen da shia suka fi rinjaye a duniya a cikinsu, hatta gwamnatocinsu ba na shia ne.

A Iran a shekara ta 1979 Imam Khomaini (a) daya daga cikin manya-manyan malaman shia a lokacin ya sami nasarar korar sarki sha daga kan kujerar sarautar kasar ya kuma kafa JMI wanda tsarin mukinsa da dukka al-amuransa suna tafiya karkashin tsarin mulki na mazhabar shia ne. da kuma Iraki inda mafi yawan mutanen kasar Shia ne kuma yana yana dauke da hubbarin limamai 6 daga cikin limamai masu tsarki daga iyalan gidan manzon All…(s). kuma birnin Najaf wanda na ne kabarin limamai na farko da cikin limaman, wato Aliyu dan Abitalib (a) yake.

Don haka iraki tana daga cikin cibiyoyin ilmi na mazhabar tun karni na 4 ko 5 hijiriyya tsakanin Najaf da Karbala. Sannan birnin Qom a kasar Iran na daga cikin cibiyoyin bada ilmi na mazhabar Iyalan gidan manzon All..(s) tun da danewa sannan hubbaren limami na 8 daga cikin liamaman masu tsarki yana birnin Mashhad a na arewa maso gabacin kasar.

Ganin yadda kasashen yamma suke adawa da samuwar JMI a Iran shekaru kimani 47 da suka gabata, ga kuma yadda cikinci ke yaduwa a duniya, kaashen yamma suna jin tsoro matuka kan cewa daga wadannan kasashen biyu, iran da iraki suna iya zaman masomin tawaye babban nan gaba ga turawan da kuma sauran kasashen musulmi a yankin da kuma sauran kasashen duniya.

Har’ila yau kasashen yamma suna jin tsoron daga cikin wadan nan kasashe biyu ko kuma daga Iran musulmi suna iya dogaro da ita su kauda HKI daga yankin wacce turawan ingila suka kafata bayan sun sami nasarar kada daular Uthmaniya ta musulmi shekaru 76 da suka gabata. Wanda kuma yake nuna raguwar karfin kafirai a kan musulmin yankin. Wanda daga karshe zai bude kofar fitar kasashen duniya da dama daga mulkin mallakar da suke masu tun daruruwan shekaru da suka gabata.

Daga nan muna iya cewa 40 na Imam Hussain (a) ya tashi daga al-amarin na addinin da kuma al-ada a cikin mabiya iyalan gidan manzon All..(s) ya zama wani al-amari wanda yake ingiza shia a ko ina suke a duniya su yi fada da zalunci. Su nuna jarunta wajen yakasar azzaluman sarakuna a cikin musulmi ko kuma sauran kafiran duniya.

Al-amarin Imam Hussain ya zama sunan da dukka azzalumai a ko ina suke a duniya, idan sun ji sunansa sai hantarsu ta kada.

Sannan daga karshe wannan halin zai ci gaba har zuwa lokacinda, kamar yadda musulmi gaba daya suka yi imanin cewa limami na 12 (a) zai zo ya ci duniyar da yaki ya kuma shimfida a dalci bayan cikarta da zalunci kamar yadda manzon All..(s) ya fada a cikin hadisai mustafida. Wato da yawa.

Share

0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Babban Sakataren Majalisar Kolin Tsaron Iran Ya Ce; Iran Zata Mayar Da Martani Mai Tsanani Kan Duk Wanda Ya Kai Mata Hari August 15, 2025 Kungiyar Kare Hakkin Bil’Adama Ta Human Rights Watch Ta Ce; Kai Hari Kan Gidan Yarin Evin Na Iran Laifin Yaki Ne August 15, 2025 Sojojin Mamayar Isra’ila Sun Kai Wani Mummunan Hari Kan Gaza Tare Da Rusa Gidajen Mutane A Khan Yunis August 15, 2025 Sojojin Mamayar Isra’ila Suna Ci Gaba Da Kashe Kansu Bayan Yakin Gaza August 15, 2025 Gwamnatin Mali Ta Bankado Wata Makarkashiyar Janyo Hargitsi A Kasar Tare Da Wargaza Shi August 15, 2025 Iran: Suna Bukatar Kawo Karshen Makaman Nukiliya Da Kuma Furuci Maras Daɗin Ji August 15, 2025 Kungiyar Ansarullahi Ta Kasar Yemen Ya Ce; Yahudawan Sahayoniyya Suna Yakar Al’ummar Falasdinu Duka Ne August 15, 2025 Kungiyoyin Kasa Da Kasa Sun Koka Kan Hana Shigar Da Kayayyakin Jin Kai Yankin Gaza August 15, 2025 Laifukan Cin Zarafi Musamman Kisha Kiyashi A Kasar Siyasa Ya Doshi Laifukan Yaki August 15, 2025 Kungiyar Ba Da Agaji Ta Sanar Da Yadda Cutar Kwalara Take Lashe Rayukan Mutane A Kasar Sudan August 15, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci About Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS News Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Explore Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS

উৎস: HausaTv

কীওয়ার্ড: iyalan gidan manzon All amarin Imam Hussain yana daga cikin daga karshe

এছাড়াও পড়ুন:

Kissoshin Rayuwa: Sirar Imam Hassan (a) 124

124-Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da haka barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na kissoshin rayuwa shiri wanda yake kawo maku kissoshin da suka zo cikin alkur’ani mai girma ko kuma cikin wasu littafan wadanda suka hada da littafin Dastane Rastan na Aya. Shahid Murtadha Muttahhari, ko kuma cikin littafin mathnawa na maulana Jalaluddeen Rumi ko kuma cikin wasu littafan da fatan masu sauraro zasu kasance tare da mu.

////… Madallah, masu sauraro idan kuna tare da mu a cikin shirimmu da ya gabata a kuma cikin sarir Imam Al-Hassan Almujtaba (a) diyar Fatima (s) kuma jikan manzon All..(s) na farko da muke kawo maku, idan kuna tare da mu a cikin shirimmu da ya gabata mun bayyana yadda.

Yadda aka yi karamin yakin Jamal, wanda ya faru bayan da Rundunar Aisha matar manzon All…(s) da talha da zubai suka kwace birnin Basra, suka saba alkawarin da suka kulla da gwamnan garin Uthman bin Hunaifa al-ansari. Suka kamashi suka azabtar da shi, harma suna son kashe, sai wata mataha ta roki Aisha ta barshi. Sai ta amince amma ta jefashi a gidan yari. Sannan ta kashe dukkan masu gadin baitul Mali sabran, basu da makami a hannunsu. Alokacin Hakim dan Jabala ya ji labarin haka, sai ya fito da mayaka kimani 300 wasu sunce 700 ya fada masu, mayakan aisha sun kashe su gaba daya.

Ance a lokacin yakin, wani daga cikin mayakan Aisha sun yanke kafar Hakim guda,sai ya kama mutumin ya kashe da kafarsa da ya yanke, sannan yaci gaba da yaki har sai da aka kada shi tare da wasu yanuwansa ukku. Duk sun yi shahada wajen kare amirul muminina Aliyu dan Abitalib (a).   Ana kiran wannan yakin Jamal Karami saboda Jamal babban shi ne yakar Amirumumina (a) ta yi daga baya. Sannan a madina kuma Imam Ali (a) yana shirin yakar muawiya dan Abisufyan, walin kufa wanda yayi tawaye, ya ce ba zai yi bai’a wa Imam Ali (a) sai ya kashe wadanda suka kashe Khalifa Uthman. A cikin wannan halin labari ya zo masa kan abinda Aisha da Talha da Zubair suka shirya.

Daga nan sai yaga cewa yakar Aisha da Talha da Zubair da farko yafi, saboda su suka fi hatsari a lokacin. Daga sai ya fita tare da wadanda suke tare da shi a Madina na manyan-manyan sahabban manzon All…(s). wasu laman tarihi sun bayyana cewa akwai akalla sahabban manzon All..(s) tare da Aliyu (a) wadanda suka kai 70. Wasunsu sun halarci sulhun Hudaibiyya. Sannan a lokacinda ya isa Rabza, sai yayi zango a can nay an kwanaki don ya kara da shi. Har’ila yau yana nan Rabzata ne labarin ya zo masa kan cewa Aisha da Talha da Zubair sun sun kwace barsara sun kuma fara yada fasadi a bayan kasa.

Don haka yayi sauran ya aiki mutane biyu zuwa Kufa kan suyi shirin fitowa don yakar masu tada fitina a Basra. Ya aiki Muhammadn Abubakar, da kuma Muhammad an Jaafar Attayyar .

Ance shi wanda aka fara sanyawa suna Muhammad bayan bayyanar musulunci kuma shi ne ya auri Ummu Kulthum diyar Fatimah (s) diyar manzon All..(s). Yayansa Abdullahi dan Jaafar ne ya auri Zainab (a) jarumar Karbala. Yana da dan uwa da ake kira Aun.

Ya rubuta wasika ya basum su kaiwa walin Kufa a lokacin Abu musa Alashari. Wasikar tana haka. [Ni na zabeku ne kan sauran birane, na kuma koma gareku ne saboda abinda ya faru, ku kasance masu taimakawa addinin All..masu kuma kai masa dauki, ku taimaka mana ku kuma yi yunkuri don taimakommu, Mu dai kyara muke so, don al-umma ta zama yanuwan juna duk wanda yake son wannan, ya kuma zabeshi, hakika ya so gaskiya, wanda kuma ya ki hakan ya ki gaskiya, ya yi watsi da ita.]

Da haka kuma yan aike guda biyu wato Muhammad dan Abubakar da kuma Muhammad dan Jaafaru. Sun kama hanya har suka isa Kufa, suka mikawa Abu Musa Al-shari wasika don karfafasu kan abinda ya zo da su na kirin mutane zuwa ya ki da Aisha da talha da zubair.

Amma sakon Imam (a) bai samu karbuwa daga wajen Abumusa ba, saboda ya bayyana halayen da ba’a saba saninsa da su ba. Ya hana mutane sauraron yan sakon Amirulmuminina Aliyu dan Abitalib (a). daga nan sai suka fara mu’amala da Abumusa Alashari da kaushi suna masa tsawo saboda ya yana mutane taimaka amirulmuminina (a) dan abitalib (a).

A lokacinda suka matsa masa, sai ya ce masu, ‘Wallahi, lalle bai’ar Uthman ta na kan wuyata, da kuma wuyar mutuminku, (ya na nufin Amirul muminina(a) idan har ya zama wajibi sai an yi yaki, to da farko sai an warware batun wadanda suka kashe Uthman).

Daga nan sai suka aikawa Imam Aliyu(a) dalla-dallan abinda ya faruwa a kufa da kuma mummunan matsayin da Abu Musa Al-Ashari ya dauka na yin masa tawaye. Da kuma hana mutane sauraron abinda suke fata.

Dagan a sai Imam (a) ya rubuta wata wasika ya bawa Hashim Al-Mirqal ya kaiwa Abumusa Al-Ashari, kuma ga binda ya zo cikin wasikar

{Lallai ni aiki Hashimu don ya kira mutane wadanda suke tare da kai su su shirya yaki su fito zuwa gareni, ka fadawa mutane, kuma lallai ne ban sanya gwamna ba sai don ka kasance cikin wadanda zasu taimaka mani a kan gaskiya.}. Sai Hashim ya kama hanya har ya isa Kufa, ya mikawa Abumusa Al-Ashari wasikar Imam (a). ya karantata amma kuma y adage a kan tawayensa, da kuma toshe hanya wa mutane su fahinci gaskiya.

A lokacinda suka matsa masa, sai Abu musa Al-ashari ya kira, Sa’ib dan Malikul As’ari(s) don ya bashi shawara kan al-amarinsa. Sai Malih al-ash’ari ya bashi shawara kan ya kasance tare da Imam (a) kada ya saba masa.

A lokacinda Hashim ya ga haka, sai ya aikawa Imam (a) wasika, inda ya bayyana masu ci gaba da nuna taurine kai da abu musa al-ashari yake yi. Don haka ya kasa shawo kansa.

A nan ne sai Imam (a) ya aiki dansa Imam Alhasan Al-mujtaba da kuma Ammar dan yasir da wasu. Ya aiki Imam Hassan (a) da wasika na tube Abumusa Al-ashari daga gwamnan Kufa, ya kuma maye gurbinsa da Qurdah dan Kaab ba-ansare.

Wannan shi ne Nissan takardan da Imam(a) ya rubuta (( Bayan haka, hakika ina ganin ka kaucewa wannan al-amarin, wanda nake ganin All.. bai sanya maka rabo a cikin sa ba, saboda ka ki aiwatar da umurnina. Hakika na aiki Hassan dan Aliyu da na, da Ammar dan Yasir su kira mutane su yi shirin yaki tare da ni. Kuma na aiki Qurdah dan Kaabu a matsayin sabon walin birnin Kufa, ka sauka daga aikimmu kana kaskantacce abin zargi, idan ka ki sauka na umurce shi ya tilasta maka yin hakan)).

Imam Hassan (a) ya Isa kufa mutanen kufa sun kewayeshi, suna girmamashi, da dama daga cikin musulmi a Kufa basu taba ganin Jikan manzon All..(s) ba, don haka sun fito don ganinsa da kuma girmama shi.

A dai-dai wannan lokacin ne sai Imam Hassan ya bayyana masu kan cewa an tube Abumusa Al-ashari wanda yake bayyana tawaye da rashin biyayya ga Amirul Muminina (a). da kuma gabatar da Qurdata a matsayinsa.

Sai dai duk da haka Abu musa ya ci gaba bayyana matsayinsa na rashin biyayya ga Amirulmuminin (a). da ya ji sanarwan Imam Hassan (a), na tube shi da kuma maye gurnsa da Qurdatah dan Kaabu. Amma Abu musa ya ci gaba da taurine kansa. Sai Imam Hassan (a) ya na masa maga da taushi, inda y ace masa: ya kai Abu Musa Wallah ba abinda muke bukata sai Alkhairi. Ba kuma kamar Amirulmuminina ne za’a ji tsoron wani abu daga wajensa ba : Sai Abu musa yace: Gaskiya ka fada, iyayena fansarka. Amma wanda ake neman shawararsa amintacce ne. sai Imam yace :ee.

