Aminiya:
2025-08-14@13:51:08 GMT

Rashin Lantarki: Babu wanda za mu zaɓa a 2027 — Jama’ar Talasse

Published: 14th, August 2025 GMT

Al’ummar garin Talasse da ke Ƙaramar Hukumar Balanga a Jihar Gombe, sun ce sun gaji da rayuwa cikin duhu har na tsawon shekaru 19.

Sun kuma bayyana takaicinsu bayan tsayawar aikin wutar lantarki da ya tsaya.

Ba a ba mu dala 100,000 da gwamnati ta mana alƙawari ba — Super Falcons NDLEA ta lalata gonar tabar wiwi a Gombe

Aikin, wanda ɗan majalisar wakilai mai wakiltar Billiri da Balanga, Ali Isa JC, ya fara tun farkon wannan shekara, ya sanya al’ummar yankin farin ciki bayan an kafa turakun wuta da na’urorin taransifoma.

Sai dai cikin watanni biyu da suka gabata, aikin ya tsaya ba tare da wani bayani ba.

“Yan siyasa su kan zo da alƙawura a lokacin zaɓe, sannan su ɓace bayan sun yi nasara,” in ji Yakubu Ayuba, mazaunin Talasse.

Ya ce rashin wuta ya jawo durƙushewar kasuwanci da tattalin arziƙi a yankin, kuma hakan zai yi tasiri a zaɓen 2027.

Wani mai sana’ar ɗinki, Musa Adamu Galadima, ya ce: “Janerata ya fi ƙarfinmu. Na kori yaran da ke koyon sana’a saboda ba zan iya ɗaukar nauyinsu ba.”

Shi ma Sulaiman Idris, mai sayar da lemun kwalba, ya ce yana kashe kusan Naira 10,000 a rana wajen siyan ƙanƙara.

“Lokacin da aka kawo kayan aiki mun yi farin ciki, amma yanzu komai ya tsaya,” in ji shi.

Da aka tuntuɓi ɗan majalisar don jin ta bakinsa, Ali Isa JC, ya ce matsalar ta samo asali ne daga jinkirin sakin kuɗaɗen aikin daga Gwamnatin Tarayya, amma suna ƙoƙarin ganin aikin ya ci gaba.

A halin yanzu, gwamnatin Jihar Gombe ta fara aikin samar da wuta ta hanyar samar da ƙaramar madatsar ruwa da hasken rana a Dam ɗin Balanga, wanda zai iya samar da 620KW.

Duk da haka, jama’ar Talasse sun ce rashin wutar zai sa su ƙauracewa kaɗa ƙuri’a a zaɓen 2027.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Ɗan Majalisa Rashin Wuta Wutar Lantarki

এছাড়াও পড়ুন:

Hukumar Alhazai ta Jihar Kaduna Ta Bukaci Maniyyatan Aikin Hajjin 2026 Su Fara Biyan Kudaden Ajiya

Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Kaduna ta shawarci maniyyata aikin Hajjin shekarar 2026 da su fara shirin biyan kudaden ajiya.

Kiran ya biyo bayan taron da Hukumar Kula da Aikin Hajji ta Kasa (NAHCON) ta gudanar tare da hukumomin Alhazai na jihohi, inda aka bayar da shawarar ajiyar naira miliyan 8 da rabi ga masu niyyar zuwa aikin Hajji, kafin a sanar da hakikanin kudin aikin Hajjin shekarar 2026.

A cikin wata sanarwa, mai magana da yawun hukumar, Yunusa Mohammed Abdullahi, ya shawarci wadanda ba su da fasfo da su gaggauta zuwa Hukumar Shige da Fice ta Kasa domin yin nasu, yana mai cewa shi ne ake amfani da shi wajen hada takardun tafiya.

Najeriya ta sake samun kujeru 95,000 daga Masarautar Saudiyya domin aikin Hajjin 2026, ana kuma sa ran  jihar Kaduna za ta sake samun yawan kujerun da aka saba bata.

Yunusa Mohammed ya kuma bayyana cewa hukumar za ta sanar da maniyyata lokacin da za a fara yin rajista a Jihar Kaduna.

 

Safiyah Abdulkadir 

 

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Kuri’ar Jin Ra’ayin Jama’a Na CGTN Ta Bayyana Rashin Gamsuwa Da Manufar Shugaba Trump Ta Korar Marasa Galihu
  • Allah zai kunyata masu ɗaukar nauyin ta’addanci a Zamfara — Gwamna Dauda
  • Rashin aiwatar da doka na bai wa masu laifi ƙwarin guiwa — Ɗan majalisar Gombe
  • Ranar Matasa: Ciyaman ya jinjina wa gwamnatin Gombe kan ɗaukar matasa aiki
  • Jama’a sun koka kan rashin kammala aikin titi a Kafanchan
  • Gwamna Namadi Ya Yaba Wa Kungiyar NBA Bisa Inganta Manufofi Da Ka’idojin Aikin Lauya
  • Babu Neman Afuwa Kan Nuna Goyan Bayan Tinubu Da Na Yi – Soludo
  • Hukumar Alhazai ta Jihar Kaduna Ta Bukaci Maniyyatan Aikin Hajjin 2026 Su Fara Biyan Kudaden Ajiya
  • UNICEF Da Gavi Sun Bada Na’urorin Samar Da Wutar Lantarki Ta Hasken Rana Ga Jihar Kano