HausaTv:
2025-10-13@15:49:54 GMT

Kissoshin Rayuwa: Sirar Imam Hassan (a) 128

Published: 13th, August 2025 GMT

128-Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka  barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na kissoshin rayuwa shirin wanda yake kawo maku kissoshi wadanda suka zo cikin alkur’ani mai girma ko cikin wasu littafai wadanda suka hada sa littafin Dastane Rastantan ko kuma cikin littafin mathnawi na maulana jalaluddeen Rumi ko kuma cikin wasu littafan da fatan masu sauraro zasu kasashence tare da mu a cikin shirimmu na yau.

///… Madallah, masu sauraro idan kuna tare da mu a cikin shirimmu da ya gabata a kuma cikin sirar Imam Al-Hassan Al-Mutaba, (a) dan Fatima (s) diyar manzon All..(s) da muke kawo maku, a cikin shirimmu da ya gabata. Mun bayyana yadda Imam Ali (a) ya kammala hujja a kan mutanen Jamal bayan bi hanyoyi da daman a hana zubar da jinin musulmi amma suka ki amincewa.

Abu na karshe da yayi shi ne ya fiyar da mushafin alkur’ani ya fara bin sahu-sahu na sojojinsa, yana cewa wa zai karbi wannan alkur’ani ya bijiro masa, ya ce masu wannan ya shiga tsakanim, ina kiranku zuwa ga littafin All..idan an yanke damarsa, ya rike da hannunsa na hagu idan an katse ta da hakoransa, ya ce za’a kasashe shi. Sai wani matashi dan kufa ya ce shi zai yi. Da farko Imam (a) ya yi watsi da shi, amma ba wanda ya amsa kiransa sai wannan matashin sai daga karshe ya bashi, ya kuma bayyana masa abinda zau fada masu.

Wannan matashin. ba tare da tsaron ba ya je ya aiwatarn da umurnin Imam, kamar yadda ya umurceshi, ya kuma kai ga shahada.

Daga nan ya ce jininsu ya halatta da wannan manzonsa na karseh da suka kashe. Don haka ya kira kwamandojin sojojinsa ya kuma bayyana masu dokokin yaki, musamman a yaki tsakanin musulm mi. Ya hanasu, kashe wanda suka ji rauni, kada su bi wanda ya gudu, kada su kashe wanda ya bada baya, kada su dauki ganima sai makamai da abin hawa a yaki. Sauran abinda ya rage na dukiyoyinsu, kamar kuyangu, bayi da sauransu na masu gadonsu ne, kamar yadda alkur’ani ya kawo.

Sannan ya bawa dansa Muhammad ibnul Hanafiyya, tutarsa, a lokacinda aka fara yaki sai ya ga rauni a waje, sai yazo ya karbi tutar a wajensa ya kuma kutsa tsakiyar yakin yana kashewa dama da hagu.

Sannan munji yadda ya hadu da Zubai a tsakiyar yakin ya kuma tunatar da shi hadisin wanzon All..(s) gareshi cewa zai yake shi, sai Zubair ya fita daga cikin yakin, amma ya je wani wuri wajen yakin sai wasu mutane tare da Al-Ahnaf  suka kashe shi yana basu sallah. Wannan shi ne karshen Zubair.

Sanna da alamun an bada umurni a kashe shi daga rundunar Aisha bayan ya fice daga cikinsu.

A yakin Jamal babba dai, kabilu 3 ne suka fi taimakawa runduranr aisha, kabilar Al-Azdi da Banu dhubba, da kuma banu Najiya. Malaman tarihin sun bayyana cewa Banu al-Al-azdi, wadanda suke kewaye da rakuminta suna rare kasidu na yabonta.

An ruwaitota tana yabonsu, suka kuma mutuwa a gabanta. Wannan halin ya ci gaba, ko wane bangare yana son kare shugabansa. An yawaita kisa a tsakanin musulmi.

Daga nan Imam Imam(a) ya ga cewa yakin ba zai kawo karshe ba matukar wannan rakumin na aisha tana tsaye.

Sai ya kira Ammar dan Yasir da kuma Malik alashtar biyu daga cikin kwamnadojinsa, a lokacinda suka zo sai yace masu: ku je ku buke soke wannan rakumin, Lalle yakin ba zai kare ba matukar tana raye, don Lalle sun maida ita Al-kibla..

Daga nan sai suka dauko wasu mayaka suka nufeta, sai wani matashi mai suna  Mu’ammar dan Abdullahi wanda ya buge ta tsakanin guiwa sa cinyanta. Wasu sun ce da farko Imam (a) ya bawa dansa Muhammad dan Hanafiyya kibiya ya habeta, sai yaje ,amma masu gadin Aisha sun hanashi sai ya dawo sannan Imam Hassan ya krbi kibiyar ya je ya kuma sameta a kafarta.

Don haka da aka bugeta a kafa da fada kasa ta yi wani kara wand aba shi da kyau jinsa, kuma ba’a taba jin irin wannan karar ba. Da zaran ta fadi sai wadanda suke kewaye da ita suka tarwatse.  Don gunkin da suka gabatar masa jinni ya fadi.

Daga baya Imam (a) ya bada umurni a konata a kuma watsa tokanta a cikin ruwa ta yadda babu abinda zai rage na jikinta, wanda zai sa wawaye su bauta mata.

Bayan an yi da ita haka, sai yace: All..ya ysinewa wannan dabban, ta yi kamada dan marakin banu isra’ila.

A lokacinda aska ta kada tokanta ya tashi sama sai yace: {Ka yi dubi zuwa ga ubangijinka wanda baka gushe ba kana bautansa  Lallei sai mun kona shi, sannan mu watsa shi cikin kogi watsa wa} Taha 20.

Daga nan sai Imam (a) yayi afwa ga Aisha, ya aika dan uwanta Muhammad dan Abubakar ya je ya fito da ita daga Haudaju, ko rumfan mata a kan rakumi, sai Muhammad ya je ya sa hannusa a cikin haudajun yana neman kama hannunta ya fitar da ita, sai ta janye hannunta, tana cewa, waye wannan

Sai tace: wanda kika fi ki a cikin danginki, sai ta gane shi, tana kyamarsa, sai tace mata ibn Hathamiyya? Sai yace . sai ta juya fuskanta daga gareshi, sai y ace mata akwai abinda ya sameki. Sai tace: wata kibiya amma bata ji mani ciwo ba. Sai ya cireta daga sai ya fito da ita daga Haudajinta, yana tare da ita har ya shigar da ita Basra a cikin dare, a gidann Abdullahi dan Khanaf al-khuzaee. Wajen matarsa Safiyatu yar Haritha. Sai ta zauna yan kwanaki a wajenta.

Imam Ali (a) ya shelanta afwa na gama gari ga dukkan makiyansa, wadanda suka yake shi ko suka yi adawa shi. A cikin wannan halin ne sai Aisha matar manzon All..ta aika wa Imam (a) tana nemawa dan yar’uwanda Abdullahi dai Zubair afwa. Saboda mahaifar Adullahi yayar Aisha  ce, wato  Asmau diyar Abubakar khalif ana farko.

Kamar yadda muka karanta a bayan Abdullahi dan Zubair a yayi khuduba a Basra, yana tuhumar Imam Ali(a) da kashe Uthman a fili, ya kuma bukaci mutanen Basra su dauki fansar jinin Uthman daga Amirul muminina Aliyu dan Abitalib (a). sai Imam Ali (a) yace ya gafarta masa.

Sannan Marwan dan Hakan, ya biyo ta Imam Al-Hassan da Al-Hussain (a) don su nemammasa Afwa daga mahaifinsu Imam Ali (a). shi ma ya amince ya yi masa Fawa. Sanna tun lokacinda aka kawo karshen yakin Imam Ali (a) tura mai shelansa yana shela yana cewa: Ku saurar, kada ku karasa wanda jiwa ciwo, kada a bi Wanya ke ya juya yana gudu, kada a buge wanda ya juya baya yana gudu, duk wanda ya yada takobinsa amintecce ne, wanda ya shiga gidansa ya kulle amintacce ne.  

Sannan Ya’akubi ya kawo a cikin tarihinsa Jz 2 shafi 159, kan cewa aka amintar da baki da ja, sai cutar da mutum ko guda daga cikin wadanda husuma da shi ba. Don haka zai zaman lafiya ya game ko ina bayan yakin. Nutsuwa ta game dukkan yankunan Basra.

Daga nan sai Amirul muminina (a) ya aiki Abdullahi dan Abbas ya je masaukin Aisha matar manzon All..(s) a Basra ya ce mata ta shirya komawa dakinta a Madina, kamar yadda All..ya umurceta. Sai ibnu Abba ya je gidan ya kuma nemi izijin shiga wajenta, sai taki ta bashi ijinin shi wajenta. Sai ibn Abba ya kutsa cikin dakin ba tare da izininta ba, sai ya ga wani batashin kai a dakin sai ya jawo shi ya zauna a kai. Sai ta ji zafi hakan da yayi, sai tace masa. Walla ya kai dan Abbas ban taba ganin irinka ba, ka shiga daki na, ka dauki matashin kai na, ka zauna a kansa  ba tare da amincewarmu ba.!!.

Sai Ibn Abbas yace mata: Na rantse da All..ba dakin ki ba ne, dakin ki kawai shi ne wanda All…ya umurceki ki zauna a cikinsa, kika ki zama a cikinsa. Kuma lallai Amirul muminina ya umurceki ki koma zuwa garinki inda kika fito.

A nan sai ta kara bayyana kiyayyarta ga Amirulmuminina (a), inda ta maiyarwa ibn Abbas Ammsa tna cewa: All..ya jikan Amirulmuminina, shi ne Umar dan Khaddab. Sai ibnu Abbas yace: Haka ne, amma wannan Aliyu dan Abitalib shi ma Amirulmuminina ne.

Sai tace: naki na ki.

Sai  yace: Kinki da hakan, na wani lokaci ne kadan, kamar tatsa da tatsa. Sai ki zama ba zaki iya hallatawa ba, ba zaki haramta ba, ba zaki bada umurnin ba ba zaki hana ba.  

Sai ta karaya da maganarsa, ta zubar da hawayenta sai tace: Haka ne, zan koma, lallai mafi munin gari a waje ne, shi ne garin da kuke zama. Sai ya ce mata: Amma na rantse da All..ba wannan ne ya kamata ya zama sakamakommu daga wajenki ba. Saboda mun sanyaki mahaifiyar muminai…..

Sai ta ce: Kana mani gori da manzon All..(s) ne? sai ya ce: Ee!! muna maki gori da wanda da kina da irinsa da kin mana gori da shi. Sai ya fita ya barta.

Sannan ya koma wajen Amirulmuminina (a) ya fada masa abinda ya faru, da kuma kalaman da suka gudana a tsakaninsu. Har’ila yau da amincewarta da umurninsa na ta koma madina. Sai yace masa ya yi dai dai.

Sannan Imam (a) ya shirya mata Ayari cikakkiya na musamman, a ranar da aka ajiye zata fita sai Imam (a) ya shiga wajenta tare da yayansa Imam Al-Hassan da Al-Hussain (a).

Share

0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Kissoshin Rayuwa: Imam Hassan (a) 127 August 13, 2025 Kissoshin Rayuwa: Sirar Imam Hassan (a) 126 August 13, 2025 Kissoshin Rayuwa: Sirar Imam Hassan (a) 125 August 13, 2025 Kissoshin Rayuwa: Sirar Imam Hassan (a) 124 August 13, 2025 Iran: Babu Mika Kai Ga Takurawar kasashen Yamma har sai An Kawo Karshen Barazana August 13, 2025 Hukuma Mai Kula Da Sauka Da Tashin Jiragen Sama A Paris Ya Dakatar Da Wani Ma’aikacinta August 13, 2025 Iraki Tace: Ita Yentacciyar Kasashe Ce Bayan da Amurka Ta Yi Korafi Kan Yarjeniyar tsaro da Iran August 13, 2025 Ministan Harkokin Wajen Masar Ya sake Ganawa da Aragchi Da Kuma Gorossy August 13, 2025 Shugaban Kasar Iran Ya Jaddada Alhininsa Kan Kashen Masanan Kasar Iran Da ‘Yan Sahayoniyya Suka Yi August 13, 2025 Ministan Harkokin Wajen Iran Ya Jaddada Cewa: Lokaci Ya Yi Da Za A Daina Kakaka Takunkumi Da Ba Dace Ba Kan Kasashe August 13, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci About Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS News Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Explore Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS

উৎস: HausaTv

কীওয়ার্ড: kamar yadda

এছাড়াও পড়ুন:

Yadda Haɗa Jinsin Shanu A Zamance Zai Ƙara Samar Da Madara

Ya kara da cewa, ana ci gaba da kokari don ganin an iske masu yin kiwon shanu a kasar nan, domin fadakar da su kan muhimmancin rungumar wannan tsari na zamani.

 

Sai dai, ya yi nuni da cewa; wasu al’adu na haifar da tarnaki a tsakanin wasu masu kiwon a kasar na rungumar wannan tsarin.

 

“Na ga wasu gidajen gona da ake yin irin wannan dabara ta zamani, sannan kuma ana bayar da kulawar da ta kamata; wanda hakan ya sanya ake iya samar da litar madarar shanu daga tsakanin lita 15 zuwa 30,” in ji Jatau.