Sai yace ya ji manzon All..(s) yana cewa: Lalle akwai fitina kasance, wanda ya zauna yafi wanda ya tashi, wanda yake zaune yafi wanda yake tafiya, wanda kuma yake tafiya ya fi mahayi. …..

Sai Ammar dan Yasir ya ce masa. Ka ji wannan daga manzon All..(s). Ya ce: ee, sai Ammar ya juya ta mutane yace masu, lalle manzon All..(s) yana nufin Amu musa ne, ya na zaune ya fi masa da ya tsaya.

Sai duk wannan bai hana Abu Musa gano abinda yakamata ya yi ba. Sai Imam Hassan (a) ya fuskanci mutane yana masu magana kan nsu shirya fita yaki. Yana cewa

 [Ya  ku mutane! Lalle Amirulmuminina yana da abinda ya isheku kome, Mun zo wajenku ne don kiraku zuwa yaki, don ku ne na gaba-gaba a yaki a cikin birane,kuma kune shugabannin larabawa. Kuma kunji yadda Talha da Zubair yadda suka kwace bai’arsu da kuma yadda suka fido da Aisha. Kamar kuka ji. Kun san raunin mata, da kuma yadda ra’ayinsu yake kaiwa da asara. Don haka ne All..ya sanyan mata masu kula da mata.

Na rantse da All..idan ba wanda ya taimaka masa, banda wadanda suke tare da shin a Muhajiruna da Ansar da sun wadatar da shi. Da wadanda All…ya aiko masa na daga cikin zababbu ya wadatar da shi, don haka ku taimakawa All..ya taimaka maku. ]. 

Sai ammar dan yasir ya tashi ya yi wa mutane jawabi dangane da yaki da kuma dangane da Uthman yace: Ya ku mutanen Kufa: duk da cewa labarimmu ya boye daga gareku amma al-amarinku ya riskeku. …

Zamu karasa wannan maganar a shirimmu nan gaba.

A nan kuma zamu dasa aya a cikin shirimmu nay au sai kuma wata fitowa idan All,,, ya kaimu, wassalamu alaikum wa rahamatullahi wa barkatuhu.

Share

0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Kissoshin Rayuwa: Sirar Imam Hassan (a) 125 August 13, 2025 Iran: Babu Mika Kai Ga Takurawar kasashen Yamma har sai An Kawo Karshen Barazana August 13, 2025 Hukuma Mai Kula Da Sauka Da Tashin Jiragen Sama A Paris Ya Dakatar Da Wani Ma’aikacinta August 13, 2025 Iraki Tace: Ita Yentacciyar Kasashe Ce Bayan da Amurka Ta Yi Korafi Kan Yarjeniyar tsaro da Iran August 13, 2025 Ministan Harkokin Wajen Masar Ya sake Ganawa da Aragchi Da Kuma Gorossy August 13, 2025 Shugaban Kasar Iran Ya Jaddada Alhininsa Kan Kashen Masanan Kasar Iran Da ‘Yan Sahayoniyya Suka Yi August 13, 2025 Ministan Harkokin Wajen Iran Ya Jaddada Cewa: Lokaci Ya Yi Da Za A Daina Kakaka Takunkumi Da Ba Dace Ba Kan Kasashe August 13, 2025 Sakataren Majalisar Kolin Tsaron Kasar Iran Ya Jaddada Kasancewar Iran Tare Da Kasar Lebanon Koda Yaushe August 13, 2025 Kasar Iraki Ta Ce: Yarjejeniyar Da Ta Kulla Da Iran Zai Amfani Dukkan Kasashen Yankin August 13, 2025 Sojojin Yemen Sun Kai Hare-Hare Kan Haramtacciyar Kasar Isra’Ila Har Sau Shida  August 13, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci About Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS News Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Explore Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Duniyarmu A Yau: Ranar 40 Ta Imam Hussain (a) A Bana
  • Miliyoyin Mutane Sun Taru A Karbala Don Juyayin 40 Na Shahadarsa Imam Hussain(a)
  • Kissoshin Rayuwa: Sirar Imam Hassan (a) 130
  • Kissoshin Rayuwa: Sirar Imam Hassan (a) 129
  • Kissoshin Rayuwa: Sirar Imam Hassan (a) 128
  • Kissoshin Rayuwa: Imam Hassan (a) 127
  • Kissoshin Rayuwa: Sirar Imam Hassan (a) 126
  • Kissoshin Rayuwa: Sirar Imam Hassan (a) 125
  • Kissoshin Rayuwa: Sirar Imam Hassan (a) 124