HausaTv:
2025-08-13@20:51:47 GMT

Kissoshin Rayuwa: Sirar Imam Hassan (a) 126

Published: 13th, August 2025 GMT

126-Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da haka barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na kissoshin rayuwa shiri wanda yake kawo maku kissoshin da suka zo cikin alkur’ani mai girma ko kuma cikin wasu littafan wadanda suka hada da littafin Dastane Rastan na Aya. Shahid Murtadha Muttahhari, ko kuma cikin littafin mathnawa na maulana Jalaluddeen Rumi ko kuma cikin wasu littafan da fatan masu sauraro zasu kasance tare da mu.

////… Madallah, masu sauraro idan kuna tare da mu a cikin shirimmu da ya gabata a kuma cikin sarir Imam Al-Hassan Almujtaba (a) diyar Fatima (s) kuma jikan manzon All..(s) na farko da muke kawo maku, idan kuna tare da mu a cikin shirimmu da ya gabata mun bayyana yadda. Imam Al-Hassan (a) tare da sahabban manzon All…(s) da dama suka fuskance Abu-Musa Al-ashari, har sai da suka fidda shi daga gidan gwamnati, sannan suka shawo kan mutanen kufa suka amince su fita yaki tare da Imam amiril muminina Aliyu dan Abi talib (a). Sannan daga karshe Imam Hassan ya fadawa mutanen kufa kan cewa, daga yanzun Urdatuh Ibn Kaab bin Thalaba al-ansari shi ne walin Kufa.

Sannan ya ce masu duk wanda yake da abin hawa ya bini mu wace wadanda kuma zasu bi ta ruwa suna iya bi.

Sannan daga karshe mun yi magana kan cewa, an yiwa Imam Al-Hassan (a) karya, dangane da shi da Mahaifinsa, Imam Ali (a), kamar yadda Tabari ya kawo a cikin tarihinsa ya ruwaito hadisin daga Saifu dan Umar Attamimi, wanda malaman da dama suna tuhumarsa da kariya da kuma kirkiro hadisai ya jinginawa manzon All..(s).

A cikin hadisin ya na cewa, Imam Hassan (a) yana umurtan mahaifinsa yayi wasu abubuwa amma yana saba masa, kama sanadiyyar haka ya fada cikin matsaloli. Kumma dukkan abubuwan sun shafi kissan Khalifa Uthman ne da kuma bai’a was hi Imam (a). Mu bayyana bayyan cewa, girmamawa da ladabi ga mahaifi da kuma limamin zamani wani al-amari ne wanda babu shakka a cikin iyalan gidan manzon All..(s) tsarkaka, don haka shi ya sa basa sabani a tsakaninsu. Wannan kuma ya nuna mana yadda musulmi da dama basu san matsayin Aliyu (a) a wajen All.. da kuma matansa da yayasa 11 masu tsarki ba.

Don haka baya da mutanen suka hadu da sauran wadanda suke tare da Imam (a). sai suka kama hanyan basra suna sauri. A lokainda ya isa wani wuri kusa da Basra wana ake kira ‘Zawiyya’ sai yayi zango a nan, sannan ya yi sallah raka’o’I 4 sannan yayi ta murgude kumatunsa a kasa yana zubar da hawaye yana addu’a, inda a ciki yana rokon All.. taimako kan wadanda suka zalunci shi, wato Talha da zubair, sannan ya roki All… ya tsare jinin musulmi da zuba a tsakaninsu.

Da ya kammala sai nana take, ya aiki Ubaidullahi dan Abbas da Zaidu dan Sauhan zuwa wajen Aisha su fada mata, kan cewa ta dakatar da zubar da jinin musulmi, ta kuma yi kokarin hada kansu. Yace masau:

{Ku fada mata, All..ya umrceki ki zauna a gidanki, kada fi fita daga gidan, kuma Lalle kin san hakan, sai dai wata jama’a ta rude ki, sai kika fito daga gidanki, sai mutane suka fada cikin bala’ii da da wahala, saboka haduwarsu da ke, abinda yafi maki alkhairi shi ne ki koma gidanki, kada ki shiga cikin jayayya da ya shafi yakin nan, to idan baki koma ba , kabi dushe wannan wutar fitina da kika kunna ba, to kuwa karshensa yaki ne, kuma za’a kashe mutane da dama saboda cikinsa, ki ji tsoron All…yak e Aisha, ki tuba zuwa ga All…, don lalle shi All..mai karban tuba ne, daga bayinsa, kuma yana yin afwa. Ana jiye maki tsoro kan son Abdullahi dan Zubair da dangin Talha, zuwa wani abinda karshensa wata ne}.

Da Aisha ta ji wannan nasir da yayi mata, dai ya fiye mata Alkhairi, ga kuma Al-ummar gaba daya. Amma ta sanya wannan nasihar bayan kunnenta, sai ta fadawa manzannin Imam (a). Lalle ni, ba zan mayarwa Aliyu dan Abitalib da wata magana ba, don ni bai kai ga hujjacewa da shi ba} gaskiyan ita ce, bata da hajjan da zata bawa Aliyu (s) a kan abinda ta aikata ba.

Sanna Imam (a) ya aikawa Talha da Zubair, yana kiransu da kawo karshen rarraba kamar yadda ya zo cikin wannan nassin.

{Bayan haka, hakika kun sani ko da kun buye shi, ni ban bukaci mutane su yi mani bai’a a matsayin Khalifa ba, su suka nemi in zama shugabansau, ban karbi bai’arsu ba sai da suka suka matsa mani da yin hakan, ku biyu din nan suna daga cikin wadanda suka zo mani da batun bai’a a gareni, kuma kuka yi mani bai’a, Kuma lalle sauran mutane basu yi mani bai’a ba, don samun iko ba, a cikin mafi yawansu, ko kuma don su sami wani abin duniya ba, idan har kun yi mani bai’a kuna masu biyayya to ku dawo ku tuba zuwa ga All..da sauri. Idan kuma kun mani bai,a ba tare da kuna so ba, to amma kun bani hujja a kanku, tare da bayyana biyayarku, sannan a dayan bangaren kuma kun dage a kan sabonku.

Na rantse da All..ba ku ne kuka fi cancantar yin takiyya ko boye abinda ke zukatanku ba,  a cikin wadanda suka yi hijira ba, ai wallah da kun ki yin bai’ar tun farko, kafin ku shigeta da ya fi maku fadi, a kan yin bai,a da kuma warware shi bayan haka ba.

Sannan kun riya cewa ni na kashe Uthman, shin tsakanina da ku, wa ye baya nan daga cikin mutanen Madina, idann har za’a luzumtawa ko wani mutum gwagwadon abinda ya aikata, Yak u dattawa biyu ku dawo daga wannan ra’ayinku, babban abinda zai sameku idan kun dawo shi ne kunya a duniya, ku tuba kafin kunya da kuma wutan Jahannama su taru gareku, wassalam}.

Amma sun ki amsa kirin Imam (a), sun ci gaba da nuna turjiya. Sanna Abdullahi dan Zubair dan Awwam ya tashi yayi magana. Kafin haka, shi yafi kowa hargitsa al-amuran Imam Ali(a) na dakatar da yaki da kuma hana zaman, lafiya, ya tare wasu mutanen Basra, yana harzukasu su yaki Imam (a). kuma shi ne ha bata dukkan shirye-shiryen Imam (a) na kada a kara zuabar da jinin musulmi, bayan wanda suka yi kafin isarsa basra.

Ga abinda Abdullahi dan zubair yake fada a lokacin: “Ya ku mutane! Lalle Aliyu dan Abitalb (a) ya kashe Khalifa Uthman da gaskiya, sannan ya tada rundunonin yaki don ya mamaye ku, ya kuma kwace birninku, ku kasance mutane, masu neman fansar jinin Khalifanku, ku kare haruminku, ku yi yaki don kare matanku da yaranku. Da kuma danginku da matsayinku da mutanenku. Shin kuna son mutanen kufa su kwace garinku? Ku yi fushi an fusatar da ku. Ku yi yaki an yakeku. Ku saurar Lallai Aliyu baya ganin wani yana tare da shi a cikin wannan al-amarin shugabanci sai shi.

Wallahi idan ya sami iko a kanku sai ya halaka addinin da duniyarku.”

Khudubar gaba dayanta a cikin da karya da kuma kokarin ingiza mutanen Basra su yaki Amirulmuminin (a). sannan shi kansa Abdullahi dan Zubair ya san cewa abinda ya fada a khudubarsa dangane da Amirul muminin (a) musamman na cewa shi ya kashe Khalifa Uthman karyace. Sai ya fadi abinda ransa ya sawwala masa ne kawai.

A lokacinda Imam Ali (a) ya ji abinda Abdullahi dan Zubair ya fada, sai ya fadawa dansa Imam Al-Hassan ya mayar masa, ko yayi masa radda.

Sai Imam Al-hassan (a) ya tashi ya yi khuduba ya godewa All..ya kuma yabe shi : Ya ku mutane, hakaki maganganin dan Zubair danagane da mahaifi na ya riske mu, kan cewa shi ya kashe Uthman, sannan ku ya ku wadanda suka yi hijira da kuma Ansar da waninsu daga cikin musulmi ku kunsan zancen Zubairu dangane da Uthman kafin a kashe shi.da kuma sunan Uthman a wajensa (a lokacin) da kuma tsokanar da yake masa. Kuma shi Talha dan’ubaidullah a lokacin, ya kafa tutarsa a kan Baitul malim (uthman yana da ransa) sannan ga shi a yau suna tuhumar mahaifina da kasashe shi. Suna aibata shi. Da muna son Magana a kansu da mun fada. Amma zancensa na cewa lalle Aliyu ya kwacewa mutane shugabancinsu, wannan shi ne hujja hujja mafi girma ga mahaifi na, ya riya cewa ya yi masa mubaya’a da  hannunsa amma bai yi masa mubaya’a da zuciyarsa ba. Hakika ya tabbatar da cewa yayi bai’a, sannan ya riya cewa bai yarda ba a cikin zuciyarsa, to ya zo da hujja kan cewa bai yarda ba, a cikin zuciyarsa, in zai iya. ?

Amma cewarsa mutanen kufa suna son shigawa mutanen basra kasarsu, menene abin mamaki na ma’abuta gaskiya, sun shigowa mutanen bata? Na rantse da All..mutanen Basra, sus an cewa zamu gamu da su a mahadarmu a ranar kiyama, Randa zamu kai kararsu a gaban All..sai ya hukunta da gaskiya a tsakamimmu, shi ne mafi alkhairin mai rarrabewa.

Amma magoya bayan Uthman, kuma, babu yaki a tsakanimmu da su, babu wata fafatawa, sai dai yakimmu da ma’abuciyar Rakumine ce, da mabiyanta.)

Da haka Imam Alhassan(a). ya mayarwa dan Zubair amma a kan zargin da yakewa babansa na kashe uthman, ya kuma tabbatar masa cewa babansa Zubair da kuma abokinsa Talha bin Ubaidullahi da kuma Aisha matar manzon All..(s) ne suka kashe Uthman, da bakunansu, babansa ya doura tutansa a kan  Baitul malin Uthman tun yana da ransa yana jiran a kasheshi don ya kwace dukiyar musulmu.

Sannan yace, yakinsu da mahayin rakumi ne don ita ta tara dangin uthman, don ta cimma burinta na nisantar da iyalan gidan manzon All.. s daga shugabancin al-ummar kakanshi.

Don haka bayan wadannan wasiku da sakonni da kuma khudubobi, da alamun babu makawa sai an ci gaba da zubar da jinni  musulmi. Don haka Imam Ali (a) ya dauki mataki na karshe, don haka zubar da jinin musulmi, idan har wannan matakin bai sami nasara ba, ba abinda ya rage in banda takobi. Wannan matakin dai shi ne kiransu zuwa ga alkur’ani mai girma wanda abin amincewa ne tsakanin dukkan bangarorin.

Masu sauraro a nan zamu dasa aya a cikin shirimmu na yau sai kuma wata fitowa idan All..ya kaimu, wassalamu alaikum wa rahamatullahi wa barakatuhu.

Share

0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Kissoshin Rayuwa: Sirar Imam Hassan (a) 125 August 13, 2025 Kissoshin Rayuwa: Sirar Imam Hassan (a) 124 August 13, 2025 Iran: Babu Mika Kai Ga Takurawar kasashen Yamma har sai An Kawo Karshen Barazana August 13, 2025 Hukuma Mai Kula Da Sauka Da Tashin Jiragen Sama A Paris Ya Dakatar Da Wani Ma’aikacinta August 13, 2025 Iraki Tace: Ita Yentacciyar Kasashe Ce Bayan da Amurka Ta Yi Korafi Kan Yarjeniyar tsaro da Iran August 13, 2025 Ministan Harkokin Wajen Masar Ya sake Ganawa da Aragchi Da Kuma Gorossy August 13, 2025 Shugaban Kasar Iran Ya Jaddada Alhininsa Kan Kashen Masanan Kasar Iran Da ‘Yan Sahayoniyya Suka Yi August 13, 2025 Ministan Harkokin Wajen Iran Ya Jaddada Cewa: Lokaci Ya Yi Da Za A Daina Kakaka Takunkumi Da Ba Dace Ba Kan Kasashe August 13, 2025 Sakataren Majalisar Kolin Tsaron Kasar Iran Ya Jaddada Kasancewar Iran Tare Da Kasar Lebanon Koda Yaushe August 13, 2025 Kasar Iraki Ta Ce: Yarjejeniyar Da Ta Kulla Da Iran Zai Amfani Dukkan Kasashen Yankin August 13, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci About Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS News Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Explore Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS

উৎস: HausaTv

কীওয়ার্ড: mutanen Basra wadanda suka masu sauraro

এছাড়াও পড়ুন:

Tireloli Sun Yi Taho Mu Gama, Mutane 4 Sun Jikkata A Titin Zariya–Kaduna

Yanzu haka mutane huɗu suna karɓar magani a Asibitin Koyarwa na Jami’ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Shika, Zariya, bayan sun jikkata a wani mummunan haɗarin da ya haɗa da tankoki biyu a ƙauyen Kake, yankin Dan Magaji, kan hanyar Zariya–Kaduna. Haɗarin ya jawo mummunar gobara bayan haɗuwar motocin.

Kwamandan hukumar kiyaye haɗɗura ta ƙasa (FRSC) reshen Zariya, Nasir Abdullahi Falgore, ya bayyana cewa ɗaya daga cikin tankokin na ɗauke da iskar gas (LNG), yayin da ɗayar kuma babu komai a cikinsa. Ya ce sakamakon binciken farko ya nuna tayar ɗaya daga cikin tankokin ce ta fashe, lamarin da ya sa tankar da ke biye ta bugi ta gaba, wanda ya haddasa fashewar gas da tayar da gobara.

Kwalejin Digiri Na Biyu Ta ABU Ta Ƙaddamar Da Sabbin Ɗalibai A Zariya Shirin Iskar Gas Na CNG Abin A Yaba Wa Shugaba Tinubu Ne -Shugaban IPMAN Na Ƙasa

Kwamandan hukumar kashe gobara ta ƙasa a Zariya, Aminu Ahmadu Kiyawa, ya ce jami’ansa sun isa wurin cikin gaggawa bayan samun kiran wayar gaggawa. Ya tabbatar da cewa mutum uku sun jikkata sakamakon fashewar gas, yayin da aka ceto mutum guda daga ɗaya tankar, kuma duka huɗun an garzaya da su zuwa asibitin ABU domin samun kulawar likitoci.

Kiyawa ya ƙaryata jita-jitar da ake cewa haɗarin ya rutsa da ƙananan motoci irin su Gulf, yana mai cewa “Lokacin da muka isa wurin, tankoki biyu ne kawai muka gani. Babu wata ƙaramar mota da ta shiga hatsarin.” Shaidun gani da ido ma sun tabbatar da cewa tankoki biyu kacal ne suka shiga haɗarin, kuma babu wanda ya rasu a lokacin da ake haɗa wannan rahoton.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Kissoshin Rayuwa: Sirar Imam Hassan (a) 130
  • Kissoshin Rayuwa: Sirar Imam Hassan (a) 129
  • Kissoshin Rayuwa: Sirar Imam Hassan (a) 128
  • Kissoshin Rayuwa: Imam Hassan (a) 127
  • Kissoshin Rayuwa: Sirar Imam Hassan (a) 125
  • Kissoshin Rayuwa: Sirar Imam Hassan (a) 124
  • Kullum a Kamaru muke kwana, mu yini a Najeriya – Mazauna ƙauyen Borno
  • Bankin Duniya zai kashe $300m domin inganta rayuwar ’yan gudun hijira a Arewacin Nijeriya
  • Tireloli Sun Yi Taho Mu Gama, Mutane 4 Sun Jikkata A Titin Zariya–Kaduna