Iran ta yi kakkausar suka kan tsare ‘yan kasarta a Birtaniya

Iran ta gayyaci mai kula da harkokin kasar Birtaniya a birnin Tehran, biyo bayan tsare wasu ‘yan kasarta da dama ba bisa ka’ida ba a

Iran ta gayyaci mai kula da harkokin kasar Birtaniya a birnin Tehran, biyo bayan tsare wasu ‘yan kasarta da dama ba bisa ka’ida ba a kasar.

Shugaban bangaren kula da sashen yammacin turai a ma’aikatar harkokin wajen kasar ya yi kakkausar suka da nuna adawa da matakin na gwamnatin Birtaniyya, da kuma zarge-zargen da ba su dace ba da ake yi wa Jamhuriyar Musulunci ta Iran.

Jami’in ya ce tsare ‘yan kasar Iran ya sabawa ka’idoji da dokokin kasa da kasa da kuma hakkokin bil’adama da aka amince da su, saboda an tuhume su ba tare da wata hujja ba.

Ya kara da cewa ‘yan kasar Iran da ake tsare da su, an kuma hana su harkokin ofishin jakadanci da kuma ba su kariya…

Jami’in na Iran ya jaddada cewa gwamnatin Birtaniyya ce ke da cikakken alhakin irin wadannan ayyuka, wadanda ake ganin suna da alaka da siyasa domin matsin lamba kan Iran.

A ranar Asabar an kama wasu mutane hudu ‘yan kasar Iran, kuma An tsare su ne a karkashin dokar ta’addanci, kamar yadda kafafen yada labaran Burtaniya suka ruwaito.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments