Kokarin Da Iran Take A Tattaunawa Da Amurka Shi Ne Dage Mata Takunkuman Zaluncin Da Aka Dora Mata
Published: 15th, April 2025 GMT
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Esmail Bagaei ya bayyana cewa kokari da JMI a tattaunawarta da kasar Amurka kan shirin Nukliyar kasar shi ne ganin an dauke mata takunkuman tattalin arzikin da aka dora mata, ko amurka da dora mata..
Tashar talabjin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar ta Iran yana fadar haka a jiya, Litinin a lokacinda yake jawabi gay an jaridu a ko wani mako.
Ya kuma kara da cewa degewa Iran wadanan takunkuman dole ne su kasance mataki na farko don ganin hanyar diblomasiyya ta yi aikinta. Kuma sai da haka ne ake iya fatan za’a cimma wani abu mai muhimmanci a wannan tattaunawar.
Banda haka kakakin ma’aikatar harkokin wajen JMI ya bayyana damuwarsa da yadda gwamnatin HKI take keta yarjeniyar da suka cimma da kasar Lebanon a cikin watannin da suka gabata. Y ace yahudawan suna keta yarjeniyar 1701 kamar ba’a samar da yarjeniyar ba.
A lokacinda aka tambayeshi dangane da takunkuman Bagaei ya ce, su da kansu ne yakamata su warware, wannan batun, don bai kamata sun a maganar tattaunwa sannan a dayan bangaren kuma suka kara takurawa wanda kuke tattaunawa da shi ba.
Yace Iran ta nuna hakukri da kuma diblomasiyya a cikin wannan al-amarin, kuma Amurka ce yakamata ta nuna cewa tana bukatar tattaunawar tare da daukar matakan da suka dace.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Shugaban Kasar Iran Ya Gana Da Fira Ministan Pakistan Tare Da Tattaunawa Kan Harin Da Iran Ta Fsukanta
Shugaban kasar Iran ya gana da fira ministan kasar Pakistan
Shugaban kasar Masoud Pezehkian ya gana da fira ministan Pakistan Shehbaz Sharif a gefen zaman taron kungiyar hadin kan tattalin arziki ta ECO da Jamhuriyar Azabaijan ta karbi bakunci.
Fira ministan Pakistan Shehbaz Sharif ya yaba da irin rawar da shugaban kasar Iran ya taka a lokacin da yahudawan sahayuniyya suka kai wa Iran hari tare da tabbatar da goyon bayan Pakistan ga Iran da kuma hada kai da hadin gwiwa da Iran don samar da zaman lafiya a yankin.
Sanarwar da ofishin fira ministan Pakistan ya fitar ta ce: shugaba Masoud Pezehkian ya gana da fira ministan Pakistan Shehbaz Sharif a gefen zaman taron kungiyar hadin kan tattalin arziki ta ECO da Jamhuriyar Azarbaijan ta dauki nauyi.
Shugaban kasar ta Iran ya isa birnin Khankandi na jamhuriyar Azarbaijan ne a yau Juma’a a domin halartar taron koli na kungiyar hadin kan tattalin arziki ta ECO karo na 17.