Amurka, Ki Fahimci Cewa “Girma Da Arziki Ke Sa A Ja Bajimin Sa Da Zaren Abawa”
Published: 15th, April 2025 GMT
Ban da haka, Wang ya ce matakan kasar Amurka sun karya ka’idojin kungiyar WTO na rashin nuna bambanci, da takaita karbar haraji, kana suna girgiza tsarin tattalin arzikin duniya, da tushen tsarin cinikayya da ya shafi bangarori daban daban. Ganin haka ya sa kasar Sin daukar matakan ramuwar gayya kan kasar Amurka, don kare halaltacciyar moriyar kai, gami da neman tabbatar da adalci a duniya.
Da ma shugaba Donald Trump na kasar Amurka ya gabatar da jerin zafafan matakan tattalin arziki ne don neman daidaita matsalolin da kasar Amurka ke fuskanta. Sai dai ra’ayinsa na dora “Amurka ta zama gaba da komai” na tarnake masa damar samun biyan bukata.
Raymond Thomas Dalio, shahararren mai kula da sha’anin hada-hadar kudi ne, wanda ya kafa kamfanin Bridgewater Associates, ya tattauna tare da ‘yan jarida a kwanan baya, inda ya fayyace matsalolin da kasar Amurka ke fuskanta a fannin tattalin arziki, kamar su: dimbin bashin da ake binta, da rashin karfin samar da kayayyakin da take bukata, da dai sauransu. A cewarsa, Amurka ta riga ta tsunduma cikin mawuyacin hali na cin bashi da kashe kudi fiye da kima a kai a kai, lamarin da ya haddasa rushewar tsarin kudi da siyasa na duniya, da kawo karshen zamanin tilasta zama karkashin jagorancin kasar Amurka. Kana mista Dalio ya ce yanzu haka, Amurka na neman daidaita matsalolin da take fuskanta ta hanyar ta da rikici a duniya, da karin matsin lamba ga sauran kasashe, lamarin da a cewarsa zai iya haifar da sakamako mafi muni, da kawo tafiyar hawainiya ga tattalin arzikinta.
Hausawa kan ce “Girma da arziki ke sa a ja sa da zaren abawa.” Sai dai a nata bangare, kasar Amurka ta tsaya kan daukar matakan radin kai, da matsawa da cin zarafin sauran kasashe, duk da cewa tana bukatar samun taimako daga saura wajen daidaita matsalar da take fuskanta, inda kuma sam ba zai yiwu ta samu biyan bukata ta wannan turbar ba.
A karshe dai za a lalubo dabara kamar yadda minsta Wang Wentao ya fada, “nemo bakin zaren wareware matsala ta hanyar shawarwari, bisa tushen girmama juna, da zaman daidaito”, matukar ana son warware matsalar.
Muna fatan ganin kasar Amurka ta zama mai sanin ya kamata, da wajabta wa kanta iya sauraron shawara, da daukar mataki mafi dacewa. (Bello Wang)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppকীওয়ার্ড: kasar Amurka
এছাড়াও পড়ুন:
Cibiyar Yaƙi da Ta’addanci Ta Yaba Wa Gwamna Lawal Kan Matakan Yaƙi Da ‘Yan Bindiga A Zamfara
A nasa jawabin, Gwamna Dauda Lawal ya yaba da ziyarar da cibiyar ta kai Zamfara domin duba ƙoƙarin gwamnati na magance matsalar rashin tsaro a jihar.
“Ina yawan cewa, idan ku ka yi ƙoƙarin shawo kan Zamfara yadda ya kamata ta fuskar rashin tsaro, za ku magance kashi 80 na matsalolin tsaro a Arewa.
“Daga dukkan tsare-tsaren da na gani ya zuwa yanzu, mun mallaki abin da ake buƙata domin tunkarar waɗannan ƙalubale bisa tuntubar juna da haxin gwiwa tsakanin jihar Zamfara da ofishin mai ba shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro, wannan abin a yaba ne.
“Na yi farin ciki da jin cewa Tarayyar Turai ta ware wasu kuɗaɗe, duk da cewa za mu samar da wani asusu, a Zamfara a shirye muke mu ba da tallafin, idan kun shirya gobe, mu ma mun shirya.
“Mun shirya, kuma ƙofar mu a buɗe take, duk wani abu da zai kawo sauyi mai kyau a Zamfara muna maraba da shi, muna buƙatar tsari na abin da ku ke yi domin mu ci gaba da bin diddigin lamarin, zan samu wata tawaga da za ta riƙa hulɗa da cibiyar yaƙi da ta’addanci.
Tun da farko, Shugabar Rigakafi da Yaƙi da Ta’addanci (PCVE), Ambasada Mairo Musa Abbas ta ce, tawagar ta zo jihar Zamfara ne a madadin mai baiwa shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro Mallam Nuhu Ribadu da kuma kodinetan yaƙi da ta’addanci na ƙasa, Manjo Janar Adamu Garba Laka. “Muna nan a matsayin wani bangare na dabarun bayar da shawarwari na ƙasa baki ɗaya.”
“Muna son sake gode muku bisa irin karramawar da ka yi mana a Jihar Zamfara da kuma irin shugabancin da ka yi wa al’umma, muna sa ran haɗin kai don ganin cewa Zamfara ta zama kan gaba wajen yaƙi da ‘yan bindiga.”
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp