Gwamnati ta amince a kafa sabbin jami’o’i masu zaman kansu guda 9
Published: 14th, August 2025 GMT
Gwamnatin Tarayya ta amince a kafa karin sababbin jami’o’i masu zaman kansu guda guda tara a fadin Najeriya.
Ministan Ilimi, Dr Tunji Alausa ne ya sanar da hakan ranar Laraba lokacin da yake jawabi ga ’yan jaridar Fadar Shugaban Kasa jim kadan da kammala taron Majalisar Zartarwa ta Kasa.
Bello Turji bai miƙa wuya ba har yanzu — DHQ Amurka za ta sayar wa Najeriya makaman N530bn don yaƙi da ta’addanciShugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu ne ya jagoranci taron wanda aka gudanar a Abuja.
A cewar ministan, sababbin jami’o’in da aka ba lasisin sun hada da Jami’ar Tazkiyah da ke Kaduna, Jami’ar Leadership da ke Abuja, Jami’ar Jimoh Babalola da ke Kwara da Jami’ar Bridget da ke Mbaise a jihar Imo.
Sauran jami’o’in sun hada da jami’ar Greenland da ke Jigawa da jami’ar JEFAP da ke Neja da jami’ar Azione Verde da ke Imo, sai jami’ar karatu daga gida ta Unique da ke jihar Legas da kuma takwararta mai suna American Open University da ke jihar Ogun.
Alausa ya kuma ce Tinubu ya gaji bukatu guda 551 na kafa makarantun gaba da sakandire masu zaman kansu, wadanda ya ce dole sai an cika tsauraran sharuda kafin a ba su lasisin.
Sai dai ya ce rashin cika wadannan sharuda ne ya rage adadin zuwa guda 79 kacal, inda daga ciki aka amince da guda tara a ranar ta Laraba.
Ya ce da yawa daga cikin jami’o’in da aka ba lasisin sun dade suna jira, wasu ma sun shafe sama da shekaru shida suna kan layi.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Gwamnatin tarayya
এছাড়াও পড়ুন:
Ƴan Bindiga Sun Amince Da Dakatar Da Hare-Hare A Ƙananan Hukumomi 5 A Katsina
ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin Kasar Sin Ta Kare Matakinta Na Takaita Fitar Da Ma’adanan Farin Karfe Na Rare Earth October 12, 2025
Daga Birnin Sin An Wallafa Ra’ayoyin Shugaba Xi Kan Batutuwan Da Suka Shafi Mata Da Yara Cikin Karin Harsunan Waje October 12, 2025
Daga Birnin Sin Jami’ar MDD: Taron Kolin Matan Duniya Ya Zo Daidai Lokacin Da Ya Dace October 12, 2025