HausaTv:
2025-08-13@20:54:04 GMT

Kissoshin Rayuwa: Sirar Imam Hassan (a) 125

Published: 13th, August 2025 GMT

125-Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na kissoshin rayuwa shiri wanda yake kawo maku kissoshi wadanda suka zo cikin alkur;abi mai girma ko cikin wasu littafan wadanda suka hada da Dastane Rastan na Aya. Shahid Murtada muttahari ko littafin Mathnawa na maulana Jalaluddin rumi ko kuma cikin wasu littafai.

Da fatan masu sauraro zasu kasance tare da mu a cikin shirimmu nay au.

////…Madallah masu sauraro, idan kuna tare da mu a cikin shirimmu da ya gabaya, a kuma cikin sirar Imam Hassan Akmujtaba (a) dan Fatima (s) diyar manzon All…(s). da muke kawo maku. A shirimmu na karshe mun kawo maku yadda amirulmuminina (A) ya yi zango a wani wuri da ake kira Rabzata a kan hanyasa ta zuwa Basra, daga nanan ta tada mutane har sau ukku zuwa Kufa da farko ya aiki Mohammada dan Abubakar da kuma Muhammad dan Jaafar Dayyar, da sako zuwa wajen Abumusa Alashari walin Immam a Kufa, amma ya ki ya aiwatar da umurnin Imam (a) na tara kasa mutanen Kufa su taimaka masa a yakin da  Talha da Zubair, bayan ya ga haka sai sake Aika masa da Hashim al-Mirqal tare da wata wasikar inda a cikin yay a bayyana masa cewa ya bar Hashin ya kira mutane zuwa ga jihadi tare da shi, kuma ya san cewa bai sanyashi gwamnan kufa don yayi abinda yaga dama ba, ya aikeshi ne don ya taimaka masa.

Amma Abumusa Al-ashari ya ki sauraronsa, daga nan sai ya aiki tawaga ta uku wacce to kunshi dansa Imam Hassan (a) tare da Ammar dan Yasir da wasunsu, tare da wasikar tube abu musa a matsayin gwamnan Kufa tare da maye gurbinsa sa Qurdhatah dan Kaab Al-Ansari.

Sai dai hakan bai sa Abu musa al-ansari ya dawo daga ra’ayinsa, a nan sai da Iammam Hassan (a) ya hau kansa, yad aka masa tsawa ya kuma bada wuri suka sami damar ya wa mutanen kufa Magana.

A cikin khudubarsa Imam Haasan (a) ya bayyana matsayin babans, na cewa ba mutum wanda za’a yi shakkansa a cikin kyautata al-amuran musulmi ba. Ya kuma tabbatar masu da cewa ko da mutanen kufa basu taimaka masa ba, muhajirun da ansar wadanda suke tare da shi a lokacin sun wadatar da shi, Ya ce mutanen Kufa su fita tare da babansa, su taimakawa All..da manzonsa ya taima ka masu.

Sai Ammar ya tashi yana kodaitar da mutane fita yake tare da Amirul muminin((a) sannan yana masu bayani a kan Uthman yana cewa: Ya ku mutanen Kufa, Idan labarimmu bai zo maku ba, hakaki amma al-amarimmu ya riskeku, Lalle wadanda suka kashe Uthman basa neman uzurin mutane saboda kashe shi, kuma basa musanta cewa su suka kasheshi, kuma sun Sanya Alkur’ani mai girma tsakaninsu da wadanda suke neman hujjar kasasheshi. All..ne yake raya wanda ya raya, sji yake kashe wanda aka kashe, Kuma Talha da Zubair sune mutane na farko da suka fara sukan Uthman kuma sune na karshe da suka bada umurni a kashesu. Banda haka sune na farko da suka yi mubaya,a ga (amirulmuminina (a). A lokacinda suka ga cewa sun yi kuskuren abinda suke fatan samu a wajensa, sai suka kwance bai’arsu ba tare da wani dalili ba.

Ga kuma dan diyar manzon All..(a) ya zo don neman ku fita yaki. Kuma ya nuna muka Aliyu (a) a cikin muhajiruna da wadanda  suke je badar, da Ansar wadanda suka zabi madina mazauna da kuma Imani da musulunci kafin hijira.  

Haka ma Kais dan Sa’ad dan Ubada ya tashi yayi Magana, yana cewa: idan da mun maida wannan al-amarin zuwa ga shura Al-Umariyya, zamu ga cewa Imam Ali ne yafi cancanta. Saboda gabaki dayan wadanta suka rage a shurar basu kai Aliyu (a) cancanta ba.

Don yan shura da suka rage a lokacin sa’ad dan abiwaqqas ne, da Talha da Zubair da kuma shi Amirul muminina(a). An kashe Uthman da kwanaki Amirul muminina (a) ya ki karban khalifanci, amma mutane suka ce, ba zasu yiwa kowa bai’a bas ai Aliyu(a) ga kuma Talha da Zubair da Sa’adu dan Abi wakkas, duk .suka dage sai Aliyu (a).

Banda haka a taron shura Umari, Zubair ya bawa Ali (a) Quri’arsa, Talha da Sa’ad dan Abiwaqqas duk sun bawa Uthman a bawa Uthman kuri’arsa. Sannan shugaban shurara Abdurrahman dan Auf  ya zabi Uthman bayan da Aliyu (a) ya ki amincea da sharuddansa.

Da imam (a) yana son Mulki da ya karba, amma ya ki sai dan Aufa ya bashi da sharuddan da ya shimfidawa Ali (a) ya karba da sharuddansa, amma bai yi aiki da ko wanne daga sharuddan da ya kar ba.

Amma bayan da mutane suka yiwa Imam Bai’a daga ciki har da Talha da Zubair, wannan kawai ya isa hujja a halatta jininsu. Ballantana sun aikata laifuka da dama.  

Don haka daga karshen saida suka tilastawa Abu Musa Al-ashari fita daga gidan gwamnati a Basra. Sannan suka fita da mutanen kufa zuwa wajen Amirul muminina (a) wanda a lokacin ya isa wani wuri da ake kira zeeqar kan hanyar Basra daga kufa. Idan zaku tuna Aisha ma ta yi zango a nan kafiya .

Don haka ya zama duk wanda Abdurrahman dan Auf ya zaba shi ne Khalifa, amma sai fara da Aliyu (a) inda ya shamfida masa sharudda idan ya  amince zai bashi. Sai Imam ya ki amincewa da sharuddan da danAuf shimfida masa na bin sunnar Abubakar da Umar.

A lokacinda Imam Hassan (a) ya gake da jujjuwar Abumusa sai ya yi masa tsawo yana cewa: {Ka ajiye mana shugabancinmu ya kai wannan mutum, ka nisanci mimbarimmu, …}

A lokacinda yayi fushi da Abumusa alashari, sai ya juya wajen mutane dana kodaitar da su taimakawa mahaifinsa a cikin khudubarsa yana cewa :  Ya ku mutane! Ku karbi kiran shugabanku. Ku je ku hadu da yan’uwanku. Sai an samar da wadanda zasu rike wannan aikin, wanda zai fito yaki. Na rantse idan ma’abuta hankali suka karbi shugabancin sa, Abin buga misali a duniya sannan Alkhairi garesu daga karshe, ku karbi kirammu, kan abinda aka jarrabamu da mu da ku a kansa.

Ya ku mutane: Amirulmuminina (a) yana fada .Lalle ne na fito fitowata kan cewa wannan Azzalumine ko wanda aka zalunta. Lalle ni ina tunatar da ku All…duk wani mutum wanda ya ga gaskiya ya fito, idan ya ga cewa ni ne aka zalunta ya taimaka mani, idan kuma na kasashen azzalumi ne, ya kwace halli daga wajen na.

Na rantse da All..Lallei Talha da Zubair sune suka fara  yi mani bai’a   kuma sune suka fara yaudarata. Shin na dauki wata dukiya ne kebe kaina da ita ne. Ko na sauya wani hukuncin All..ku fito yaki tare da ni, ku fito ku yi umurni da mai kyawu, ku kuma hana marasa yau.}

Sai kawai mutane suka ce mun amince zamu ji mu bi, suna cewa mun amince da jagoranci,

Amma duk tare da wannan nasarrar da suka samu. Malikil Ashtara yana ganin sai an fitowa Abumusa da karfi. Don haka da shi da wasu mutanesa sun je sun yiwa gidan gwamnati a kufa kawayya. A lokacinda yaransa suka ga haka sai suka yi sauri suka je suka fada masa. Suan cikin tsoro suna cewa: Ya Aba musa, ga Asya rya shiga gida ya kuma dakemu yana cewa mu fita.

Sai Abu musa ya sauka daga gidan fada sai Ashar ya ce masa ka fita daga gidammu,..) ya yi ta nanata masa, ka fita daga gidammu, kai munafiki ne. daga nan sai Abu musa ya fada da sauti mai Rauni: Ku yi mani hakuri zuwa yammacin yau.

Sai Ashtar ya ce masa, kada ka kwana a nan wannan daren. Suka fara wawason kayakinsa, sai Ashat yace masu su daina, mun jinkirtamasa zuwa daren. Sai mutane suka daina.

A lokacinda gari ya waye, Al-as’ari ya fita daga gidan gwamnati. Sai Imam hassan (a) ya sake tara mutane yana kodaitar da su shiri don fita yaki. Sannan yace masu: Ya ku mutane, Ni zan tafi wanda yake so ya fita da ni a haye, sai mu tafi tare wanda kuma yake son fita ta Ruwan kogi yana iya yi.

Daga nan nasara ta bayyana fili mutane sun fara Shirin fita tare da Imam Al-Haasan (a ) don riskan mahaifsa Amirul muminina(a). a Zeekar yana jiransu, yayi kuma farin ciki da abinda ya faru.

Sai wata karyan da aka yiwa Imam Hassan (a), wanda Dabari ya kawo a cikin littafinsa Attarikh, inda yake cewa: Imam Hassan (a) ya zo wajen mahaifinsa bayan fitowar Talha da zubair, sai yace masa: Na umurceka ka saba mani, sai gashi a yau za’a kasheka saboda sakacinka. Baka da mataimaki.

Sai Imam Ali (a) ya ce masa: Baka gushe ba kana kokanka kamar kuka kuyanga. Me ka umurceni na sabamaka?

-Na umurceka a ranar da aka kashe Uthman ka bar Madina a kasheshi baka nan. Sannan na umurceka, a randa aka kasheshi kada ka yarda ayi maka bai;a, san an zo maka da bai’ar dukkan birane da kuma larabawa. Sannan na umurceka, a lokacinda wadan nan mutane 2 suka yi abinda suka yi, ka zauna a gidanka har sai sun sulhunta a tsakaninsu, don haka idan wani abu y abaci ba a hannunka, sai dai a hannun wanika. Amma sai ka saba mani.

Sai Imam ya bashi amsa da cewa: Ya da : Amma zancenka da na bar madina a lokacinda aka yi kofar ragowa gida Uthman, ai muma an yiwa gidammu kawanya kamar yadda aka yi wa uthman. Amma zancenka kada ayi maka bai’a sai an kawo maka bai’ar birabe. Ai al-amari na mutanen madina ne, ba ma son hakan ya kubuce mana. Amma  zancenka a lokacinda Talha da zubair suka fita. Wannan ai wulakanci ne ga addinin musulunci. Na rantse da All..ban gushe ba, an rinjayeni tun lokacin da na karbi shugabancin. …

Amma zancenka ka zauna a gidanka. To yaya zanyi bayan ya zama dole. ,,, har zuwa karshenn maganarsa.

Wannan hadisin Tabari ya ruwaitoshi daga saifu dan Umar wanda malamai sun gamu a kan cewa makaryaci ne yana kuma kirkiro hadisai. An san shi da karya da kuma kirjiranbn hadsai.

Sannan yadda muka san iyalan gidan manzon All..(s) ta yayi Imam Hassan zai umurci babansa. Imam Hassan da kansa (a) bayan Jana’izarsa yana cewa . Lalle na farko basu fishi aikiba, wadanda zasu zo ba zasu riske shi ba. Wannan hadisin ya sabawa halayen Imam Hassan.

Masu saurararo a nan zamu dasa aya a cikin shirimmu nay au ai kuma wata fitowa idan All..ya kaimu. Wassalamu alaikum wa rahmatullahi wa barakatuhu.

Share

0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Kissoshin Rayuwa: Sirar Imam Hassan (a) 124 August 13, 2025 Iran: Babu Mika Kai Ga Takurawar kasashen Yamma har sai An Kawo Karshen Barazana August 13, 2025 Hukuma Mai Kula Da Sauka Da Tashin Jiragen Sama A Paris Ya Dakatar Da Wani Ma’aikacinta August 13, 2025 Iraki Tace: Ita Yentacciyar Kasashe Ce Bayan da Amurka Ta Yi Korafi Kan Yarjeniyar tsaro da Iran August 13, 2025 Ministan Harkokin Wajen Masar Ya sake Ganawa da Aragchi Da Kuma Gorossy August 13, 2025 Shugaban Kasar Iran Ya Jaddada Alhininsa Kan Kashen Masanan Kasar Iran Da ‘Yan Sahayoniyya Suka Yi August 13, 2025 Ministan Harkokin Wajen Iran Ya Jaddada Cewa: Lokaci Ya Yi Da Za A Daina Kakaka Takunkumi Da Ba Dace Ba Kan Kasashe August 13, 2025 Sakataren Majalisar Kolin Tsaron Kasar Iran Ya Jaddada Kasancewar Iran Tare Da Kasar Lebanon Koda Yaushe August 13, 2025 Kasar Iraki Ta Ce: Yarjejeniyar Da Ta Kulla Da Iran Zai Amfani Dukkan Kasashen Yankin August 13, 2025 Sojojin Yemen Sun Kai Hare-Hare Kan Haramtacciyar Kasar Isra’Ila Har Sau Shida  August 13, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci About Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS News Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Explore Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS

উৎস: HausaTv

কীওয়ার্ড: wadanda suka Ya ku mutane

এছাড়াও পড়ুন:

Fursunoni 16 sun tsere daga gidan yarin Keffi

Ana fargabar cewa wasu fursunoni 16 sun tsere daga gidan yarin Keffi da ke Jihar Nasarawa bayan wani kwantan bauna da suka yi wa gandirebobi.

Wata sanarwa da mai magana da yawun Hukumar Kula da Gidajen Gyaran Hali a Nijeriya, Umar Abubakar, ta ce fursunonin da ke gidan sun yi wa ma’aikatan da ke tsaronsu rubdugu, lamarin da ya bai wa mutane 16 damar guduwa a safiyar wannan Talatar.

An kama ɗan shekara 18 kan zargin fashi da makami a Gombe An kama basarake kan zargin yi wa ’yar shekara 12 fyaɗe a Gombe

Sanarwar ta ce biyu daga cikin jami’ai biyar da suka ji rauni a yayin harin na cikin mawuyacin hali, kuma yanzu haka ana duba lafiyarsu a wani asibitin gwamnati.

Ya kara da cewa an kamo mutumin bakwai daga cikin waɗanda suka tsere yayin da ake ci gaba da neman ragowar fursunoni tara.

Sanarwar ta ambato cewa Kwanturola-Janar na Hukumar Gidajen Gyaran Hali a Nijeriya, NCoS, Sylvester Nwakuche, ya ziyarci wurin bayan faruwar lamarin, inda ya bayar da umarnin gudanar da cikakken bincike tare da gargaɗin cewa duk wani ma’aikaci da aka samu da hannu zai kuka da kansa.

Haka kuma, Nwakuche ya ba da umarnin a gaggauta fita samamen haɗin gwiwa da sauran hukumomin tsaro domin kamo waɗanda suka tsere.

Mahukunta sun yi kira ga jama’a da su kwantar da hankalinsu, tare da neman su hanzarta bayar da rahoton duk wani motsi ko alamar mutanen da suka tsere ga ofishin tsaro mafi kusa.

A ‘yan shekarun nan dai, an samu tserewar fursunoni a Nijeriya lokuta daban-daban, inda a bara kaɗai, fursunoni 118 sun tsere daga gidan gyaran hali na Suleja a Jihar Neja, bayan ruwan sama mai karfi ya lalata bangon gidan yarin da ake cewa daɗewarsa ce ta janyo rushewar ginin.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Kissoshin Rayuwa: Sirar Imam Hassan (a) 130
  • Kissoshin Rayuwa: Sirar Imam Hassan (a) 129
  • Kissoshin Rayuwa: Sirar Imam Hassan (a) 128
  • Kissoshin Rayuwa: Imam Hassan (a) 127
  • Kissoshin Rayuwa: Sirar Imam Hassan (a) 126
  • Kissoshin Rayuwa: Sirar Imam Hassan (a) 124
  • DAGA LARABA: Yadda sinadaran dandanon abinci ke yin illa ga lafiya
  • Fursunoni 16 sun tsere daga gidan yarin Keffi
  • Tireloli Sun Yi Taho Mu Gama, Mutane 4 Sun Jikkata A Titin Zariya–Kaduna