Sojoji Sun Ceto Shugaban Fulani, Mutane 5 Daga Hannun Ƴan Bindiga A Kogi
Published: 15th, August 2025 GMT
Sojojin Nijeriya a Lokoja, tare da haɗin gwuiwar sauran hukumomin tsaro, sun kuɓutar da mutane shida da aka yi garkuwa da su a yankin Obajana na Jihar Kogi. Cikin waɗanda aka ceto akwai Sarkin Fulani na Asinwe a ƙaramar hukumar Okehi, wanda aka sace a gidansa, tare da wasu mutum huɗu da aka sace a ranar 12 ga Agusta, da kuma mutum biyu da aka sace a ranar 28 ga Yuli a Apata, Lokoja.
Kwamandan bataliya ta 12, kuma Kwamandan Operation Accord III, Birgediya Janar Kasim Sidi, wanda Commanding Officer na bataliya ta 126, Laftanar Kanal Francis Nwoffiah ya wakilta, ya ce an samu nasarar kuɓutar da fursunonin ne bayan samun sahihan bayanan leƙen asiri, inda dakarun suka bi sawun ƴan bindigar har cikin daji. Ya ce ƴan bindigar sun tsere da raunuka bayan fuskantar ƙarin ƙarfin Soji, suka bar waɗanda suka sace da kuma kayan su, ciki har da alburusai.
Jihar Kogi Ta Kafa Kotuna 9 Don Hukunta Masu Cin Zarafin Mata ’Yansanda Sun Gano Gawar Ɗan Jaridar Da Aka Kashe A Jihar KogiYa ƙara da cewa, an kuɓutar da dukkan waɗanda aka sace ba tare da wani rauni ba, kuma za a haɗa su da iyalansu bayan sun sami kulawar likita. Janar Sidi ya gargaɗi ƴan ta’adda da masu garkuwa da mutane a Kogi da jihohin makwabta su tuba, in ba haka ba za su fuskanci mummunar sakamako.
Wani daga cikin waɗanda aka ceto, Sarkin Fulani na Asinwe, Malam Adamu Zage, ya gode wa Sojojin da sauran jami’an tsaro bisa jarumtar da suka nuna. Gwamnan jihar, Ahmed Usman Ododo, ya ce gwamnati ba za ta lamunci aikata laifuka a Kogi ba, tare da bayyana cewa ana ci gaba da kai farmaki kan masu aikata miyagun laifuka a jihar da kewaye.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppকীওয়ার্ড: Garkuwa Sojojin Nijeriya
এছাড়াও পড়ুন:
Sojoji Sun Kashe Kwamandan IPOB ‘Alhaji’, Da Wasu 26, Sun Kama 22
Sojojin Nijeriya sun kashe wani kwamandan ƙungiyar ƴan ta’adda IPOB/ESN da ake nema ruwa a jallo, mai suna ‘Alhaji’, tare da wasu mutane 26 a jerin hare-haren da suka kai a sassan ƙasar tsakanin 8 zuwa 11 ga Oktoba, 2025. Rundunar Sojin ta ce an kuma ceto mutane biyar da aka yi garkuwa da su, tare da kwace makamai, da harsasai, da kuɗaɗe.
A kudu maso gabas, Sojojin Operation UDO KA sun kai farmaki a Izzi, jihar Ebonyi, inda suka kashe ‘Alhaji’ bayan ya yi yunƙurin kwace bindiga daga hannun wani Soja lokacin kama shi. Haka kuma, a jihar Imo, an rusa wata maboyar IPOB/ESN da ake amfani da shi wajen horar da mambobi.
Sojoji Sun Cafke Babban Kwamandan IPOB Sojoji Sun Kama Ƙasurgumin Ɗan Bindiga, Sun Kashe Shugaban IPOBA Arewa maso gabas, Sojojin Operation Haɗin Kai sun kashe ‘yan ta’adda tara a Magumeri da Gajiram a jihar Borno, inda suka ceto fararen hula biyu tare da ƙwato fiye da Naira ₦4.3 miliyan. A wasu hare-haren sama a jihar Sokoto, an hallaka shugabannin ‘yan ta’adda da dama, yayin da aka kama masu safarar miyagun ƙwayoyi daga Legas zuwa Zamfara.
A Arewa ta Tsakiya da Kudu maso Kudu, Sojojin Operation Whirl Stroke da Operation DELTA SAFE sun kama masu garkuwa da mutane, sun kashe ‘yan ƙungiyar asiri biyu, kuma sun ƙwato makamai da babura. Rundunar Sojin ta ce gaba ɗaya an kashe ‘yan ta’adda 26, an kama mutum 22, kuma an ceto mutane biyar da aka yi garkuwa da su.
ShareTweetSendShare MASU ALAKA