 

“Akwai wasu Fulani Makiyaya ‘yan kalilan da suka rungumi wannan tsari, misali a Jihar Bauchi; inda wani makiyayi ya rungumi wannan tsari tare kuma da amfanarsa yadda ya kamata,” a cewarsa.

 

“A lokacin da muka gudanar da ayyukanmu, wasu daga cikin Fulani Makiyaya, sun zo sun saurari wannan batu na dabara ta zamani tare da shanunsu, mun kuma aiwatar da tsarin a kan shanun nasu, inda daga baya suka ga yadda madarar shanunsu ta kara habaka,” in ji shi.

 

Jatau ya kara da cewa, suna kan ci gaba da bai wa Fulani Makiyaya kwarin guiwa, kan rungumar wannnan tsari, sai dai, wasu na fuskantar kalubale na kula da shanunsu da aka dora su a kan tsarin.

 

“A wasu kasashen na Afirka za ka cewa, Makiyayin da suka rungumi wannan tsari, na da shanu uku ne kacal da daukacin iyakansa suka dogara a kansu, wanda hakan ke ba su dama a kullam na samar da litar madara daga tsanakin 15 zuwa 20, “ a cewarsa.

 

Ya kara da cewa, hakan ya sanya a kullum suke samar wa da kansu dimbin riba, wanda kuma hakan ya sa ba su dogaro da aikin gwamnati ba kwata-kwata.

 

Ya yi nuni da cewa, idan har a raba daya za ka sayar da litar madara daya kan Naira 1,000, a wata za ka iya samun kudin shiga da suka kai Naira miliyan 1.8 da shanu uku kacal.

 

Ya ci gaba da cewa, da wannan ribar kadai za ka iya ci gaba da ciyar da shanun da lula da lafiyarsu da biyan ma’aikatan da ke kula da su da kuma daukar sauran dawainiyar kula da iyalanka.

 

Ya bayyana cewa, duba da cewa; ana fuskantar matsalar wajen da dabbobi za su yi kiwo a kasar nan, amma idan Fulani Makiyaya suka rungumi wannan tsari, hakan zai rage yawan samu rikice-rikice a tsakanin manoma da Fulani Makiyya a kasar.

 

Kazalika, ya sanar da cewa; idan masu kiwon suka dauki wannan tsari za a samu cewa, alfanun da za su samu ya dara irin na kiwon gargajiya da ake yi a cikin kasar.

 

Jatau ya bayyana cewa, wannan tsarin abu ne da ke da tsawon tarihi a kasar nan, domin an faro shi ne tun a shekarar 1949; tun bayan da aka dauki nau’in na jinsin daga wata gona da ke garin Shika a birnin Zaria, aka kuma kai shi zuwa cibiyar gudanar da bincike kan lafiyar dabbobi ta Bom.

 

Sai dai, ya bayyana cewa; rashin ci gaba da bibiyar wannan tsare-tsaren daga bangaren gwamnati, hakan ya haifar da koma baya ga wannan tsair.

ShareTweetSendShare MASU ALAKA Noma Da Kiwo Nazari Kan Yadda Za A Iya Samun Wadatacciyar Riba A Kiwon Jimina October 3, 2025 Noma Da Kiwo Hikimar Gwamnatin Tarayya Ta Tallafa Wa Manoman Jihar Edo October 3, 2025 Noma Da Kiwo Gwamnatin Tarayya Ta Kaddamar Da Shirin Bunkasa Kiwon Kifi September 27, 2025

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • An Wallafa Ra’ayoyin Shugaba Xi Kan Batutuwan Da Suka Shafi Mata Da Yara Cikin Karin Harsunan Waje
  • Mutane A Fadin Duniya Sun Soki Ayyukan Neman ‘Yancin Kan Taiwan
  • Ayyukan Da Suka Sauya Fuskar Zamfara A Ƙarƙashin Gwamna Dauda Lawal
  • Maryam Sanda na cikin waɗanda Tinubu ya yi wa afuwa
  • ’Yan sanda sun ceto mutum 10 daga hannun ’yan bindiga a Kaduna
  • Tarihin Hassan Usman Katsina (1)
  • Masana Sun Bayyana Yadda Za A Magance Ficewar Kamfanoni Da Masana’antu Daga Nijeriya
  • Wasu Daga Cikin Muhimman Alamomin Ciwon Kansa
  • Yadda Haɗa Jinsin Shanu A Zamance Zai Ƙara Samar Da Madara
  • Kasar Sin Ta Samu Manyan Nasarori A Fannin Inganta Walwalar Yara Da Tsoffi Cikin Shekaru 5 Da Suka Gabata