Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ya godewa ministan harkokin wajen kasar Omman
Published: 13th, April 2025 GMT
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Esma’ila Bagaei ya godeawa ministan harkokin wajen kasar Omman kan yadda ya shirya ya kuma gabatar da tattaunawa tsakanin JMI da Amurka a birnin Mascat da kuma kai kawon da yayi a tsakanin bangarorin biyu.
Kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar Iran ya nakalto Bagaei yana bayyana haka a wani sakon da ya aika a cikin shafinsa na X a jiya Asabar, ya kuma aika da sakon ne a dai dai lokacinda ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi yana kan hanyarsa ta dawowa Tehran, bayan tattaunawar.
উৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: ministan harkokin wajen kasar harkokin wajen kasar Iran
এছাড়াও পড়ুন:
Taron APEC Na 2026 Da Za A Shirya A Kasar Sin Zai Bude Sabon Babin Na Gina Al’ummar Bai Daya Ta Asiya-Pasifik
Bayan an mika damar karbar bakuncin taron kungiyar APEC, kasashen duniya sun soma zura ido kan kasar Sin. Ana sa ran cewa, taron APEC da za a gudanar a Shenzhen, zai kara habaka hadin gwiwa, da samun ci gaba, da wadata tare a shiyyar, kana zai shaida yadda kasar Sin ke kara samar da sabbin damammaki ga yankin Asiya da Pasifik, bisa ga sabbin nasarorin da take samu ta hanyar zamanantarwa irin ta kasar Sin. (Mai fassara Bilkisu Xin)
ShareTweetSendShare MASU ALAKA