Kasar Rasha Ta Gabatar Da Shawara Ga Kwamitin Sulhun MDD Kan Shirin Makamashin Nukiliyar Iran
Published: 27th, August 2025 GMT
Rasha ta ba da shawarar tsawaita kudurin kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya kan yarjejeniyar makamashin nukiliyar Iran
Mataimakin wakilin dindindin na kasar Rasha a Majalisar Dinkin Duniya Dmitry Polyansky ya sanar da cewa, Rasha ta gabatar da shawarwarin a Majalisar Dinkin Duniya na tsawaita sahihancin kudurin kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya kan yarjejeniyar makamashin nukiliyar Iran.
Ya kara da cewa: “Sun yi imanin cewa ya kamata kasashen duniya su zabi zaman lafiya da diflomasiyya, ba goyon bayan yaki ba, kuma shi ne ainihin abin da daftarin kudurin nasu ya kunsa… Ana mika siga na biyu (na daftarin kudurin) ga mambobin kwamitin sulhu a halin yanzu, kamar yadda suke magana, suna fatan za a amince da shi.”
Kamar yadda takardar ta nuna, Rasha ta ba da shawarar tsawaita kudurin da ya dace na tsawon watanni shida, har zuwa ranar 18 ga Afrilu, 2026.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Majalisar Ministocin Sudan Ta Fara Zamanta A Birnin Khartoum Fadar Mulkin Kasar Tun Bayan Barkewar Yaki August 27, 2025 Araqchi: Jakadan Australia a Tehran dan koren Isra’ila ne August 27, 2025 Rasha ta shirya daftarin dakile Shirin turai na mayar da takunkumin MDD kan Iran August 27, 2025 ECOWAS na Shirin hada rundunar dakaru 260,000 domin yaki da ta’addanci August 27, 2025 Trump ya yi barazanar korar Gwamnar Babban Bankin Amurka August 27, 2025 Syria: Adadin mutanen da suka mutu a harin Isra’ila a yankin Damascus ya kai 5 August 27, 2025 An Kammala Taron Iran Da E3 A Geneva August 26, 2025 Iran Ta ce Zata Rama Kan Korar Jakadanta Daga kasar Australia August 26, 2025 Najeriya: Jirgin Kasa tsakan Abuja da Kaduna Ya Sauka Kan Layin Dogo August 26, 2025 Iran A Shirye Take Ta Hada kai Da Pakistan Don Kawo Karshen Ayyukan Ta’addanci August 26, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: a Majalisar Dinkin Duniya
এছাড়াও পড়ুন:
Araqchi: Gwajin Makaman Nukiliya Na Amurka Babbar Barazana Ce Ga Duniya
Ministan Harkokin Wajen Iran Abbas Araghchi ya yi gargadi a matsayin martani ga sanarwar Washington na ci gaba da gwajin makaman nukiliya, yana mai kiran hakan a matsayin wani mataki na koma-baya da Rashin yin da’a ga dokokin kasa da kasa.
Wannan na zuwa ne a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Alhamis, inda ya soki Washington saboda sauya wa Ma’aikatar Tsaron kasar suna zuwa Ma’aikatar Yaki, kuma ya yi Allah Wadai da Shirin Amurka na yin gwajin makaman nukiliya, tare da bayyana hakan a matsayin yunkurin tayar da zaune tsaye da jefa duniya a cikin bala’i.
Wanda yake aikata irin wannan halayya ne ke ci gaba da yin barazanar sake kai hari kan cibiyoyin nukiliya na Iran bisa hujjar hana Iran mallakar makaman nukiliya da sunan kare kansu daga Iran domin kada ta mallaki makaman kare dangi.” in ji ministan harkokin wajen Iran.
Ya yi Allah wadai da Amurka saboda sukar da ta dade tana yi wa shirin nukiliya na zaman lafiya na Iran yayin da ita kuma take ci gaba da gwajin makamanta na nukiliya, wanda hakan ya saba wa dokokin duniya.
Shugaban Amurka Donald Trump a ranar Laraba ya bayyana cewa makaman nukiliya na Washington su ne mafi girma a duniya, kuma ya danganta wannan matsayin da gyare-gyare da aka yi a lokacin gwamnatinsa.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Masar da Eritrea Sun Tattauna Bukatar Tallafawa Kasar Sudan October 31, 2025 Shugaban Lebanon Ya Umarci Sojoji Da Su Fuskanci Kutsen Na Isra’ila A Kudancin Kasar October 31, 2025 Madagascar Ta Sanar da Kafa Sabuwar Gwamnati Tare da Manyan ‘Yan Adawa October 31, 2025 Iran ta yi fatali da kalamman IAEA Kan Shirin Nukiliyarta October 30, 2025 Trump Ya Umarci Ma’aikatar Yakin Amurka Ta koma gwajin makaman nukiliya October 30, 2025 Isra’ila ta amince da fadada matsugunai a Yammacin Kogin Jordan October 30, 2025 Gaza: hare-haren Isra’ila sun kashe mutane 100 Cikin Kwanaki Biyu October 30, 2025 Sudan : Kasashen duniya na tir da cin zarafi a El-Fasher October 30, 2025 Iran Ta Jaddada Bin Hanyar Diflomasiya Ko Da A Lokacin Yaki Ne Amma Ba Zata Amince Da Bin Umarni Ba October 30, 2025 Qalibaf: Amurka Tana Yaudarar Duniya Da Zaman Lafiya, Alhalin Tana Ci Gaba Da Kai Harin Wuce Gona Da Iri October 30, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci