HausaTv:
2025-11-27@21:55:06 GMT

Kissoshin Rayuwa: Imam Hassan (a) 127

Published: 13th, August 2025 GMT

127-Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka  barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na kissoshin rayuwa shirin wanda yake kawo maku kissoshi wadanda suka zo cikin alkur’ani mai girma ko cikin wasu littafai wadanda suka hada sa littafin Dastane Rastantan ko kuma cikin littafin mathnawi na maulana jalaluddeen Rumi ko kuma cikin wasu littafan da fatan masu sauraro zasu kasashence tare da mu a cikin shirimmu na yau.

///… Madallah, masu sauraro idan kuna tare da mu a cikin shirimmu da ya gabata a kuma cikin sirar Imam Al-Hassan Al-Mutaba, (a) dan Fatima (s) diyar manzon All..(s) da muke kawo maku, a cikin shirin munyi maganar yadda Imam Ali (a) da dansa Imam Al-Hassan(a) tare da rundunarsu suka iso birnin Basra na kasar Iraki, inda suka yi sansani a wani wuri wanda ake kira zawiyya sannan Imam yayi sallar nafiya raka’oi biyu biyu sannan yayi addu’o’ii . ya kammala sai ya aikawa Aisha yan sako guda biyu su fada mata sakonsa gareta. Sakon kuma tunatar da ita kan cewa manzon All..(s) ya  umurceta ta zauna a gidanta amma sai ta fito, sannan tare da nuna mata hatsarin abinda ta sa kanta ya shiga cikin al-amuran shugabancin al-ummar musulmi, da kuma nasihar ta koma gida, tun al-amarin ya kara lalacewa, sannan daga karshe ta tuba daga laifukan da ta aikata.  Yan sako sun isar da sakon amma taki ta fadi kome, sannan taki ta koma gida. Munji yadda dan renonta Abdullahi don zubair yayi magana mara dani, kan Amirul muminina (a) inda a cikin maganar ya nuna cewa wai Imam Ali(a) ne kashe Khalifa Uthman…da dai wasu karyayyaki da ya yi magana.

Sannnan a lokacinda ya  labara ya riskeshi sai ya umurci dansa Imam Al-Hassan ya mayar masa da martayi. Sai Imam Hassan (a) ya hau mimbari ya mayar masa ta martani, inda a ciki ya kafa shaida da mutanen Madina muharun da Ankasar kan karyar abinda ya fada na cewa mahaifinsa ne ya kashe Uthman sanan ya tabbatar masa babansa Zubair dan Awwam shi yana daga cikin wadanda suka ingiza mutane su kashe Uthman, tun ya kai gay a kafa tutansa a kan baitl malin Uthman tun yana da rai, yana jiran a kashe shi ya zama tasa.

Sannan yace, masu su yakinsu da Aisha ce mai rakumi, wacce banu umayya suka zagayata wai suna son daukar fansar jinin mutuminsa daga Imam Ali(a). Ba don ita ba da ba’a yi yakin Jamal karama da kuma babban ba.

Bayanda Imam Ali (a) yayi duk abinda zai yi, na hada yaki, sun lalatasu, sai ya fito da mushafi alkur’ani mai girma ya rike shi da hannunsa na dama sai ya fara zagayawa cikin sahon sojojinsa, yana cewa : waye daga cikinku zai bijiromasu wannan mushafin da abinda yake cikin? Idan an yanke hannunsa guda ya rike shi da dayan hannun, idan an yanketa ya rike da hakoransa, kuma za’a kashe shi?

Wani matashi daga cikin matasan kufa ya fito ya ce, nine ya Amiral Muminin! Sai Imam (a) ya dube shi, sai ya juya fuskansa ya ci gaba da cewa wa zai bijiro masau da wannan mushafi… har zuwa karshen maganarsa, ba wanda ya amsa masa sai wannan matashin .

Daga nan sai ya mika masa mushafin ya ce masa: Ka bijiro masa wannan! Shi ne zai shiga tsakanimmu da ku, ina ahadku da All..dangane da zubar da jinku da jinimmu.

Sai matashin nan ya riko shi, ba tare da wani tsoro ba, ya bijoro musu da Al-kur’ani yana cewa , wannan al-kur’ani tsakanimm, ina hanaku da All, a cikin zubar da jininku, sai suka yi kamar da su yake magana ba. Daga karshe sai wani daga cikinsu ya yanke hannunsa , guda sai ya rike shi da hannun hagu, sai suka katse hannun sai ya rike da hakuransa jininsa na zuba, yana kiransu ga aiki da littafin All.. sai suka yi masa ruwan kibaw sai ya fadi gawa  shahidi. Sai mahaifiyarsa ta tashi tana juyayin shahadarsa.

Don haka daga nan ya sauke dukkan uzurin da zai basu, ba kuma abinda ya rage sai yaki.

Bayan haka sai ya fadawa sahabbansa, A yanzu ne ya halatta ku yakesu, dukansu ya halatta. Sai Imam ya kira kwamandojinsa shugabannin sojojinsa ya tsaida su a wurarensu bayan an kashe jakadansa na karshe a garesu suka kashe shi. Sannan yace masu Ayyuhan Nasu, ! Idan kun sami nasara a kansu kada ku karasa wanda kuka ji masa rauni! Kada ku kashe wanda kuka kama, kada ku bi wanda ya jiya yana gudu daga gareku, wanda ya jiya bayansa kada ku bi shi, kada ku yaye al-auransu. Kada ku yayyanka jikin wadanda  kuka kashe. Kada ku yaye labule, sannan kada ku kusanci dukiyoyinsu, sai abinda kuka gani a sansaninsu na daga makami.ko abin hawa, ko bawa, ko kuyanga, banda wadannan duk abinda suka bari abin gadone ga masu gadansu kamar yadda yazo cikin littafin All…

Daga nan Aisha ta hau rakuminta, wecc ta sukan sanya mata rigar fatan dabbobi, da kuma fatar shanu, da wasu fatun dabbobi.

Itsa ce da shugabancin rundunonin gaba daya. Ita ce take tsara mayaka, ta kuma bada umurni. Ta tura sojojinta masu kibiyoyo kan sojojin Imam suka kashe wasu sahabbansa. Don haka dai ya zama dole a yayi yaki.

Sai Imam ya saba takobinsa, ya bawa dansa Muammad dan Hanafiyya tutansa sai ya fadawa  Al-Hassan da Al-Hussain (a) kan cewa na bawa dan’uwanku tuta ne don matsayinku a wajen manzon All..(s).

Sai Muhammad bin Hanafiyya ya nausa da tutarsa zuwa tsakiyar yaki, amma sai suka yi masa ruwan kibau, sai ya rage saurinsa, sai kawai ya ji hannun babansa ya taba shi yana cewa, wata jijiya daga mahaifiyarsa ta same ka. Sannan ya kwace tutar ya girgizata ya nosa gaba.

Ya riketa da hanun hagu sannan takobin zulfikar kuma daga hannun damarsa, da shi ne ya yaki kafirai a yake-yaken Badar da Uhud a zamanin manzon All..(a) sai ga shi a yau yana yakar wadanda suka karya alkawari da ita ya na dukansu dama da hago, a cikin dan karamin lokacin ya maida mutane Basra kamar fari suka watsewa, sai ga tutocin muhajirun da Ansar kuma sun suna sama suka ta yakan wadanda suka karya al-kawari.

Ana cikin wannan halin wanda makiya suke kewaye da Imam (a) sai ya tuna da Zubai, sai ya kira babban murya, ina Zubair!, sai zubair yace, ganinan, sai ya ce: Ya baban Abdullahi me ya kawoka nan, sai yace:  neman jinin Uthmanu, sai  Imam ya dube shi da idon shakka, sai yace: Kana neman Jinan Uthmanu? Sai yace Eee, sai Imam yace: All.. ya tsinewa wanda ya kashe Uthman.

Sai Imam(a) ya zo kusa da shi ya fara masa magana, yana cewa : Ina hadaka da All..Ya Zubair, zaka tuna wata rana ka wuce ni, kana tare da manzon All..(a) yana dogaro da hannunka, sai manzon All..(s) yayi mani sallama sannan ya yi mani dariya, sai ya juya wajenka, sai yace maka, ya Zubair , zaka yaki Aliyu kana mai zaluntarsa.

Sai Zubai ya sunkuya kansa, ya nuna damuwa, sai ya cewa Ali(a): ee na tuna. Sai Imam yace to me yasa kake yaka ta, Sau yace na manta da shi, da na tuna, da ban yakeka ba. Sai Imam yace masa: Koma ka daina yakata. Sai yace ta yaya hakan zai yu, bayan rundunoni sun rika sun gamu, wallahi wannan kunya ne wanda ba zai wanku ba har abada.

Sai Imam yace masa: Ka koma kafin kunya da wuta su hadammaka. Sai Zubar ya jiyu ya na karanta wasu baitoci ya na yabon Imam Ali (a). Yana son ya bar wannan fitinar,

Sannan ya kai kansa gaban babban kwamandan sojojinsu Aisha matar manzon All..(s). yana fada mata: Ya ummul Muminina, lallai ne ban taba shiga wani hali ba a rayuwata, sai na san in azan sanya kafata ba, sai wannan halin da na shiga. Bann sani ba, shin zan ci gaba ne ko zan koma baya.

Aisha ta fahinci abinda yake boye a cikin zuciyarsa da wadannan maganganun da yayi, sai  tace: Kai bari Ya baban Abdullahi, ka dai ji tsoron takubban yayan Abdulmuttalib.

Ana cikin wannan halin sai dansa Abdullahi ya zo yana cewa: Ka fita a cikin basira da yakinin cewa kana kan gaskiya, amma a lokacinda kaga tutucin dan Abitalib ka fahinci cewa mutuwa ce a fili sai kaji tsoro, Zubai ya zauna yana tunani ga dansa ya zo yana tuhumarsa da tsoro da ragonci, sai ya ce masa: kaiton ka, Ai ni na yi  masa wato (Aliyu) al-kawalin ba zan sake yakarsa ba”. sai Abdullahi ya ce masa: in don wannan ne: Ka yi kaffarar rantsuwarka da yentar da bawanka Sirjas?

Wasu malamai sun bayyana cewa a lokacinda dansa ya tuhumeshi da tsoro da razana, sai ya sake shiga cikin masu yaki ya kutsa ta dama ya sake kutsawa da hagu sannan ya fita ya zo wajen dansa All..ya ce masa mai tsoro zai yi abinda nayi yanzu nan? .

Bayan haka sai Zubair ya kama hanya ya bar wajen yakin ya hau dokinsa ya tafi har ya kai wani wuri da ake kira wadi –Sabaa, ya sami Al-Ahnaf dan kais tare da mutanensa suna zaune a wurin sai suka ce masa, Ga Zubair nan Ya tsallaka.

Sai yace masu: Me zan yi da zubair? Ya hada kan bangarori manya-manya biyu suna kashe junansu. Sai mutane daga cikin sojojin Aisha daga kabilar Banu Taim suka bishi, amma Amru dan Jamus ya rikasu isa wajen Zubair, a lokacin ya sauka don yayi sallah, sai yace masu zaku bada sallah ko in bada sallar jam’i. sai suka ce ya bada sallah. Zubai ya fara sallah sai suka kashe shi.

Karshen rayuwar Zubai Kenan, wanda ya kyautata farkon sa, tare da khilful Fudul, wacce take maganar tallafawa wanda aka zalunta tun kafin bayyanar musulunci. Sannan ya yi yakin Badar da uhud ya yayewa manzon All..(s) bakin ciki da dama a lokacin da sahabban suka gudu suka barshi. Bayan wafatin manzon All..(s), a lokacin Banu taim suka kwacewa Amirul muminina (a) hankkinsa ya kasance tare da shi, yana ganin hakkinsa ne shi kadai, ya cancanci Khalifancin manzon All..bayan wafatinsa. Amma lokacin ya sauya shima ya sauya, har ya kaiga shi ne yake son kwace khalifanci daga Amirul muminina (a). ina lillah wa inna ilaihi Raji’un.

Masu sauraro a nan zamu dasa aya a cikin shirimmu na yau sai kuma wata fitowa idan All..ya kaimu. Wassalamu alaikum wa rahamatullahi wa barakatuhu.

Share

0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Kissoshin Rayuwa: Sirar Imam Hassan (a) 128 August 13, 2025 Kissoshin Rayuwa: Sirar Imam Hassan (a) 126 August 13, 2025 Kissoshin Rayuwa: Sirar Imam Hassan (a) 125 August 13, 2025 Kissoshin Rayuwa: Sirar Imam Hassan (a) 124 August 13, 2025 Iran: Babu Mika Kai Ga Takurawar kasashen Yamma har sai An Kawo Karshen Barazana August 13, 2025 Hukuma Mai Kula Da Sauka Da Tashin Jiragen Sama A Paris Ya Dakatar Da Wani Ma’aikacinta August 13, 2025 Iraki Tace: Ita Yentacciyar Kasashe Ce Bayan da Amurka Ta Yi Korafi Kan Yarjeniyar tsaro da Iran August 13, 2025 Ministan Harkokin Wajen Masar Ya sake Ganawa da Aragchi Da Kuma Gorossy August 13, 2025 Shugaban Kasar Iran Ya Jaddada Alhininsa Kan Kashen Masanan Kasar Iran Da ‘Yan Sahayoniyya Suka Yi August 13, 2025 Ministan Harkokin Wajen Iran Ya Jaddada Cewa: Lokaci Ya Yi Da Za A Daina Kakaka Takunkumi Da Ba Dace Ba Kan Kasashe August 13, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci About Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS News Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Explore Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS

উৎস: HausaTv

কীওয়ার্ড: sai Imam yace Sai Imam yace masu sauraro wadanda suka Sai Imam ya sai Imam ya

এছাড়াও পড়ুন:

Shugaban Iran: Kasuwar jarin cikin gida sirrin nasarorin gwamnati na tattalin arziki

Shugaban Iran ya sanar da cewa gwamnati na aiki don inganta juriya da ingancin tattalin arzikin kasar.

Masoud Pezeshkian, Shugaban Iran, ya yi jawabi a taron Kasuwar Jarin Iran na shekara-shekara mai taken “Juriya, Kirkire-kirkire, Ci gaba,” yana mai jaddada gyare-gyaren manufofin tattalin arziki, kula da albarkatu, da kuma tallafawa masu zuba jari. Ya bayyana cewa gwamnati na aiki don rage cikas ga samar da kayayyaki da ciniki.

Pezeshkian ya nuna muhimmancin yin tarurruka na wata-wata tare da masu zuba jari da masu samar da kayayyaki don nemo hanyoyin magance matsalolin da ake fuskanta.

Ya kara da cewa, “Tanadin kashi 10% na iya adana ganga 800,000 zuwa 900,000 na mai a kowace rana.” Ya kuma nuna cewa samar da wutar lantarki daga hanyoyin da ake sabuntawa ya karu sosai kuma ya tabbatar da cewa gwamnati ta shirya tsaf don biyan bukatun makamashi a lokacin hunturu.

Share

0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Larijani: Hadin gwiwar Iran da Pakistan na taimaka wa zaman lafiya a yankin November 26, 2025 Al-Houthi ya yi ta’aziyyar shahadar babban kwamanda na Hizbullah November 26, 2025 UNIFIL: Isra’ila tana sabawa wa kudurorin MDD a cikin  Lebanon November 26, 2025 Matsalolin Tsaro A Yankunan Bakin Ruwa A Kasar Siriya Ya Kai Ga Zanga-Zangar Lumana November 26, 2025 Aljeriya Ta Bukaci Kasashen Duniya Su Dauki Mataki Don Kawo Karshen Ta’asan HKI A Yankin Asiya Ta Kudu November 26, 2025 Shugaban Majalisar Koli Ta Taron Kasa Iran Ya Yabawa Pakistan Saboda Goyon Bayanta November 26, 2025 EU da AU na taro kan diyya ga laifukan mulkin mallaka da cinikin bayi November 25, 2025 Hizbullah: Isra’ila na kure idan ta na tunanin kashe-kashe zai kawo karshen kungiyarmu November 25, 2025 Tashar Press TV ta kaddamar da sashen harshen Hebrew November 25, 2025 Bincike : Isra’ila Ta Kashe Falasdinawa Akalla 100,000 a Gaza November 25, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci About Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS News Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Explore Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Mutuwar Sheikh Dahiru Bauchi Babban Rashi Ne Ga Kasa Baki Daya- Shugaba Tinubu
  • Mutuwar Sheikh Dahiru Bauchi Babban Rashi Ne Ga Kasa Baki Daya
  • Sheikh Dahiru Bauchi: Malamin da zuri’arsa ta fi kowacce yawan mahaddata Alkur’ani
  • An Zabi JMI A Cikin Majalisar Zartarwan Ta Hukumar Yaki Da Makaman Guba Ta Duniya CWC
  • Juyin mulki ya rutsa da Jonathan a Guinea-Bissau
  • Ɗan bindiga ya harbe sojoji 2 a fadar shugaban Amurka
  • Shugaban Iran: Kasuwar jarin cikin gida sirrin nasarorin gwamnati na tattalin arziki
  • Kotu ta yanke wa mutum 5 hukuncin rataya a Oyo saboda aikata kisan kai
  • UNIFIL: Isra’ila tana sabawa wa kudurorin MDD a cikin  Lebanon
  • ’Yan Majalisar Kudu sun roƙi Tinubu ya yi wa Nnamdi Kanu Afuwa