Sanƙarau: An tabbatar da ɓullar cutar ga mutane 300 a Sokoto
Published: 11th, April 2025 GMT
Gwamnatin jihar Sokoto ta tabbatar da samun ɓullar cutar sanƙarau guda 300 a wasu ƙananan hukumomin jihar.
Kwamishinan lafiya na jihar Dakta Farouk Abubakar ne ya tabbatar da hakan a taron wayar da kan jama’a na kwana ɗaya da ƙungiyar raya unguwanni ta jiha (WDC) tare da haɗin gwiwar ma’aikatar lafiya ta jiha da hukumar kula da lafiya matakin farko ta jihar suka shirya a ranar Juma’a.
Sai dai kwamishinan bai yi ƙarin bayani kan adadin mace-macen da aka samu tun watan Fabrairu da aka fara samun ɓullar cutar ba.
Ya ce har yanzu mutane 16 na ci gaba da karɓar magani a asibitoci yayin da sauran kuma aka sallame su.
A jawabansu daban daban, mai ba da shawara na musamman kan harkokin kiwon lafiya a matakin farko na jiha, Dakta Muhammad Bello Marnona, da babbar sakatariyar hukumar, Dakta Larai Aliyu Tambuwal, sun yaba da irin hangen nesa na shugabancin hukumar ta WDC.
Sun ce, ana iya rigakafin cutar kuma sun shawarci mutane da su ziyarci cibiyoyin lafiya da ke kusa don samun magungunan da suka dace a duk lokacin da suka fuskanci wata matsala.
Shima da yake tsokaci shugaban yankin Malam Ya’u Muhammad Danda wanda mataimakinsa Alhaji Faruk Umar Garba ya wakilta ya bayyana taron a matsayin wanda ya dace.
A nasa jawabin, Sarkin Musulmi Sultan Sa’ad Abubakar wanda Hakimin Gagi, Alhaji Sani Umar Jabbi ya wakilta, ya yaba wa Gwamna Ahmed Aliyu da jagororin gwamnatinsa na inganta lafiyar al’umma.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: sankarau
এছাড়াও পড়ুন:
Hajjin 2025: Jihar Kwara Ta Fara Allurar Rigakafi Ga Maniyyata
Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Kwara ta fara yi wa maniyyata rigakafin cututtuka kafin gudanar da aikin Hajji na shekarar 2025.
Da yake jawabi a wajen kaddamar da shirin rigakafin da aka gudanar a harabar hukumar da ke Ilori, shugaban hukumar, Alhaji Abdulsalam Abdulkadir, ya bayyana rigakafin a matsayin wani sharadi da ya zamto wajibi ga dukkan Alhazai bisa umarnin gwamnatin Saudiyya.
Ya ce yin rigakafin yana da matuƙar muhimmanci wajen tabbatar da lafiyar Alhazai a lokacin gudanar da aikin Hajji.
A cewarsa, an shirya shirin rigakafin ne domin hana yaduwar cututtuka da kuma tabbatar da cewa Alhazai sun samu lafiya da kwanciyar hankali yayin aikin Hajjin.
Alhaji Abdulkadir ya bayyana cewa za a fara jigilar rukuni na farko na Alhazai daga jihar zuwa ƙasar Saudiyya ranar 12 ga watan Mayu.
Shugaban hukumar ya ƙara da cewa za a kammala aikin rigakafin ne ranar Laraba 30 ga watan Mayu, sannan kuma za a fara raba tufafi da jakunkunan tafiya nan take.
Alhaji Abdulkadir ya yi kira ga maniyyatan da su kammala duk shirye-shiryen lafiyar jiki da na tafiya cikin lokacin da aka kayyade domin samun nasarar aikin Hajjin ba tare da wata tangarda ba.
Ali Muhammad Rabi’u