Jama’a ba sa yaba wa kokarinmu na hana aikata laifi – Babban Sufeton ’Yan Sanda
Published: 15th, August 2025 GMT
Babban Sufeton ’Yan Sanda na Najeriya, Kayode Egbetokun, ya ce galibin jama’a ba sa yaba wa kokarin jami’ansu na hana aikata laifi a cikin al’umma, duk da yana daya daga cikin manyan ayyukansu.
Kayode, wanda Mataimakin Babban Sufeto mai kula da sashen sayo kayayyaki na rundunar, A.A. Hamza ya wakilta, ya fadi hakan ne a Abuja ranar Alhamis, yayin taron kaddamar da wani littafi mai suna “Fraud unmasked”, wanda Dr Preal Ogbulu ya wallafa.
A cewarsa, “Duk laifin da aka dakile aikatawa, dole akwai namijin kokarin da aka yi a kan hakan. Kundin tsarin mulki da kuma dokokin’yan sanda ya ba rundunarmu aikin ganowa da kuma hana aikata laifi. Abu mafi muhimmanci ma shi ne hana aikata laifin tun kafin a yi shi, saboda ya fi sauki, ya fi sauri sannan yana rage cutar da mara karfi,”
Ya kuma lura cewa galibi jama’a kan auna nasarorin ayyukan ’yan sanda ne a kan laifukan da suka faru, ba tare da kallon wadanda suka dakile faruwarsu ba.
Babban Sufeton ya ce, “Duk lokacin da muka hana aikata wani laifi, ba a ganin mun yi kokari. Lokacin da kawai ake ganin kokarinmu shi ne bayan aikata laifi, kodayake aikinmu ya wuce iya nan”.
Daga nan sai Kayode ya yaba wa mawallafin littafin kan yadda ya tabo batutuwan binciken kwakwaf da ya ce yana da matukar muhimmanci wajen hana aikata laifi da kuma hukunta masu aikata shi.
Babban Sufeton ya kuma ce littafin ya yi daidai da kudurorin rundunarsu sannan ya fito da muhimmancin hadin gwiwa wajen dakile aikata laifuka.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Yan Sanda Kayode Egbetokun
এছাড়াও পড়ুন:
Dan Majalisar Tarayyar Kaduna ya bar Jam’iyyar PDP
Ɗan Majalisar Tarayya mai Wakiltar Sabon Gari Daga Jihar Kaduna, Sadiq Ango Abdullahi, ya fice daga Jam’iyyarsa ta PDP.
Honorabul Abdullahi wanda shi ne Mataimakin Shugaban Kwamishinan Hukumar Kula da Hanyoyi (FERMA) ya alaƙanta ficewarsa da rikicin cikin gida da rabuwar kai da ya ki ci ya ƙi cinyewa a jam’iyyar.
A ranar Litinin ya aike da wasikar ta ficewa ga Shugaban PDP na Mazabar Hanwa da ke Ƙaramar Hukumar Sabon Gari, yana mai cewa rikicin ya hana shi taɓukawa matsayin zaɓaɓɓen ɗan Majalisar Tarayya.
Ya cewa saboda haka yana dacewar ficewarsa daga jam’iyyar ba tare da la’akari da siyasa ba, domin amfanin ɗauƙacin al’ummar mazabar.
Majalisar Shura ta fara ganawar sirri da Malam Triumph Zaben Kamaru: Issa Tchiroma Bakary ya lashe yankunan da Biya ke da rinjayeYa yaba wa jam’iyyar bisa damar da kuma gudummawar da ta ba shi domin hidimta wa al’umma.