Iran Zata Yaye Labulen Ire-Iren Makamanta Na Musamman Da Ta Mallaka Domin Kare Kai
Published: 13th, April 2025 GMT
Kwamandan rundunar sojojin kasa ta Iran ya bayyana cewa: Nan ba da jimawa ba za a yaye labulen ire-iren makamai na musamman da Iran ta mallaka
Kwamandan rundunar sojin kasa ta Iran Birgediya Janar Kiomars Heidari ya yi nuni da shirin rufe kan iyakar kasar da ke gabashin Iran, yana mai cewa: Wannan ba kawai wata katanga ba ce mai tsayin mita 4, saboda an tanadar da ita ce da nau’o’in makamai masu kwaloluwar ci gaba na zamani a duniya, wannan shiri an gudanar da shi ne tsawon shekaru hudu kuma za a kammala shi nan da shekaru uku masu zuwa.
Kwamandan rundunar sojin kasa ta Iran ya jaddada haka ne a wani taron manema labarai da ya gudanar a yau Lahadi cewa, yana mai cewa; An bullo da sauye-sauye ne ga tsarin rundunar sojojin kasa baki daya, don ba da damar wuce tsohon tsari saboda kai wa ga tsari na zamani da zai iya tunkarar kalubalen da ake fuskanta a yau.
Birgediya Janar Haidari ya yi jawabi kan muhimman sauye-sauye a cikin tsari da makaman da sojojin kasa suka samar, yana mai cewa, “Sun mayar da bukatu na yau da kullum zuwa wani rundunar kai hari cikin gaggawa mai saurin mayar da martani.
Ya kara da cewa, “Wannan runduna ta mallaki karfin motsawa 100%, da karfin kai hari 100%, da kuma juriya 100%. Don cimma wannan buri, suna bukatar makamai na musamman wadanda ke dauke da wadannan siffofi guda biyu.”
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Matsalar Tsaro: Tinubu Ya Yi Ganawar Sirri da Gwamnonin Jihohi Shidda
Daga Bello Wakili
Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya yi ganawar sirri da gwamnonin jihohi shidda daga sassan ƙasar a ci gaba da tattaunawar da ake yi domin ƙarfafa batun tsaro a ƙasa.
Gwamnonin da suka halarci taron sun hada da Gwamna Monday Okpebholo na jihar Edo, Umar Namadi na Jigawa, Nasir Idris na Kebbi, Ahmed Ododo na Kogi, Lucky Aiyedatiwa na Ondo, da Ahmed Aliyu na jihar Sokoto.
Taron, wanda ya ɗauki kusan mintuna 40, ya mayar da hankali ne kan muhimman matsalolin tsaro da ke shafar jihohinsu, duk da cewa ba a bayyana cikakkun bayanai ba.
Wakilin Rediyon Najeriya da ke fadar shugaban kasa ya ruwaito cewa wannan zaman na daga cikin kokarin shugaban kasa na ƙara haɗin kai da jihohi wajen magance matsalolin tsaro.
Wannan cigaban ya biyo bayan nasarar da Gwamnatin Tarayya ta samu na kubutar da dalibai 100 da aka yi garkuwa da su a Jihar Neja, baya ga wanda aka yi a Jihar Kebbi.
Ci gaba da irin waɗannan tattaunawa na shugaban kasa na nuna jajircewar gwamnati wajen tabbatar da tsaro da kwanciyar hankali a fadin ƙasar.