Aminiya:
2025-10-13@18:08:21 GMT

Kullum a Kamaru muke kwana, mu yini a Najeriya – Mazauna ƙauyen Borno

Published: 13th, August 2025 GMT

Dubban mazauna garin Kirawa da ke jihar Borno da mayakan Boko Haram suka raba da gidajensu, sun ce yanzu kullum a kasar Kamaru suke saboda gudun harin ’yan Boko Haram cikin dare.

Mutanen, wadanda yanzu haka ke samun mafaka a kauyukan kasar ta Kamaru, sun kuma koka da halin kuncin da suke ciki a yanzu.

‘Zan iya shiga mummunan yanayi idan Dangote bai aure ni ba’ Lafiyar Tinubu kalau – Soludo

Mazauna yankin shin shaida wa wata kafar yada labarai a ranar Talata cewa tun bayan harin da aka kai ranar Asabar da ya kai ga janye sojoji daga yankin mazauna kauyuka da dama sun bazu a kauyukan da ke kan iyaka da Kamaru.

Sun kuma ce a sakamakon haka, suna kwana a kan tituna, masallatai da azuzuwan makaranta saboda fargabar hare-hare cikin tsakar dare.

Hakimin yankin na Kirawa, Abdulrahman Abubakar, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin, ya yi kira ga gwamnati da ta gaggauta daukar matakin tsugunar da al’umma da kuma tabbatar da zaman lafiya a yankin.

“A halin da ake ciki yanzu ba ma iya yin barci da idanunmu biyu a rufe, yayin da mutanenmu a yanzu ke ke kai kawo a tsakanin kasashen biyu, suna kwana a Kamaru da daddare su yini kuma a Najeriya.

“Wannan shi ne karo na farko da muke fuskantar wannan hari tun bayan da aka sake tsugunar da al’ummarmu shekaru da suka wuce,” in ji Abubakar.

Daya daga cikin ‘yan gudun hijirar, Buba Aji, wanda ya ba da labarin abubuwan da ‘yan Najeriya suka fuskanta a kauyukan Kamaru, ya bayyana hakan a matsayin abin tada hankali da rashin mutuntawa.

Ya ce, “A cikin dare, abubuwan da suka faru yawanci ba su da kyau, misali, a ranar litinin da daddare, an yi ruwan sama kamar da bakin qwarya, wanda yawancin mutanen  mu suka kwana ruwan saman na dukan su a filin Allah ta’ala illa kalilan daga cikin mu da muka samu mafaka a masallatai da makarantu, saboda muna fargabar ‘yan tada ƙayar bayan su dawo da dare.

“Yanzu wurin da muke samun mafaka shine Kerawa da Lamise a Kamaru, kuma a kan tituna kai tsaye akasarin mu ke kwana, “ in ji shi.

Ya kara da cewa “A halin yanzu babu wani sojan Najeriya a cikin yankinmj, ‘yan sibiliyan JTF, wadanda sojojin Kamaru ne suma sun koma kasarsu.

“Don haka muna bukatar gwamnati ta saurari kokenmu, ta kuma kawo mana xauki kafin wadannan mutane (masu tada qayar baya) su sake kawo wani harin,“ Buba Aji.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Boko Haram Kamaru

এছাড়াও পড়ুন:

Tinubu ya tafi Rome don halartar taro kan sha’anin tsaro

Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya tafi birnin Rome na Ƙasar Italiya, domin halartar taron shugabannin ƙasashe kan sha’anin tsaro.

Mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan harkokin labarai, Bayo Onanuga, ya ce za a fara taron ne a ranar 14 ga watan Oktoba, kuma zai mayar da hankali kan matsalar tsaro da ke addabar yankin Yammacin Afirka.

’Yan sanda sun ceto mutum 10 daga hannun ’yan bindiga a Kaduna Talauci da tsangwama na hana yara mata karatu a Gombe — Kwamishina

Taron na ‘Aqaba Process’ an kafa shi ne a shekarar 2015 ta hannun Sarki Abdullah II na Ƙasar Jordan, kuma ana gudanar da shi tare da haɗin gwiwar Jordan da ƙasar Italiya.

Taron na nufin tattauna hanyoyin yaƙi da ta’addanci da kuma magance matsalolin tsaro da ke adabbar ƙasashe daban-daban, musamman a yankin Yammacin Afirka.

Taron zai haɗa shugabannin ƙasashe na Afirka, jami’an leƙen asiri da na tsaro, da wakilan ƙungiyoyin ƙasa da ƙasa da na ƙungiyoyin fararen hula, domin tattauna yadda za a magance matsalolin tsaro da ke addabar yankin.

Za a tattauna kan yadda ƙungiyoyin ta’addanci ke yaɗuwa a Yammacin Afirka, alaƙa tsakanin masu laifi da ’yan ta’adda, da kuma alaƙar da ke tsakanin ta’addanci a yankin Sahel.

Hakazalika, za a tattauna yadda za a daƙile yaɗuwar aƙidar ta’addanci a Intanet da kuma lalata hanyoyin sadarwar da ’yan ta’adda ke amfani da su wajen yaɗa ra’ayoyinsu da ɗaukar sababbin mabiya.

Shugaba Tinubu zai kuma tattauna da wasu shugabannin ƙasashe don neman hanyoyin daƙile matsalar tsaro da ke addabar yankin.

Tinubu ya samu rakiyar Ministan Harkokin Waje, Ambasada Bianca Odumegwu–Ojukwu; Ministan Tsaro, Mohammed Badaru Abubakar.

Sauran sun haɗa daMai bai wa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, Nuhu Ribadu; Darakta-Janar na Hukumar Leƙen Asiri ta Ƙasa (NIA), Ambasada Mohammed Mohammed; da wasu manyan jami’an gwamnati.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Zaben Kamaru: Issa Tchiroma Bakary ya lashe yankunan da Biya ke da rinjaye
  • Ba Gudu Ba Ja-da-baya Kan Ci Gaba Da Kwaskwarima Ga Tsarin Haƙar Ma’adanai – Minista
  • Sojoji sun kashe ’yan ta’adda 9, sun kwato kudin fansa a Borno
  • Kungiyar Malaman Jami’o’in Najeriya ASUU ta Shiga Yajin Aiki
  • Tinubu ya tafi Rome don halartar taro kan sha’anin tsaro
  • Maryam Sanda na cikin waɗanda Tinubu ya yi wa afuwa
  • Wasu Daga Cikin Muhimman Alamomin Ciwon Kansa
  • ’Yan ta’adda sun kashe sojoji 4 a wani sabon hari a Borno
  • A Ba Mu Makamai Don Kare Kanmu – Jama’ar Sakkwato
  • Sojoji sun hallaka ’yan ta’adda 5 a Borno